Hausanovels

Hausanovels Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hausanovels, Zaria Road Rigasa kaduna, Kaduna.

Ɗabi’a ce dake ƙara yawaita acikin al’umma, har matan aure ana amfani dasu ta duburaBincike ya nuna cewa maza suna fuska...
17/03/2026

Ɗabi’a ce dake ƙara yawaita acikin al’umma, har matan aure ana amfani dasu ta dubura

Bincike ya nuna cewa maza suna fuskantar wannan matsala fiye da mata da ratio na 28:1

Duk yadda kikeson mijinki, kar ki bari yayi amfani dake ta dubura, bazaki gane illar abun ba har sai tsufa yazo miki lokacin zaki fara zubarda bahaya a dubura, jikinki yana warin bahaya, yan uwa da dangi na gudunki

Duk yadda kake girmama mutum, ko kakeson mutum, to karka bari yayi amfani dakai ta dubura 📌

Iphone, mota, babur, aikin gwamnati, jarin kasuwanci, kujerar hajji, ɗaukar nauyinka, duk basu kai darajar lafiya ba 📌

Faɗakarwa: Dubura ba wurin jima’i ba ce, wani ɓangare ne na hanji (alimentary canal). Ku kiyaye lafiyarku, kada ku jefa kanku cikin hatsari

Alhassan Mai Lafia

11/03/2026

Jarin Tsoffin Jaruman Finafinan Hausa Da Ali Nuhu Ya Baiwa Kyautar Kuɗaɗe Masu Tsoka

Daga Yahaya S. Kaya Media

Shugaban Hukumar Finafunai ta Nijeriya kuma fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuhu, ya sake jawo hankalin jama’a bayan wani abin alkairi da ya yi wa ‘yan masana’antar Kannywood.

Rahotanni sun nuna cewa Ali Nuhu ya gwangwaje tsofaffin jarumai mata da maza da makudan kudade, domin tallafa musu da kuma nuna godiya ga irin gudunmawar da s**a bayar ga masana’antar a tsawon shekaru.

Baya ga haka, Ali Nuhu ya kuma raba babura ga wasu daga cikin ma’aikatan masana’antar, domin su samu saukin zirga-zirga wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

Wannan abin alkhairi nasa ya karade kafafen sada zumunta, inda mutane da dama ke yabawa wannan mataki nasa na tausayi da kuma tallafawa wadanda s**a sadaukar da rayuwarsu wajen ci gaban masana’antar Kannywood.

Jerin Wasu Daga Cikin Wadanda S**a Rabauta

1. Isa Ja
2. Mama Hajjo
3. Danmagori
4. Baba Sogiji
5. Haruna Aliyu
6. Kabiru Nakwango
7. Ahmad Alkanawy
8. Mal Khalid
9. Tanimu Akawu
10. Alh Yusuf Khalid
11. Haj Balaraba Ramat
12. Haj Zulai
13. Bashir Bala Ciroki
14. Albalash Jos
15. Haj Hadiza Garba
16. Auwal Ishaq
17. Hashimu N Dikko
18. Auwal Marshal
19. Adamu Kwabon Masoyi
20. Bala Anas Babinlata
21. Hamza Dogo
22. Ali Worthme
23. Lawal D Funtua
24. Muntari Bandaru
25. Baba Karami
26. Bawa Mai Kanwa
27. Fati Mohd
28. Abida Mohd
29. Maijidda Abdulkadir
30. Maijidda Ibrahim
31. Halisa Mohd
32. Halima Adam Yahaya
33. Hafsat Iliyasu
34. Fati Sulaiman
35. Hafsat Sulaiman
36. Fati Baffa
37. Fati Karishma
38. Farida Jalal
39. Wasila Ismail
40. Hindatu Bashir
41. Ummi Nuhu
42. Hafsat Shehu

Me za ku ce game da wannan abin alkairi da Ali Nuhu ya yi?

Tsautsayi ko son banza?Muna cikin motar haya da abokina sai wani da muke zaune a seat guda ya fiddo iPhone 14 pro max, y...
09/03/2026

Tsautsayi ko son banza?

Muna cikin motar haya da abokina sai wani da muke zaune a seat guda ya fiddo iPhone 14 pro max, ya ce ma abokina mamansa ce ba ta da lafiya Kuma suna buqace da kudi shi ya sa ya ke son ko Dubu 75 ne don su biya kudin da za a Yi ma ta tiyata.

Ko da Aboki na ya ji an ce dubu 70 sai ya kar6i wayar ya na duba ta don ya tabbatar ko jabu ce. Amma abun mamaki sai mu ka ga komi na ta lafiya Lau ne, ga Kuma hoton gayen a wallpaper. Ko da na ga haka sai na ce ma abokina "anya wannan wayar ba ta sata ba ce?". Sai ya ce min ai ko ta sata ce in ya saye ta zai je a yi Mata flashing ne, sannan ya sake mata kes sai ya yi saurin sayar da ita.

