Littafin mai sarki Hausa group

Littafin mai sarki Hausa group Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Littafin mai sarki Hausa group, Men's clothes shop, 07048317077, Jada.

27/01/2023
04/01/2023

HI

04/01/2023

I miss u fr

04/01/2023

Gaisuwa
1 Daga Bulus, bawan Yesu Almasihu, manzo kirayayye, keɓaɓɓe domin yin bisharar Allah, 2 wadda Allah ya yi alkawari tun dā, ta bakin annabawansa a cikin Littattafai masu tsarki. 3 Bishara ɗin nan a kan Ɗansa ce, Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ga jiki shi zuriyar Dawuda ne, 4amma ga tsarkinsa na ruhu shi Ɗan Allah ne, da iko aka ayyana shi haka ta wurin tashinsa daga matattu. 5 Ta wurinsa ne muka sami alheri da kuma manzanci, saboda sunansa dukan al'ummai su gaskata su yi biyayya, 6 a cikinsu kuma har da ku da kuke kirayayyun Yesu Almasihu. 7 Daga Bulus zuwa ga dukan ƙaunatattun Allah da kuke a Roma, tsarkaka kirayayyu.

Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

Nufin Bulus Ya Ziyarci Roma
8 Da farko dai ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Almasihu saboda ku duka, domin ana baza labarin bangaskiyarku a ko'ina a duniya. 9 Domin kuwa Allah, wanda nake bauta wa a ruhuna ta yin bisharar Ɗansa, shi ne mashaidina a kan yadda kullum ba na fasa ambatonku a cikin addu'ata, 10 ina addu'a, ko ta ƙaƙa, da yardar Allah, a yanzu kam, in sami arzikin zuwa wurinku. 11 Domin ina ɗokin ganinku, in ni'imta ku da wata baiwa ta ruhu, domin ku ƙarfafa. 12Wato ni da ku, mu ƙarfafa juna ta bangaskiyarmu, tawa da taku. 13 Ina so ku sani 'yan'uwa, na sha ɗaura niyyar zuwa wurinku, ko da yake har yanzu ba a yardar mini ba, domin ku ma in sami amfani a gare ku, k**ar yadda na samu a cikin al'ummai. 14 Akwai hakkin Helenawa, da na bare, da na masu ilimi, da na jahilai duka a kaina. 15 Saboda haka a gwargwadon iyawata, ina da himma ku ma in yi muku bisharar, ku da kuke a Roma.

Ikon Bishara
16 Gama ba na jin kunyar bishara, domin ita ce ikon Allah mai kai kowane mai ba da gaskiya ga samun ceto, Yahudawa da fari, sa'an nan kuma al'ummai. 17 Gama bishara ɗin ta bayyana wata hanyar samun adalci a gaban Allah, hanyar nan kuwa ta bangaskiya ce, tun daga farko har zuwa ƙarshe, yadda yake a rubuce cewa, “Wanda yake da adalci ta wurin bangaskiya zai rayu.”

Laifin 'Yan Adam
18 Gama ana bayyana fushin Allah daga Sama, a kan dukan rashin bin Allah, da aikin mugunta na mutanen da suke danne gaskiya, ta aikin muguntarsu, 19 Domin abin da za a iya sani a game da Allah a bayyane yake a gare su, gama Allah ne ya bayyana musu shi. 20 Gama tun daga halittar duniya al'amuran Allah marasa gănuwa, wato ikonsa madawwami, da allahntakarsa, sun fahimtu sarai, ta hanyar abubuwan da aka halitta kuma ake gane su. Saboda haka mutane sun rasa hanzari. 21 Domin kuwa ko da yake sun san da Allah, duk da haka ba su ɗaukaka shi a kan shi Allah ne ba, ba su kuma gode masa ba. Sai tunaninsu ya wofince, zuciyarsu marar fahimta kuma ta duhunta. 22 Suna da'awa cewa, su masu hikima ne, sai s**a zama wawaye. 23 Sun sauya ɗaukakar Allah marar mutuwa da misalin siffar mutum mai mutuwa, da ta tsuntsaye, da ta dabbobi, da kuma ta masu jan ciki.

24 Saboda haka Allah ya sallama su ga rashin tsarkaka ta mugayen sha'awace-sha'awacensu, har su wulakanta jikinsu a junansu, 25 saboda sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, har yi wa halitta ibada, sun kuma bauta mata, sun ƙi su yi wa Mahalicci, shi wanda yabo ya tabbata a gare shi har abada. Amin.

26 Don haka Allah ya sallama su ga mugayen sha'awace-sha'awace masu banƙyama, har matansu s**a sauya ɗabi'arsu ta halal, da wadda take ta haram. 27 Haka kuma maza s**a bar ma'amalarsu ta halal da mata, jarabar juna ta ɗebe su, maza da maza suna aikata rashin kunya, suna jawo wa kansu sak**ako daidai da bauɗewarsu.

