26/12/2025
YADDA ZAKA ZAMA HA€KER CIKIN SAUƘI ⚔️🥇
Ba a zama Ha¢ker a dare daya, kuma ba a zama Ha¢ker ta hanyar sauke wata 'App' guda daya a Playstore. Ha€king ilimi ne, fasaha ce, kuma sana'a ce mai matukar daraja idan ka san hanyar da zaka bi!" 💡⚡
Idan kana son fara koyon Ethical Ha¢king (Ha¢king nagari) da kuma Bug Bounty,
GA matakai 4 da ya kamata kabi,
🥇Koyi Networking (Yadda Intanet ke aiki) 🌐
Kafin ka koyi yadda ake hakar ramin shiga gida, dole ka san yadda kofofin gidan suke. Dole ka fahimci abubuwa kamar IP Addresses, DNS, da kuma yadda HTTP/HTTPS suke aiki.
🥈Koyi Linux Operating System 🐧 Kusan dukkan kayan aikin hackers (Tools) suna tafiya ne a kan Linux (musamman Kali Linux ko Parrot OS). Idan baka san Linux ba, tafiyar zata yi maka wahala.
💻Koyi Programming (Coding)
Ba lallai sai ka zama babban "Software Developer" ba, amma dole ka san yadda ake code.
Fara koyon Python ko JavaScript. Wannan shi zai ba ka damar rubuta naka "scripts" din.
🌐Fahimtar Web Vulnerabilities:
Koyi yadda ake bankado matsaloli kamar SQL Injection, XSS, da IDOR. Wadannan su ne hanyoyin da zaka bi ka samu kudi a matsayin Bug Bounty Hunter.
"Wanne ne daga cikin wadannan matakan kake son fara koyo ?
//////