04/06/2015
MAZAN NE KO MATAN NE.?
1. Ina mamakin wai ko wanne namiji idan ya
tashi yin aure wai FARAR MACE yakeso mai kyau
malam kai FARI ne ko KYAWUN ne da kai.???
2. Idan da ace MATA zasu cire son kudi da abin
duniya suma s**e sai fari dogo mai hanci mai
kyau sukeso su aura, don Allah MAZA nawa ne
kenan zamu AURU 5% ko 10%
3. Sannan sai kaga namiji ya dage wai shi sai yar
mai KUDI zai aura tokai dan mai KUDI ne.???
4. Kema MACE ki dage waike sai mai kudi zaki
aura, to a lokacin da mahaifinki yayi auren farare
bugun Abuja nawa yake dasu.???
5. Sai kaga namiji ya dage waishi ba zaiyi aure
ba sai yayi KUDI, tambayata a nan shine kasan
lokacin da zakayi KUDIN,??? Kuma nawa ne zaka
mallaka a duniya.???
6. Haba yan MATA wai kema sai ki dage lallai sai
anyi miki LEFE akwati 12 wata ma sai dai 14, yan
MATA koma gida ki tambayi mahaifiyarki akwati
nawa ya kawo tsohonki ya kawo mata a lokacin
da zai aureta,??? Wata kila ma KWALLA ce 1 ko
2.
7. Yan MATA kun jefa SAMARI akan sai sunyi
kudi ta ko wanne hali sannan zaku auresu, wanda
ta hakan wasu sun koma 419, wasu sata kawai
don su auri FARAREN MATA masu kyau.
8. mu kuma MAZA mun jefa MATA a Bala'I na
BLEACHING, SHIGAR BANZA, NUNA TSARAICI,
BARA'A GA DOKAN ALLAH, kawai don su auri
namiji mai kudi mai kyau
9. SAMARI da yan MATA mu ajiye burukan dake
makare a cikin zucuyoyin mu, mu rufawa juna
asiri
10. MAZA da MATA mu farga wallahi ba haka
iyayen mu s**a rayu ba, kuma zanyi muku
gargadi mafi tsoratarwa dan duk wanda ya kuma
takurawa MATA ni dashi ne.