Rukyelmuaz

Rukyelmuaz Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Rukyelmuaz, Women's clothes shop, Zaria Road funtua, Funtua.

🎬 AI Cartoon Production
🎥 AI Movie-Style Video Creation
✍️ Scriptwriting & Story Development
🎓 AI Training & Content Creation
📢 Brand Promotions & Advertising
🛍️ Women's, Men's & Kids' Fashion
📩 Open for collaborations, AI training, video projects

RIKON KAKA ✍️ Written by Rukayyat Rukyelmuaz CHAPTER 1 YOUNG TALENTED WRITER ASSOCIATION (YOTA) BATSARI LOCAL GOVERNMENT...
28/08/2026

RIKON KAKA

✍️ Written by Rukayyat

Rukyelmuaz

CHAPTER 1

YOUNG TALENTED WRITER ASSOCIATION (YOTA)

BATSARI LOCAL GOVERNMENT

Da sanyin safiyar ranar asabar gari yayi shiru iska mai daɗi tana kaɗawa haɗe da sanyi mai shiga jiki a hankali.

Daga yanayin garin kaɗai ya isa ya tabbatar maka da cewa wannan lokacin damuna ne duk da kasancewar goma na safe yayi amma ka ɗauka karfe takwas din safiya ne.

Gida ne irin ginin kauye jar ƙasa daga waje amma daga ciki kallo ɗaya zaka masa kasan cewa ko a ƙauyen wannan gidan bana ya ku bayi ba ne. Don daga tsarin cikin gidan ka san cewa, Alhamdulillah masu rayuwa a cikin shi tabbas ra'ayin zaman ƙauyen su ka yi.

Dattijuwa ce da, ba ta wuce shekara saba'in ba a duniya ke kai kawo da gani kasan irin jikinsu na mutan da ne. Ga kuma hutu daya samu a jikinta. Kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin kwanciyar hankali da wadatar rayuwa domin kai komo take ba tare da gazawa ko nauyin jiki irin na mutan zamanin nan namu ba.

Ƙarar gudu da hayaniyar yara ta karaɗe gidan tun daga soro kafin su iso inda take tsaye yanda kasan sunayi ne a gabanta alhali ko cikin gidan ba su kai ga shigowa ba.

Muryoyin su ta karaɗe ko ina a cikin gidan da hayaniya.

Fitowar ta kitchen yayi daidai da isowar su gabanta, ta kalle su cikin mamaki kafin ta ce,

“Lafiya dai"?

"Me ya faru kuke wannan ihu haka kuna kirana tun daga soro ba za ku bari ku ƙaraso ba lafiya?”

S**a tsaya suna maida numfashi suna kallon ta. Haki kawai suke saboda tsananin gudun da s**ayi, bayan ɗan lokaci ɗaya daga cikinsu ya ce cikin firgici.

“Kaka Malam Bala mai zikiri ya k**a haisu.
ya hana ta dawowa gida tana can a cikin gona yaki bari ta taho gida".

Fuskar kaka hasatu ta canza cikin rashin jin dadin abinda s**a faɗa ta ce.

"Me haisu ta yi masa"?.

Kallon juna s**ayi kafin wani ya amsa ma ta abinda takeson ji.

"Wai saboda haisu ta hau bishiya ta katso mana mangoro shine ya shigo gonar yasa aka tsareta ya rike ta yaki bari ta taho gida .”

Ya karasa faɗar maganar yana kallon sauran yaran dake bayan shi suma kai s**a ɗaga a tare alamar gaskiya ya faɗa.

Girgiza kai tayi cikin damuwa da tashin hankali domin tunanin ta ɗaya kar a sabauta mata yar tsoka ɗaya amiya yar gudaliyarta.

“To, ku dakata. Bari in saka mayafi, mu je mu ji abin da ya faru".

Kaka ta faɗa tareda faɗawa cikin ɗakin ta da yayi tsaf dashi komi zaune yake a inda ya dace k**ar ba ɗakin dattijuwa ba.

Ɗauko mayafinta, tayi ta yafa a kanta sannan ta fito ganin ta fito sanye da mayafi ne yasa yaran duka s**a juya da gudu suma bayan su tabi domin zuwa ta ganema idon ta abinda ke faruwa.

Ba daɗewa s**a isa gonar inda korayen, ciyawu da sauran anfanin gona s**ayi gore sharr alamar damuna tayi albarka kunya s**a fara tsallekewa kafin su Isa inda bishiyar mangoro din take.

Bishiya ce babba wacce ƴa'ƴan mangoro sunyi sama da ganyen cikin ta sosai wanda in ba kasa doguwar sanda ba ko kuma ka hau sama ba babu yanda za'ayi ka ciro ɗaya daga cikin ƴaƴan cikin ta.

