NDC Kwankwasiyya Update

NDC Kwankwasiyya Update Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from NDC Kwankwasiyya Update, Maiduguri.

Who do you vote for?
04/06/2026

Who do you vote for?

NDC Kwankwasiyya Update
02/06/2026

NDC Kwankwasiyya Update

Senator Aishatu BinaniGovernor FintiriGovernor Agbu KefasGovernor Inuwa YahayaSenator Danjuma GojeSheikh Isa Ali Pantami...
02/06/2026

Senator Aishatu Binani
Governor Fintiri
Governor Agbu Kefas
Governor Inuwa Yahaya
Senator Danjuma Goje
Sheikh Isa Ali Pantami
Ibrahim Hassan Dankwambo
Former Governor M. A. Abubakar
Governor Bala Kauran Bauchi
Senator Ningi
Former Governor Ibrahim Gaidam
Governor Mai Mala Buni
Senator Ahmad Lawan
Governor Zulum, and lastly,
Vice President Kashim Shettima.

Waɗannan fa duk basa tare da Atiku kuma ƴan yanki ɗaya ne ,amman ba wanda ya taɓa zaginsu akan basa tare da Atiku duk da kasancewarsu ƴan yanki guda ,sai Kwankwaso da ba ɗan yankinsu ba .Kuma ba wanda ya taɓa ce musu basa kishin Arewa .

Dan Allah dan Annabi wanne irin tsana kuka yi mana ne wai? Duk sanda bala'i ya afku a jahohinku Kano ce kan gaba wajen bada tallafin da ba kowa ke bayarwa ba ,amman ita ke shan zagi da s**a daga wajenku meyasa ?

Tunda suna na ya fito, ba yadda na iya dole sai na ce wani abu duk da dai ba zai yiwu a fadi komai ba. Mu uku ne mu ka z...
02/06/2026

Tunda suna na ya fito, ba yadda na iya dole sai na ce wani abu duk da dai ba zai yiwu a fadi komai ba.

Mu uku ne mu ka zauna mu ka rubuta Bill sakamakon abunda gwamnan jahar Imo na lokacin, Rochas Okorocha, ya shigo da shi na yiwa mutanen Arewa rijista da kuma basu ID card da za su rika yawo da shi. Bill din kwata-kwata ba shi da alaka da Peter Obi ko ma jaharsa ta Anambra.

Mun ce za mu kai Bill din majalisun dokokin jahohin Kano, Kaduna, Katsina da Jigawa. Mun fara kaiwa majalisar Kano. Washe gari sai mu ka dunguma mu ka tafi Kaduna. Mun je tare da Kamilu Hassan Hamza , Sunusilawan Fandubu da marigayi Saleeth Omar . Akwai kuma Amoke da ya ke a can Kadunan wanda shi ya tattaro ma na 'yan jarida.

'Yan jarida sun yi aikin su. Tun mu na hanyar dawowa mu ka ga labarin cewa shugaban kasa Jonathan ya kira taron gaggawa na majalisar tsaro kan abinda ya ke faruwa a Imo din kuma majalisar ta dakatar da tsarin a koma ina ne.

Mu na dai kan hanyar a ka kira mu a ka ce kwamishinan Sharia na jahar Kano, Maliki Kuliya Umar, ya na son ganin mu. Washe gari mun je wajensa. Da ya ke lokacin su Kwankwaso ba su jima da barin PDP ba don kafa APC. Kwamishinan Shariar ya ce su yanzu sun zama ma su saurin laifi a wurin gwamnatin taraiya. Mun yi abu ana cewa su ne su ka sa mu.

Bayan nan AIG Tambari Yabo ma ya kira mu. Haka ma ofishin DSS na Kano.

Wannan amana ce ta tarihi. Mu fadi abinda da mu a ka yi shi a yadda ya faru. Kuma kamar yadda na fada, ba don suna na ya fito a screenshot ba da ba zan ce komai ba, kamar yadda ban ce komai ba kan wasu abubuwan da da ni aka yi su amma ina gani ana malkwada su. Bahaushe ya ce in mafadin magana wawa ne, to majiyinta ba wawa ba ne. Don haka abinda ake malkwadawar in dai majiyin ba wawa ba ne zai gane.

Adadin ƙuri'un da Tunibu zai samu daga Arewacin Nigeria masu ƙuri'un sune adadin dabbobin da muke da su a Arewacin Niger...
02/06/2026

Adadin ƙuri'un da Tunibu zai samu daga Arewacin Nigeria masu ƙuri'un sune adadin dabbobin da muke da su a Arewacin Nigeria,

Adadin ƙuri'un da Atikuloser zai samu masu ƙuri'un sune adadin asararrun da muke da su a Arewacin Nigeria,

Adadin ƙuri'un da Mr. Peter Obi zai samu daga Arewa masu ƙuri'un sune adadin mutanen kirkin Arewa masu son zaman lfy da haɗin kan ƙasa da son cigaban ƙasa,

No More Tribalism, No More Bigotry, We'll Choose Wisely, Obi/Kwankwaso Is The Only Answer, kar ka zama dabba kar ka zama asararre Open Your Eyes 👀 Brother.

✍️
Isa Mohammad Abu Sadiq Al'Nigeria
Jagoran Arewa O/K Movement

Daga Wace Jaha a Nigeria Zaku Zabi OBI Kwankwaso
01/06/2026

Daga Wace Jaha a Nigeria Zaku Zabi OBI Kwankwaso

01/06/2026

Boom 💥 💥
Insha Allah Kafin 12 Na Rana
A Zaben Kano Central 2027
Gawuna Ya Kwarfe Malam

01/06/2026

Jam'iyar NDC ta tsayar da Engr. Sunusi Danbatta takarar sanatan kano ta Arewa wanda zai kara da Senator Barau jibrin.

Dan takarar Majalisar Jiha a Bebeji kuma abokin arziki, Hon. Hamisu Gwarmai ya kawo ziyarar dubiya da gaisuwar Sallah ga...
01/06/2026

Dan takarar Majalisar Jiha a Bebeji kuma abokin arziki, Hon. Hamisu Gwarmai ya kawo ziyarar dubiya da gaisuwar Sallah garinmu, inda ya ziyarci Jagoran Kwankwasiyya, Alh. Jibrin Dan Akko Tariwa tare da mahaifiyata da take jinya. Muna godiya!

Comr. Sule Yau Tariwa
NDC Kwankwasiyya Update

Address

Maiduguri
234

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when NDC Kwankwasiyya Update posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share