28 Tun da yake sun ƙi su yarda su san Allah, Allah ya sallama su ga halin banza, su aikata abin kunya. 29 Su masu aikata rashin adalci ne ƙwarai, da mugunta, da kwaɗayi, da ƙeta. Masu hassada ne, da kisankai, da jayayya, da ha'inci, da kuma nukura gaya matuƙa. Macizan ƙaiƙayi ne, 30 da masu yanke, da maƙiyan Allah, da masu cin mutunci, da masu girmankai, da masu ruba, da masu haddasa mugunta, da marasa bin iyaye, 31 da marasa fahimta, da masu ta da alkawari, da marasa ƙauna, da marasa tausayi. 32 Waɗannan kuwa ko da yake sun san shari'ar Allah cewa masu yin irin waɗannan abubuwa, sun cancanci mutuwa, duk da haka, ba aikata su kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon masu yinsu.

03/01/2023

Hello

03/01/2023

Send a message to learn more

03/01/2023

Kalman Ya Zama Mutum
1 Tun fil'azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne. 2 Shi ne tun fil'azal yake tare da Allah. 3 Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da s**a kasance, sai ta game da shi. 4 Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane. 5 Haske na haskakawa cikin duhu, duhun kuwa bai rinjaye shi ba.

6 Akwai wani mutum da Allah ya aiko, mai suna Yahaya. 7 Shi fa ya zo shaida ne, domin ya shaidi hasken, kowa yă ba da gaskiya ta hanyarsa. 8Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken.

9 Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum. 10 Dā yana duniya, duniyar ta wurinsa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba. 11Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama'a tasa kuwa ba ta karɓe shi ba. 12 Amma duk iyakar waɗanda s**a karɓe shi, wato, masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama 'ya'yan Allah, 13 wato, waɗanda aka haifa ba daga jini ba, ba daga nufin jiki ko nufin mutum ba, amma daga wurin Allah.

14 Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.

15 Yahaya ya shaida shi, ya ɗaga murya ya ce, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ ” 16 Dukanmu kuwa daga falala tasa muka samu, alheri kan alheri. 17 Domin Shari'a, ta hannun Musa aka ba da ita, alheri da gaskiya kuwa ta wurin Yesu Almasihu s**a kasance. 18 Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai. Makaɗaicin Ɗa, wanda yake yadda Allah yake, wanda kuma yake a wurin Uba, shi ne ya bayyana shi.

Shaidar Yahaya Maibaftisma
(Mat 3.1-12; Mar 1.1-8; Luka 3.1-18)
19 Wannan kuwa ita ce shaidar Yahaya, wato, sa'ad da Yahudawa s**a aiki firistoci da Lawiyawa daga Urushalima su tambaye shi, ko shi wane ne. 20 Sai ya faɗi gaskiya, bai yi musu ba, gaskiya ya faɗa ya ce, “Ba ni ne Almasihu ba.” 21 Sai s**a tambaye shi, “To, yaya, Iliya ne kai?” Ya ce, “A'a, ba shi ba ne.” S**a ce, “Kai ne annabin nan?” Ya ce, “A'a.” 22Sai s**a ce masa, “To, wane ne kai, domin mu sami amsar da za mu mayar wa waɗanda s**a aiko mu? Me kake ce da kanka?” 23 Ya ce, “Ni murya ce ta mai kira a jeji, mai cewa, ‘Ku miƙe wa Ubangiji tafarki,’ yadda Annabi Ishaya ya faɗa.”

24Su kuwa, Farisiyawa ne s**a aiko su. 25Sai s**a tambaye shi s**a ce, “To, don me kake yin baftisma in kai ba Almasihu ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?” 26Sai Yahaya ya amsa musu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake baftisma, amma da wani nan tsaye a cikinku wanda ba ku sani ba, 27 shi ne mai zuwa bayana, wanda ko maɓallin takalminsa ma, ban isa in ɓalle ba.” 28 An yi wannan a Betanya ne, a hayin Kogin Urdun, inda Yahaya yake yin baftisma.

“Ga Ɗan Rago na Allah”
29 Kashegari Yahaya ya tsinkayo Yesu na nufo shi, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah, wanda zai ɗauke zunubin duniya! 30 Wannan shi ne wanda na ce, ‘Wani yana zuwa bayana, wanda ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ 31Dā kam, ban san shi ba, sai domin a bayyana shi ga Isra'ila na zo, nake baftisma da ruwa.” 32 Yahaya ya yi shaida ya ce, “Na ga Ruhu na saukowa k**ar kurciya daga sama, ya kuma zauna a kansa. 33 Dā kam, ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa, shi ne ya ce mini, ‘Wanda ka ga Ruhun na sauko masa, yana kuma kasance a kansa, shi ne mai yin baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’ 34 Na kuwa gani, na kuma yi shaida, cewa wannan Ɗan Allah ne.”

