26/09/2025
KISHI
A gaskiya mata sai munyi hakuri akan wannan topic din don iya gaskiya ta Zan fada maku.
kowacce mace damuwarta ace ita kadai take jiyuwa acikin zuciyar mijinta ya zamto bai da wani tunani na wata mace sai nata , kuma zan fadi miki gaskiya abinda bazai taba yiwuwa har abada .
👉ki sanya a ranki cewa mijinki zae iya son wata mace fiye da yanda yake sonki
👉ki sabarwa ranki cewa bayanki akwae wata mace da zata saka mijinki nishadi
👉ki yarda wa ranki cewa mijinki zae iya sharing damuwarsa da wata daban Wanda bake ba
Dalilina kuwa shine :
👉su maza dakike gani Allah dakansa ya halatta masu auren wasu matan abayanki
👉ki sani koda ace kin samu kin tsallake anan duniya ba ayi miki kishiya ba kisani cewa zaki hadu dasu acan lahira kinga fa abokiyar zama kan wajibi ne
👉su maza dakike gani duk dadinki dasu dole acan kasar zuciyar su suna bukatar wata daban domin nature dinsu dey are polygamous in nature
👉muddin kikace zaki takurawa namiji akan mata kisani tsoron ki zai sa yaje yaci amanarki .
Amma matukar idan har kikace zaki daga hankalin ki akan namiji wlh zaki rasa ranki wataran saboda shikam namiji duk rantsuwa dazai miki kan mata kar kisaki ranki akai ke kadai ce,don haka karki haramta abin da Allah ya halatta ki duba duk irin soyayya da Annabi Muhammad sallalahu alayhi wasallam yayi da Nana Aisha Allah yakara mata yarda amma sai da akayi mata abokan zama kuma bawae itama babu kishi azuciyar ta bane akwae amma tsoron Allah dabin umarninsa yasa tayi biyayya tayarda muji tsoron Allah