Magidanci ne babba sanye yake da riga yar shara da wani tsohon wando wanda daganin kayan jikinshi zakaba kanka amsar cewa shine Malam Bala mai zikiri, mutum ne wanda baifi shekaru hamsin ba da kallon fuskan shi kawai zakasan yana cikin ɓacin rai.

Rike yake da hannun yar budurwan da, ba tafi karfin shekaru goma sha biyar ba. Fara ce wacce yanayin jikinta kawai zakace bata cin abinci don kuwa irin yaran nan ne da koda ace suna cin abinda sukeso to ba lallai yana musu aiki yanda ya dace ba saboda dan jikinsu da baifi.....ba.

Cika take tana batsewa tana karkaɗa ƙafa ita a dole yan mata anyi mata abinda bataso ga yanayin shagwaɓa na ɗawainiya da ita kanta a ƙasa don babu damuwar komi a fuskanta fa ce ɓacin rai na anci ma ta fuska.

Yara ne s**a fara isa inda take cikin hada baki s**ace, "Haisu yar larabawa".

Sai a wannan lokacin ta d**o da kanta.dayv karamar fuskanta wadda manyan idanunta s**a sauka akan wanda s**a kira sunanta kafin su ƙara wata magana. Kaka ta karaso gurin da suke cikin ɓacin rai ta ce.

“Malam Bala, ko mene ne haisu ta yi ai ka sanar da ni ba wai ka tsare ta ba me ya sa ka tsare ta haka"?.

Mutumin da aka kira da Malam Bala ya nuna haisu da yatsa cikin fushin daya bayyana ƙarara a fuskan shi ya ce.

“Kaka Hasatu wannan yarinyar ba ƙaramin tashin hankali ba ce a cikin kauyen nan da gonakin mutane kalli abin da ta jawo mini".

Ya ƙarasa maganar yana nuna kasan gonar da ƴa'ƴan mangoron da bai gama nunaba duk ya fado birjit a kasa ya cigaba da magana cikin fada

"Ta kawo mini yara sun taru a gonata suna jifan juna da duwatsu suna hawa bishiyoyi suna karya rassan mangoro Ita ce ta jagoran ce su wallahi ba zan ƙyale wannan abun ba.”

Haisu ta ɗago kanta cikin shagwaɓa ta kalli kaka a maraice k**ar zatayi kuka cikin salon shagwaɓa da kwarewa a sarrafa kalami ta ce.

“Kaka... ai mangoro ne ya biya mana rai, kuma ba za mu cutar da kan mu ba shi ya sa muka tsinka kaɗan ai har lada zai samu saboda ya ciyar da musulmai.”

Kaka ta saki murmushi a hankali ta ce .
“Rabu da shi ke, haisu.”

Juyawa tayi ta kalli Malam Bala da tuni ya sake baki yana kallon ikon Allah sangarta da la'lacewa ta wannan yarinyar maganar kaka ce ta dawo dashi daga tunanin daya ɗauke mishi hankali.

Cikin halin ko in kula take magana.

“Malam Bala, ko haƙƙin maƙwabta ba ka saukewa amma ka tsare marainiyar Allah saboda mangoro?”

Haisu ta kasa ɓoye murmushinta domin ta san indai akwai kaka a gari, to ba ta da damuwar komai.

Fa kaitar idon kaka tayi ta ɗan yi wa malam bala gwalo abin da ya ƙara hura masa wutar fushin da yake ciki na ɓarnar da s**a yi masa.

Malam Bala ya girgiza kai ya kalli kaka da ta gama sauke mishi hadda akan bin bayan ƙarya.

“Yanzu kaka Hasatu abin da za ki faɗa kenan duk ɓarnar da wannan shaiɗaniyar tayi min ya tafi a banza kenan?”

Ya ɗaga murya cikin fushi wanda ita kanta sarkin ɓarnar ta tsorata dajin yanayin da yayi maganar.

“Wallahi sai kun biya ni kuɗin mangoron da ta la'lata Idan ba haka ba zan kai ta gaban mai gari.”

Ya karasa maganar yana kallon kaka da ta saki baki tana kallon yanda yake fitina haka k**ar wanda aka kwashewa anfanin gona gaba ɗaya.

Fuskar kaka ta sauya da jin furucin da malam bala mai zikiri ya yi akan jikarta wadda ta fi so take jin za ta iya kona garin batsari akanta zata iya faɗa da kowa har liman bataki ya mutu ba akan jikarta ta rayu ba.

Cikin ɓacin rai da furucin da yayi ta ce,

“Saboda mangoro za ka kai min haisu gaban mai gari? wannan kam ba zai yiwu ba.”

Malam Bala bai sauya matsayarsa ba.

