05/11/2025
JIYA NAGA ABIN MAMAKI
wannan matar da kuke Gani jiya ta shigo kasuwar Dawanau dauke da speaker Mai karar gaske tana kira ga musulmi suzo su bi yesu Mai ceto😂
Duk da nasan ce constitution din Nigeria ya bawa kowa dama ya yada addinisa a ko'ina a fadin kasar Nan batare da an tsangwameshi ba, Amma a yanzu bazai yiwu musulmi ya dauki speaker ya shiga cikin Enugu ko Anambra Yana yawo cikin kasuwa yanawa'azi batare da ya samu matsala ba.
Amma nagodewa mutanen mu ta s**a Zuba mata Ido har ta gama wa'azinta batare kowa ya kulata ba, idan ma Wani shiryayyan Alma'ari ne to dai Allah ya kiyaye.
Daga Bilya Labaran