Shapshap s**a yi ciniki abokina ya nemi ragi aka sayar Masa da ita dubu hamsin. Take abokina ya Yi ma gayen tiransifa, Ni dai Ina riqe da waya a tsorace ina Tunanin ba abin da zai sa mutum ya sayar da iPhone dubu 50 in har ta sa ce.

Muka sauka daga bus din muna daga ma abokin cinikin mu hannu har s**a tafi.

Muka zauna qarqashin wata bishiya abokina na qara dudduba wayar, Yana cikin dubawa sai wayar ta dauke, sai muka yi tunanin qila chaji ne, na qar6i wayar na dan duba kwatsam Kuma wayar sai ta kunnu da kanta, sai mu ka ga screen din ya nuna "searching... Sai abokina ya yi murmushi ya ce "yawwa ta kunnu😁. Da ma wayar tana hannuna, ba a yi minti 2 ba sai rubutun ya 6ace wani ya fito. Tracking.. Tracking... Tracking kawai ta ke nunawa🙄 Ina ganin haka sai na miqa Masa wayarsa, Amma sai ya Yi k**ar bai ga Ina miqo Masa ba. Sai na ce Masa "amshi wayarka!". Wai sai ya ce min "ba hannunka take ba, ka riqe ta har ta gama tracking din ta Mana"🙄. Na ce Masa "tayi tracking din mi🙄? Malam dalla riqe wayarka". Sai ya ce "haba bar ta wajenka har ta gama tracking din network dinta, ba Ina Nan ba,ko guduwa zan Yi ne?🙄". Na ce "Kai Malam amshi wayarka ta Yi tracking din network din a hannunka, na tura Masa ita cikin aljihu na Yi gaba na bar shi baya.

Ha'a! Kawai ba sai na ga abokina ya wuce ni a sukwane ba🤔 ai Nima sai na bishi a dubu, da na taddo shi muna gudu na ce Masa gudun me mu ke? Sai ya ce ai wayar ce ta rubuta LOCATION FOUND 😯😮watau ko su waye sun Gane haqiqanin wajen da wayar ta ke! Kam ai sai na qara giya, Ina gudu na juyo sai na ga abokina na bina Shima a dubu Kuma ga wayar a hannun shi, ai sai na qara wuta, da dai na ga ya liqe man bumpa to bumpa sai na yanke na fada daji da gudu. Na Yi gudu ya Kai na minti 5 ina tunanin na 6ace Masa kawai sai na hango shi ya shawo kwana da gudu ya nufo inda Nike da Wayar a hannunsa😮 Kam bala'in nan! Gudu bai qare ba kenan. Ai sai muka qara retawa a guje
🏃🏃
Ko yanxu haka Ina gudu Ina rubuta wannan post din, Kuma shi Dan shegiyar ya qi daina bi na, ga shi Kuma ya kasa yadda wayar sai ka ce uwarsa ce ta Zama iPhone din, ya wani maqalqale ta, ko da ya ke ban ga laihinsa ba, Dubu Hansin ai ba Wasa ba ce.

©️ Yusuf Rabiu Jibia

28/02/2026

Celebrating my 7th year on Facebook. Thank you for your continuing support. I could never have made it without you. 🙏🤗🎉

Kwanakin baya Oga Abba Sa'adu Hadejia yayi Bayani akan Kiwon Agwagwa: Daga  #70,000 amma na maayar dashi ₦82,000 zuwa Mi...
28/02/2026

Kwanakin baya Oga Abba Sa'adu Hadejia yayi Bayani akan Kiwon Agwagwa: Daga #70,000 amma na maayar dashi ₦82,000 zuwa Miliyan Uku a Shekara wasu suna mamaki bari muyi wani lissafi

Mutane da yawa sun bar kiwon agwagwa a baya saboda suna ganin agwagwa tana da kazanta. Amma gaskiya ita kazantar tana dogara ne da tsarin kiwo.
Idan ka tanadi:
Wuri mai tsafta
Ruwan sha mai kyau
Abinci a kan lokaci
Killace uwa da ‘ya’yanta

To agwagwa ba ta da wata matsala mai yawa.

Mu Yi Lissafi a Hankali

1️⃣ Ka Fara da:
Agwagwa mata 10 (masu yin kwai)
Toro (namiji) 1 ko 2

Farashin:
Mace mai yin kwai ≈ ₦7000
10 × 7000 =70,000
Toro ≈ ₦12,000

Jimilla jarin farko ≈ ₦82000

2️⃣ Yawan Kwai

Agwagwa ɗaya tana iya:
Yin kwai 25–30 a kowane kwanci
Yin kwanci sau 3 a shekara

Amma mu rage lissafi don mu dauki tsaka-tsaki.

