18/12/2020
BAYA GA TUKIN MOTA, KA KWARE A JAN ZUKATA MAULANA PROF..
Nakan saurara, na maimaita sauraro, amma gwargwadon yawan sauraro na, gwargwadon sabbin fahimta nake nakalta cikin karatuttukan sa wanda ban riska a littafi ba, hakika karantarwar sa tayi matukar tasiri sosai da sosai a rayuwata wacce bazan iya misaltawa ba.
Bana matawa, a Shekarar 2016 lokacin muna gab da kammala karatun mu na N.C.E a kwalejin ilmi ta garin mu, sai aka turamu koyon aikin koyarwa zuwa wata makaranta, hakika ajin da aka turani ajine da aciki akwai yara masu tarin kiriniya wadanda basujin magana, a ka'ida akan zane duk yaron da ya zamto mai kiriniya tare da bashi horo, amma wallahi da zarar yaro yayi min laifi babba, da nayi niyyar zane shi sai naji duk na kasa, idan ta kure sai dai nasa monitor ya zane shi shima sai naji duk ya sanyani a wani irin yanayi na zallar tausayi, tsabar yadda karantarwar sa akan jinkai ga halitta da kyautata mata ya ratsa zuciyata. ALHAMDULILLAH.
Inason mutumin da zai fada da baki, kuma ya aikata abinda ya fada a aikace, wanda gina Addini ne a gaban sa, ba gina kansa ba, wanda wayar da mutane fahimtar addini ne a gaban sa ba tallata kansa ba, wanda yake yi saboda ALLAH ba damuwar sa a yabe shi ko kuma a kushe shi ba, wannan dalilin yasa na bashi kujerar din-din-din a cikin zuciyata, kuma na aminta dashi 100%.
Idan kanason tozali da Ahli-Sunnah na hakika, wanda yake matukar kwatanta koyi da MANZON ALLAH (S.A.W) ta fuskar kyautatawa, kawaici, yafiya, da kuma hidimar bayin ALLAH, da koyi da sauran dabi'un sa a aikace, to kaje ka aboci zama da Prof. Ibrahim Maqari koda na wasu yan mintuna ne, wallahi anan zaka tabbatar da cewa Malaman kungiya da suke ikirarin Sunnah kashi 90% din su basu ma san cikekkiyar ma'anar sunnar ba, idan ka nakalci dabi'u da ayyukan su, na Sayar da Addini ta hanyar amfani da mabiya, da neman kudi da Addini, da kuma daura mutane akan fatawowi na saba lamba.
ALLAH YA TSAWAITA MANA RAYUWAR HAZIKIN DAN BAIWA, MUJADDADIN MU NA WANNAN KARNI.
Daga :Muhammad Usman Gashua.
ALHAMDULILLAH.