22/06/2026
DIWANI DA RUHUL ADAB
*
**
***
Duk wanda ya karanta Ruhul Adab a gaban sufi ba masanin larabci kawai ba, kuma ya kiyaye baitocin ta da abinda ke cikin ta na ma'ana, zai ga zamanin nan kusan hanyar gamawa lafiya a faidha baya samuwa sai ga wanda ya kiyaye Ruhul Adab.
Ruhul Adab littafi ne da Shehu ya rubuta ta musamman domin shiryar da halitta, kuma litattafai da yawa na Shehu an ce daga baya akwai inda ya ɗora alƙalami yayi yan gyare-gyare, amma bai gyara komai a Ruhul Adab ba, kuma tana sahun litattafan Shehu da ke girgiza mazaje wurin yi mata sharhi.
Sannan Hifzi (حفظ) yana nufin kiyaye wani abu, na ilimi ko dukiya ko wanin haka, duk abinda aka ce an kiyaye shi, ana nufin yana cikin kulawa, don haka in aka ce ga mahaddacin Alqur'ani, ana nufin wanda ya karanta ta, yasan darajar ta, sannan ya rubuta ta a allon zuciyar sa, yake gani da jin ta a cikin motsin sa.
Mahaddatan ta a baya kusan galibin su masu tsoron Allah ne da kiyaye sunnonin Annabi ﷺ, amma a yau, ƙara yawa suke yi kullum, amma wasun su basu daina wargi da izgili ga addinin Allah ba, ya ishe ka misali, yan ta'adda suna taƙamar saƙon Alqur'ani suke isarwa amma duk wanda ya fahimci Annabi ﷺ da kyau, yasan sun yiwa Alqur'ani gurguwar fahimta domin babu inda taci karo da halayen nan na Annabi ﷺ kyawawa, amma daga ƙarshe in muka yi nazari zamu gane ashe tabbas Alqur'ani shiriya ne sai dai ba ga kowa ba, sai masu "Taƙawa" kawai.
To haka nan a halin da muke ciki yau a Faidha, mune ruhin Ɗarikar Tijjaniyya, duk batijjanen da baiyi riƙo da faidhar Shehu ba, zaka gan shi ya cika amma ba cif-cif ba, kuma masana ilimin larabci da sira da sauran su, sun tabbatar babu littafin da aka yabi Annabi ﷺ da kyau kamar Diwani, littafin dake ƙunshe da sirron Alqur'ani da salatai baki ɗaya da Asma'ul husna da sauran hasake, gashi kullum masu karanta ta da haddace ta kara yawa suke yi.
Amma kamar yadda Alqur'ani take zama shiriya ga mai taƙawa kawai, Haddace Alqur'ani kawai bata samar da taƙawa, akwai hanyoyin da shari'a ta kawo wanda za a bi don samun Taƙawa, haka nan sirrin Diwani babu mai samun ta sai wanda baya sahun mutane biyun nan da Shehu RTA yace baya tare dasu, don gudun faɗawa cikin su, hanya mafi sauƙi shine fahimta da kiyaye nasihohin Shehu da yayi a Ruhul Adab, domin musamman ya wallafa littafin don shiryar da duk mai neman shiriya.
Mai ilimi da hankali in yaji kace "Allah kasa masoya Annabi ﷺ na haƙiƙa su fi masu Sallah yawa a Musulunci" yasan kana nufin a samu masu sallah kamar yadda Annabi ﷺ ya umarta ne ba wai a rage yawan masallata ba, domin duk masoyin Annabi ﷺ na haƙiƙa zai yi sallah cikin khushu'i, wanda ko baya ganin girman Annabi ﷺ baya son sa, sallar sa ba zata karɓu ba komi tajwidi da kyan tsayuwar sa, b***e ta hana shi alfasha, b***e kuma tayi masa rana a kiyama, kamar yadda bata yiwa shugaban munafukai ba.
Haka nan fadin Allah yasa Mahaddatan Ruhul Adab su fi Mahaddatan Diwani yawa a faidha, yana nufin a samu wayanda da an gansu za a tuna Shehu ba wayanda zasu fadi abinda Shehu ya faɗa kawai, amma aikin su ya sha bambam da nasa ba.
Kullum Mu'awalli ake karɓa, Kullum Diwani ake karantawa, amma in ka zauna cikin wasu wayanda s**a ce sun san mu'awwali sun haddace diwani, za kaga a filin karatun diwanin suke cewa an raina su, an ba wanin su sifika su ba a basu ba, alhalin sun fi shi hadda, sun fi shi wancan da wannan, ka ga Ruhul Adab kiyaye ta sannu a hankali take fidda mutum daga ganin kan sa zuwa ganin zatin Allah kawai.
A takaice, Yadda Ilimin Fiƙihu ta fi amfani kai tsaye ga mai son yayi ibada fiye da ilimin hadisi, haka ilimin Ruhul Adab kai tsaye tafi amfani ga Muridi fiye da Diwani.
An tashi!