Rukhsah Global Empire

Rukhsah Global Empire Your Gateway to Global Excellence We specialized in serving whole sales and retail on: foreing shoes, caps, suits, etc

SIRRIN SAMUN KWASTOMA MAI DAWOWA AKAI-AKAI1️⃣ Yi hulɗa da su da gaskiya – kar ka taɓa yaudara.2️⃣ Ka riƙa bada ƙarin ser...
02/10/2025

SIRRIN SAMUN KWASTOMA MAI DAWOWA AKAI-AKAI

1️⃣ Yi hulɗa da su da gaskiya – kar ka taɓa yaudara.
2️⃣ Ka riƙa bada ƙarin service ko shawara koda ba a biya ka ba.
3️⃣ Ka dinga tambayar su ra’ayi: “Me za mu inganta?”.
4️⃣ Ka tuna da su bayan sayayya – small message of thanks ko promo.
5️⃣ Ka kula da ingancin kaya a kowane lokaci.

👉 Koda kwastoma ya tafi, ka tabbata zai dawo saboda irin yadda ka kula da shi.
🤞 Ka sake fuska ka koyi yiwa kwastoma Godiya

02/10/2025
🌍ABUBUWA 3 DA KASUWANCI A DUNIYA YAKE KOYA MANA1️⃣ Digital Transformation – A yau, mafi yawan manyan kamfanoni suna amfa...
01/10/2025

🌍ABUBUWA 3 DA KASUWANCI A DUNIYA YAKE KOYA MANA

1️⃣ Digital Transformation – A yau, mafi yawan manyan kamfanoni suna amfani da online platforms wajen sayar da kayayyaki. Idan kasuwanci baya kan internet, yana rasa dama mai yawa.

2️⃣ Customer First – A duniya, duk kasuwanci da ya fi bauta wa kwastomomi shi yafi tashi. Misali: Amazon da Jumia.

3️⃣ Small Start, Big Growth – Manyan kamfanoni kamar Apple da Dangote sun fara da ƙarami amma sun yi haƙuri s**a girma.

👉 Darasi: Ka fara da abin da kake da shi, amma ka yi shi da hikima + consistency.

SABUWAR PROMO Daga: RUKHSAH GLOBAL EMPIRE 📌 Data & Recharge Cards👉 MTN, Airtel, Glo, 9mobile available.👉 Farashi mai rah...
30/09/2025

SABUWAR PROMO
Daga: RUKHSAH GLOBAL EMPIRE

📌 Data & Recharge Cards
👉 MTN, Airtel, Glo, 9mobile available.
👉 Farashi mai rahusa – ka samu karin data da kudi kadan.

📌 Soft Drinks & Bread
👉 Sanyi kamar kankara ❄
👉 Farashi mai sauƙi, inganci tabbatacce.

📞 Tuntube mu: 07039852682

HANYOYI 5 DA ZAKA  IYA RAGE KASHE KUD'I BA DOLE BA1️⃣ Ka daina sayen abin da baka buƙata kawai don ganin ya yi kyau.2️⃣ ...
30/09/2025

HANYOYI 5 DA ZAKA IYA RAGE KASHE KUD'I BA DOLE BA

1️⃣ Ka daina sayen abin da baka buƙata kawai don ganin ya yi kyau.
2️⃣ Ka riƙa yin budget a kowane mako kafin ka kashe.
3️⃣ Ka rage fita yawon ci abinci a waje, ka fi dafa naka a gida 🍲.
4️⃣ Ka daina bin trends (sabuwar waya, kaya, ko fashion) idan babu buƙata.
5️⃣ Ka fara adana kuɗi kadan-kadan koda ₦200 ne a rana.

👉 Sirrin kudi ba wai samun yawa bane, sai dai iya sarrafa wanda kake da shi.

🤞A shekarar 2023 na samu karfin guiwar gina sabuwar kwantaina (container/shop) ta hanyar ajiye N20 a duk transaction da nayi a POS, Wanda na tara sama da N60,000 cikin qaramin lokaci.

🤞A farkon shekarar 2024 cikin qaramin lokaci na tara kusan 30k na sayi fanka (ceiling fan) na saka a shagona, kuma na biya Departmental fee a GSU ta hanyar commission da nake samu idan na sayar da katin waya (momo agent) N2 ko N3



-Mal. Abdulwahab Nasir Isah
MD/CEO Rukhsah Global Empire

Yadda zaka fara sana’a da ₦5,000Idan kana da ƙananan kudi amma kana sha’awar kasuwanci, zaka iya fara da:1️⃣ Siyar da re...
29/09/2025

Yadda zaka fara sana’a da ₦5,000

Idan kana da ƙananan kudi amma kana sha’awar kasuwanci, zaka iya fara da:
1️⃣ Siyar da recharge card & data 📱
2️⃣ Siyar da soft drinks & ruwa a wuraren taro 🥤
3️⃣ Siyar da snacks ko abinci a kusa da makaranta/office 🍞🍗
4️⃣ Online reselling (sayen kaya daga jumia/kasuwa → sayarwa akan Facebook/WhatsApp)

👉 Babban sirri shi ne ka fara da abin da kake da shi, sannan ka riƙa sake juyar da ribarka.

A shekarar 2022 ina da 11k only na sayi Lema 6k da table 5k na fara sana'ar POS da aron 30k daga wajen wani abokina, aka bani bashin POS terminal, zuwa yanzu dai Alhamdulillah 🙏

-Malam, Abdulwahab Nasir Isah

Nasara tana zuwa ne ga wanda baya daina gwadawa. Duk wanda ya tsaya tsayin daka, to ba shakka zai ga sakamako.👉 Ka tuna,...
29/09/2025

Nasara tana zuwa ne ga wanda baya daina gwadawa. Duk wanda ya tsaya tsayin daka, to ba shakka zai ga sakamako.