“To ku biya kuɗin ɓarnar da tayi Idan ba haka ba, ba zan fasa kai ta wurin mai gari ba.”

Kaka Hasatu ta sauke numfashi a zuciyar ta, ta ce inda kasan kudin kake so aida baka tsareta ba in akazo kace tayima ɓarna a biyaka ma biyanka zansa ayi a fili kuma ta ce..

“To, shikenan. Ka saketa yanzu ka tafi anjima idan mahaifinta ya kira zan sa ya turo kuɗin mangoron sai haisu taje gurin mai na'urar cirewa (P.O.S) ta kawoma tsabar kudin .

"Zata ta kawo maka, ko kuma kai da kanka ka zo gida ka karɓa.” Kaka ta faɗa tare da kallon malam bala.

Malam Bala ya yi shiru na ɗan lokaci daga ƙarshe ya ce,

“Wallahi ki ja mata kunne kar na sake ganin ƙafarta a gonata tunda ba mutuniyar arziki bace.”

Yana kai nan a maganar shi ya juya ya fice daga gonar ya bar bakin kaka a buɗe tana kallon bayan shi.

Yara s**a fara tsalle da murna saboda an saki haisu.

Kaka ta kalli haisu ta ce,

“Don Allah Hafsatu yaushe za ki girma? hawan bishiya ba na mata ba ne.”

Cikin shagwaɓa ta turo baki ta ce

“Ni fa ya biya mana rai ne kuma ba zan bar ƴan tawaga ta su ga abu suna so ban yi musu ba.”

Rufe bakin ta ke da wuya yara s**a fasa ihu da murna.

Sai haisu ƴar larabawa, “Yeeeeeeeeeeee!” cikin farin ciki da kirarin da s**a mata ta ce,

“Yara, ku faɗa ku ƙara nice ɗaya tilo duk fadin batsari babu wata ƴar larabawa sai ni!”

Duk faɗin garin batsari da gani babu wata. Nice nan ƴar larabawa don haka yau dole ku ci kifin Isiya me dala’ilu.

Cikin gwarin gwui'war ta, na sangarta ta ce,

“ku je"

Yanzu za mu je gida da Kaka yunwa nake ji zan samo kuɗin kifin mu haɗu a dandalin.

Yaran na jin haka s**a ƙara fasa ihu na farin ciki. Masu ta ya s**a ɗauka s**a gara, duka s**a fita gonar da gudu.

Kaka ta ja hannun jikarta ta fita da ita daga gonar.

Amma da kafiya irin ta haisu sai da ta ɗauko mangoro huɗu, ta sa a hijab tana tafe tana mutsu'mutsu kaka ce ta ji tana mutsu-mutsu.

Cikin rashin yarda ta ce,

“Hafsatu, me kika ɗauko?

Baki ta turo cikin shagwaɓar da aka raine ta a ciki ta ce.

“Hakki na'ne na ɗauko.”

Dogon salati kaka ta ja sannan ta ce,

“Kin san Allah ki watsar da su ko na yi maganin ki.”

“Allah ba zan watsar ba. Ta ba kaka amsa cikin sangarta.

Amsar da ta bata ne ya bata damar juyawa ta kalli fuskarta duk da kasancewar tasan zata iya aikata abinda yafi wannan ba sabon abu bane a gurin haisu.

Kallonta tayi batare da ta ce komi ba ƙara rike hannun ta tayi sosai cikin nata yanda kasan an ce wani zai zagayo ta baya ya amshe ma ta ita.

Domin samun next page ku shiga channel dina
Ga link na channel a
nd group ku shiga domin samun next page

https://chat.whatsapp.com/ImNMf843o0l7d159gPngxr



Follow the 📚 RUKYELMUAZ LITERARY HOUSE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbDEcdKK5cDNt98YsD3Z

27/08/2026

Rikon kaka part 7

26/08/2026

Maraici yanzu nu'aimat zatasan daɗin zama da nu'aim

26/08/2026

Maraici next part abinda nu'aim yayi yafi komi burgeni gaskiya nu'aimat tanada hakuri

Kana neman furniture ko kayan gida masu kyau, sabbi ko second-hand, amma baka samu ba ko kaje kasaya kuma basu yi ma ƙwa...
24/08/2026

Kana neman furniture ko kayan gida masu kyau, sabbi ko second-hand, amma baka samu ba ko kaje kasaya kuma basu yi ma ƙwari ba kana son ka same su cikin sauƙi ba tare da kasha wahalar nema ba? Ko kina son ki bada kayan ɗakin ki kiyi ciko ki amsa wasu ne?? Kukan ki ya ƙare domin kuwa,ka zo inda ya dace! 🏡🛋️

A FAIRLY USED & NEW ITEMS – MU NA SAYE, MU NA SAYARWA, muna da nau’o’in kaya daban-daban da s**a haɗa da:

🛏️ Bed & bedroom furniture
🪑 Chairs da sauran furniture
🧳 Travel akwatin / luggage
❄️ Fridge
🪑 Kayan kitchen & kayan gida
📺 TV da sauran kayan lantarki
🧸 Kayan wasan yara
🏠 Da sauran kayan furniture na gida iri-iri

✨ Abu mafi kyau kuwa?
Idan kana neman wani kaya na musamman da baka gani a hotunanmu ba, kada ka damu!