Mu ce:
Agwagwa ɗaya ta fitar da ‘ya’ya 50 kacal a shekara

To:
50 × 10 agwagwa = ‘ya’ya 500 a shekara

3️⃣ Yawan Kuɗi

Idan ka sayar da ɗan agwagwa bayan ya girma a ₦6,000:

500 × 6,000 = ₦3,000,000

Wannan shine inda miliyan uku ke fitowa.
Sannnan yanzu haka mutane suna bukatar day old na agwagwa
Kuma ka tuna:
Wasu daga cikin waɗannan 500 idan sun kai wata 5–6, su ma za su fara yin kwai.
Anan ne ribar ke fara ninkawa.

Abubuwan Lura
Kada ka yawaita maza (Toro).
Toro 1 zuwa mata 8–10 ya isa.
Idan s**a yi yawa, fada zai iya kaiwa ga mutuwa (k**ar yadda ka gani).
Idan kana son rayuwar ‘ya’ya ta ƙaru:
Killace uwa da zarar ta fara kwanci
Kada ka bar su yawo a waje ba kulawa
Idan ka sayi injin kyankyasa (incubator), yawan fitar ‘ya’ya zai fi yawa, ribar ma zata karu.

Itama haka Kwakwa

Idan agwagwa tana iya yin:
Har kwai 200–250 a shekara

Idan muka ɗauki 200 kawai:
200 × 10 = 2,000 kwai

Ko da kaso 70% ne s**a kyankyasa:
= 1,400 ‘ya’ya

Ko da ka sayar da su a ₦5,000:
1,400 × 5,000 = ₦7,000,000

Wannan ya nuna maka cewa:
Kiwon agwagwa na iya zama kasuwanci mai ƙarfi idan an tsara shi yadda ya k**ata.

Abu na karshe

Kiwon agwagwa:
Ba ya da yawan rashin lafiya sosai
Ba ya cin abinci k**ar kaji sosai
Yana da saurin ninkawa

Babban sirri shine:
Tsari + Haƙuri + Kulawa

Allah Yasa Mudace





B Abdoulraxack M Sani

 .Cikakken bayani game da tsarin MTN-CUG wani tsari ne da MTN s**a zo da shi domin sauƙaƙawa masu yin doguwar waya misal...
24/02/2026

.

Cikakken bayani game da tsarin MTN-CUG wani tsari ne da MTN s**a zo da shi domin sauƙaƙawa masu yin doguwar waya misali MASOYA, YAN KASUWA, YAN UWA da sauransu, shi tsarin mutum zai bayar da numbers ɗin abokan hulɗarsa ne a ɗorasu a kai domin sauƙaƙa yawan kashe kuɗin kati (a taƙaice tsari ne wanda idan aka ɗora SIM ɗinka akai to subscription na katin N400 za ka rinƙa yi suna baka damar yin waya har ta 7HOURS da kuma 50 FREE MESSAGES, Amma iya tsakaninka da wanda ka bayar aka ɗoraku k**ar kai da Budurwarka, ku biyun SUBSCRIPTION ɗin katin N800 kenan)

MISALI: Ace kullum domin waya da Budurwarka kana kashe katin N500 ka ga a wata guda zai k**a N15k ko to idan aka ɗora numberka da ta Budurwartaka akan tsarin MTN-CUG katin N800 zai maye gurbin wancan N15k ɗin da za ka kashe, sbd haka za ka iya haɗa Numbers ɗin Ahakalinka gaɓadaya a ɗoraku akan tsarin ko Abokan kasuwarka ko dai abokan mu'amalarka, ko tsakaninka da iyayenka.

ABUBUWAN da ake buƙata domin ɗorawa SIM wannan tsarin kawai Numbers ɗin da mutum yake so a ɗora masa zai mayar sai kuɗin Aikin, Farashi k**ar yadda ku ka gani ban faɗa ba a FACEBOOK sbd tsaro sbd kuma sirrin kune wannan,

Tunda yanzun kun san tsarin kuma kun ga farashi za ku iya fara tallatawa kuna amsar NUMBERS da kudin Aikin kuna tarawa a hannunku kun ga ranar SUBMITT tana zuwa ALREADY da kaya a hannunku kawai turowa za ku yi (Ga sabbi MEMBERS ta PRIVATE ake turowa zan bada account number da za ka saka kudi na adadi Numbers ɗin da za ka yi SUBMITT kai haɗa da receipt of payment da kuma Numbers ɗin ka turo).

Duk mai tambaya a bayan wannan rubutun ya mun a private please.

Address

Zaria Road Rigasa Kaduna
Kaduna
800001

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausanovels posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hausanovels:

Share