👉 Ka tuna, duk wani babban kamfani da kake gani, ya fara ne da ƙaramar mafarki. Ka ci gaba da ƙoƙari yau, domin gobe naka ne.

Wani Miji ya tambayi matarsa:“Me mutum yake rasawa idan ya yi aure, kuma me yake samu?”Matar ta yi murmushi da hikima ta...
31/08/2025

Wani Miji ya tambayi matarsa:
“Me mutum yake rasawa idan ya yi aure, kuma me yake samu?”

Matar ta yi murmushi da hikima ta ce:
“Namiji yana rasa zaman kansa na samartaka, ’yancin yanke ƙananan hukunci shi kaɗai, da kuma damar yin abubuwa ba tare da yin la’akari da nauyin da ya rataya a kansa ba. Amma a gefe guda kuma, yana samun abokiyar rayuwa, uwa ga ’ya’yansa, gida da ke cike da dumi da annashuwa.”

Sai mijin ya yi dariya ya ce: “To fa game da farin ciki fa?”
Ta amsa tana murmushi: “Farin ciki, ya kai masoyina, mu ne kanmu ke gina shi. Idan muka ɗauki aure a matsayin rabon ɗaukar nauyi tare da raba farin ciki da nasara, to za mu kasance da farin ciki. Amma idan muka gan shi a matsayin asara, to kullum za mu kasance cikin rashin gamsuwa da asara.”

Mijin ya yi tunani a kan maganarta, sannan ya tambaya:
“Kin fi sona ko kuwa kina son ’ya’yanki fiye da ni?”

Ta amsa ba tare da jinkiri ba:
“’Ya’yana.”

Sai mijin ya yi mamaki ya ce: “Me ya sa?”
Ta ce: “Saboda su jinin jikina ne, ruhina ne.”
Ya ce yana murmushi: “Ni fa?”
Ta yi dariya ta ce: “Kai abokin tafiya ne a wannan hanya, wani lokaci kana faranta min rai, wani lokaci kuma kana bakanta min!”

Bayan wannan tattaunawar, mijin ya zauna yana tunani: Shin da gaske ne alaƙar ma’aurata tana ginuwa ne akan sadaukarwa? Kuma shin waɗannan sadaukarwar ana darajasu da gaske?

A cikin al’ummarmu, ana ganin mace ce ginshiƙin gida. Ita ce uwa da take yin daren tsakar dare tana kula, tana dafa abinci, tana koyarwa, tana tarbiyya, tana tsabtace gida, tana jinya, tana tallafa wa kowa cikin gida. Ita ce take ɗaukar dukkan nauyin rayuwa cikin shiru amma tana murmushi a fuska duk da gajiyarta.

Idan yaro ya yi rauni a makaranta, sai a ce: “Ina mahaifiyar tasa?”
Idan yaro bai da hali mai kyau, sai a ce: “Uwa ba ta tarbiyyantar da shi ba!”
Idan miji bai da farin ciki, sai a ce: “Matar ba ta yi iya kokarinta ba!”
Idan gida ba shi da tsafta, sai a ce: “Uwa ba ta yin aikinta kazamiya ce!”

Amma gaskiyar magana, mace tana yin aiki babba kwarai. Ita ce makaranta a zahiri, amma har ma fiye da haka. Ita ce likita da ke warkar da rauni, malama da ke dasa kyawawan dabi’u, mai ba da shawara, jinya mai kula da ƙanana da manya. Ita ce ɗakin karatu da ke ɗauke da hikimar rayuwa, ita ce zuciyar da ke bugawa da sadaukarwa, ita ce kashin bayan gida da al'umma.

Saboda haka, gaisuwa daga zuciya ga kowace mace da ke ɗaukar nauyin rayuwa babba da ƙanana, wadda take sadaukar da jin daɗinta da farin cikinta saboda wasu, wadda ke kawo farin ciki ga kowa duk da ƙalubalen datake fuskanta.

Ya ke mace, ki yi murmushi ki kuma yi alfahari da kanki, domin ke ce mai haifar da al’umma, tushen ƙarfi da ƙauna a duniya, Kamal yana muku jinjina

KO KA SAN.........Yaƙin Chimpanzee mai suna "Gombe Chimpanzee War" ya faru ne tsakanin 🦧🐒 birran yanki biyu na dajin Gom...
31/08/2025

KO KA SAN.........

Yaƙin Chimpanzee mai suna "Gombe Chimpanzee War" ya faru ne tsakanin 🦧🐒 birran yanki biyu na dajin Gombe mai suna "Gombe Stream National Park" kuma sun ɗauki tsawon shekara 4, da wata 4 da kuma sati biyu ana gwabza yaƙi tsakanin waɗannan birran, wanda aka zubar da jini, aka yi kashe-kashe.
Yaƙin ya fara ne tun daga ranar 22 ga watan Janairu ta shekarar 1974 zuwa 5 ga watan Yuni na shekarar 1978.

A'a, dakata, wannan garin Gomben fa ba Gombe madinar Nigeria ake nufi ba! 😅 A'a, garin Gombe ta ƙasar Tanzaniya ne. Akwai Gombe ma a ƙasar Uganda, har da makaranta mai suna "Gombe Junior & High School" (kamar yadda a Gomben Nigeria akwai "Gombe High School", kuma ba wai baturen nan Mr. Terry wanda ya kafawa Dr. Sulaiman Kumo makarantar shi ne ya je can Uganda ya kafa waccar ba, kawai sunan ne ya zamo daya). Sannan akwai kuma Gombe a Kinshasa, babban birnin kasar DRC.

✍️ 2022

Address

Jekadafari Gombe
Gombe

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Rukhsah Global Empire posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share