👉 Ka shiga group ɗinmu ta link ɗin da ke ƙasa, ka turo mana sako ko hoton kayan da kake nema. Za mu duba maka mu taimaka maka ka same shi cikin farashi me sauki. 💯

Sannan zaka iya shiga group dinmu domin samun kayan da s**a dace da gidan ka zakaga kaya iri daban daban nau'i nau'i

📲 WhatsApp: 09030637067

Kada ka jira sai ka ga kayan da kake nema kafin ka shigo group — shiga yanzu, ka faɗi abin da kake buƙata! 🔥

https://chat.whatsapp.com/Gouj81Tk7PQ5Koszv3VDLC?s=cl&p=i&mlu=4

🏷️ FAIRLY USED & NEW ITEMS
Muna Saya • Muna Sayarwa • Muna Taimakawa Ka Samu Abin da Kake Nema

👇 LINK ƊIN GROUP YANA NAN ƘASA — Danna ka shiga yanzu! 👇

24/08/2026

Soyayya Dadi in kayi dace da masoyin gaskiya

23/08/2026

Maraici next part yaufa ya k**ata ayima Nu'aimat kyauta gaskiya don mance abinda nu'aim ya yi mata cikin sauki nada wahala

📢 Assalamu Alaikum masoyan shirin MARAICI ❤️Na ga wasu daga cikinku suna tambaya tare da yin korafi cewa me ya sa bana f...
23/08/2026

📢
Assalamu Alaikum masoyan shirin MARAICI ❤️
Na ga wasu daga cikinku suna tambaya tare da yin korafi cewa me ya sa bana fitar da Maraici kullum, ko kuma me ya sa wasu episodes ba sa yin tsawo.
Ina so in yi muku bayani kaɗan. ❤️
A yanzu, app ɗin da nake amfani da shi wajen haɗa wannan drama yana aiki ne da credits wannan credit. A wata, innayi subscribe ana ba ni 1,000 credits kawai, kuma kowane scene na video yana cin credits 15 or 20. Wani lokacin ma app ɗin yana lalata wasu scenes, wanda hakan ke sa na sake gyarawa ko na sake ƙirƙirar scene ɗin.
Saboda haka, idan zan riƙa yin Maraici kullum kuma mai tsawo k**ar yanda kuke so , credits ɗin ba za su ishe ni ba a wata.
🎬 Hada wannan shiri yana cin kuɗi, lokaci sosai.
Amma idan kuna son Maraici ya ci gaba kuma kuna son ganin episodes masu kyau da tsawo, kuna iya support ɗin shirin ta hanyar Subscribe. ❤️
Support ɗinku zai taimaka wajen ci gaba da samar da sabbin episodes da kuma rage matsalar credits da nake fuskanta.
🙏 Ba dole ba ne, amma duk wanda ya yi niyya zai iya support, ya taimaka wajen ganin Maraici ya ci gaba.
Na gode sosai da ƙaunarku, haƙurinku da kuma yadda kuke kallon shirin. ❤️
Allah ya saka muku da alheri.
📌 Domin support https://www.facebook.com/Rukyelmuaz1/subscribenow?surface=pinned_comments

Allah yasa mu anfana da juna Ameen ya Allah Big shout out to my newest top fans! 💎 Khadijat Hussaini, Samira Sulaiman, A...
23/08/2026

Allah yasa mu anfana da juna Ameen ya Allah

Big shout out to my newest top fans! 💎 Khadijat Hussaini, Samira Sulaiman, Aysha Annur, Bilkisu Aliyu, Naja Atu Abubakar, Binta Kaura, Oum Ahyaan, Khadeehanah Khamees, Unique Sawwamarh Kawwamarh, Farida Muhammad Adam, Teemah Abubakar, Khadijah Abdulrashid, Aminatu Kabir Minasco, Oum Abdurrahman, Rukayya Muhammad, Na Esh Abubakar, Bashir Muhammad Magaji, Teema M Sani, Ahamad Rabi, Fatima Zahra, Meerha Umar, Dahiru Musa

Drop a comment to welcome them to our
community,

Address

Zaria Road Funtua
Funtua

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Rukyelmuaz posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share