Almajiran Yesu na Farko
35 Kashegari kuma Yahaya na tsaye da almajiransa biyu. 36 Yana duban Yesu na tafiya, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah!” 37Almajiran nan biyu s**a ji ya faɗi haka, sai s**a bi Yesu. 38 Yesu ya waiwaya ya ga suna biye da shi, sai ya ce musu, “Me kuke nema?” S**a ce masa, “Ya Rabbi, wato Malam ke nan, ina kake da zama?” 39Sai ya ce musu, “Ku zo ku gani.” Sai s**a je s**a ga inda yake da zama, s**a kuwa yini tare da shi. Wajen ƙarfe huɗu na yamma ne kuwa. 40Ɗaya daga cikin biyun nan da s**a ji maganar Yahaya s**a kuma bi Yesu, Andarawas ne, ɗan'uwan Bitrus. 41 Sai ya fara samo ɗan'uwansa Bitrus, ya ce masa, “Mun sami Almasihu,” wato shafaffe. 42 Sai ya kai shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi, ya ce, “Wato kai ne Saminu ɗan Yahaya? Za a kira ka Kefas,” wato Bitrus.

Yesu Ya Kira Filibus da Nata'ala
43 Kashegari Yesu ya yi niyyar zuwa ƙasar Galili. Sai ya sami Filibus, ya ce masa, “Bi ni.” 44 Filibus kuwa mutumin Betsaida ne, garin su Andarawas da Bitrus. 45 Filibus ya sami Nata'ala, ya ce masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta labarinsa a Attaura, annabawa kuma s**a rubuta labarinsa, wato Yesu Banazare, ɗan Yusufu.” 46 Nata'ala ya ce masa, “A iya samun wani abin kirki a Nazarat kuwa?” Sai Filibus ya ce masa, “Taho dai, ka gani.” 47 Yesu ya ga Nata'ala na nufo shi, sai ya yi zancensa ya ce, “Kun ga, ga Ba'isra'ile na gaske wanda ba shi da ha'inci!” 48Nata'ala ya ce masa, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Tun kafin Filibus ya kira ka, sa'ad da kake gindin ɓaure, na gan ka.” 49 Sai Nata'ala ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, kai Ɗan Allah ne! Kai Sarkin Isra'ila ne!” 50Yesu ya amsa ya ce, “Wato, domin na ce maka na gan ka a gindin ɓaure ne kake ba da gaskiya? Ai, za ka ga al'amuran da s**a fi haka ma.” 51 Yesu kuma ya ce masa, “Lalle hakika, ina gaya muku, za ku ga sama ta dāre, mala'ikun Allah suna hawa da sauka ga Ɗan Mutum.”

Gabatarwa1Tun da yake mutane da yawa sun ɗauka su tsara labarin waɗannan al'amura da s**a tabbata a cikinmu, 2 daidai ya...
03/01/2023

Gabatarwa
1Tun da yake mutane da yawa sun ɗauka su tsara labarin waɗannan al'amura da s**a tabbata a cikinmu, 2 daidai yadda waɗanda suke shaidu tun farkon al'amari, masu hidimar Maganar, s**a rattaba mana, 3 da yake kuma na bi diddigin kowane abu daidai tun farko, ni ma dai na ga ya kyautu in rubuta maka su bi da bi, ya mafifici Tiyofalas, 4 domin kă san ingancin maganar da aka sanar da kai baki da baki.

An Yi Faɗin Haihuwar Yahaya Maibaftisma
5 A zamanin Hirudus, Sarkin Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na ƙungiyar Abaija. Yana auren wata a cikin zuriyar Haruna, sunanta Alisabatu. 6 Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna bin umarnin Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi. 7Amma ba su da ɗa, don Alisabatu bakararriya ce, dukansu biyu kuma sun tsufa.

8 Ana nan, wata rana Zakariya na kan hidima tasa ta firist, a sa'ad da hidimar ta kewayo kan ƙungiyarsu, 9 bisa ga al'adar hidimar firistoci, sai kuri'a ta nuna shi ne mai shiga Haikalin Ubangiji, ya ƙona turare. 10 A lokacin ƙona turare kuwa duk taron jama'a suna waje, suna addu'a, 11 sai wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare shi, yana tsaye a dama da bagadin ƙona turare. 12 Da Zakariya ya gan shi ya firgita, tsoro ya k**a shi. 13 Amma mala'ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro Zakariya, an karɓi addu'arka, matarka Alisabatu za ta haifa maka ɗa, za ka kuma sa masa suna Yahaya.

14 Za ka yi murna da farin ciki,

Mutane da yawa kuma za su yi farin ciki da haihuwa tasa.

15 Domin zai zama mai girma a wurin Ubangiji,

Ba kuwa zai sha ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba.

Za a cika shi da Ruhu Mai Tsarki

Tun yana cikin uwa tasa.

16Zai kuma juyo da Isra'ilawa da yawa ga Ubangiji Allahnsu.

17 Zai riga shi gaba cikin ruhu da iko irin na Iliya.

Yă mai da hankalin iyaye a kan 'ya'yansu,

Yă kuma juyo da marasa biyayya su bi hikimar adalai,

Ya tanada wa Ubangiji jama'a, ya same su a shirye.”

18 Sai Zakariya ya ce wa mala'ikan, “Ta ƙaƙa zan san haka? Ga ni tsoho, maiɗakina kuma ta kw

03/01/2023

Ya ubangiji a gare ka muke dogara kadaka boyemin fuskaka

Address

07048317077
Jada

Telephone

+17048317077

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Littafin mai sarki Hausa group posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share