Bin Abdulwahab Masari

Bin Abdulwahab Masari T shirt �

22/12/2025
06/05/2025

Da aljannu zasu yadda a zauna ayi sulhu dasu ba karamin alkhairi za'a samu ba wajen jigilar alhazai a hajjin bana🤣

27/08/2022

SANA'A MAGANIN RAINI.

Arziki na Allah SWT ne. Amma duk wanda baya da Sana'a a cikin Al'umma, baya da mutunci a cikin al'umma. An gaya masa ko ba a gaya masa ba. Ka k**a Sana'a. Kar ka raina Sana'a Komai kankantarta. Ka bar sana'ar da zata iya rike ka kaje ka k**a wadda tafi ƙarfin ka. Dan wannan shima kuskure ne a rayuwa. Babu sana'ar da ba ayin arziki. Ko Bola kake sayarwa zaka iya Arziki in Allah SWT ya ƙaddara maka.

14/08/2022

Kada ka yaudari kanka da duniyar nan.
Ka tsaya kayi abinda zai amfane ka, ya amafani lahirarka.

06/03/2022

*ZA'A MANTA DAKAI A TARIHI*

Kullum ka dinga sawa a ranka cewa lallai fa wannan duniyar dole sai ka barta, zaka tafi kabar duk wani abu da ka same shi acikinta, kai samamme ne acikinta, to haka nan zaka tafi kabarta ka zamto tamkar wanda bai taɓa ɓulluwa ba acikinta

Kullum ɗan adam yakan manta da ramin ƙabarinsa, shi abinda ke gabansa kaɗai itace duniya, ya manta da cewa wataran ƙabari ne makomarsa

Za'a binne ka acikin ramin kabarinka duk yadda ka kai wajen matsayi, za'a manta dakai tamkar ba'a taba yinka ba a tarihi.

18/11/2021

Alqawari ne na Allah, duk Wanda yayi masa da'a a lokacin rayuwarsa, zai kula masa da bayansa a lokacin da ya bar duniya.

09/11/2021

TAUHEEDI SHI NE MABUDIN ALJANNAH.

Ibnul Qayyim Allah ya masa rahama yana cewa: "Hakika Allah ya sanyawa duk wani abu da ake nema mabuɗi da ake bude wannan abun da shi, Allah ya sanya mabudin sallah shi ne tsarki, mabudin aikin hajji kuma Ihrami, mabudin aikin alkhairi kuma shi ne gaskiya, mabudin aljannah kuma tauheedi, mabudin ilmi kuma shine kyautata tambaya tare da kyautata sauraro".

20/10/2021

*عادت الصفوف في الحرمين*

عاد الصفوف إلى الحرمين فابتهجت
كل النفوس بهذا الحدث وائتنقت

قال الإمام: أتموا الصف واعتدلوا
سدّوا الخلال فقام الناس واعتدلت

زال الوباء وفرّ الخوف وانتقلا
والقوم في فرح أرواحهم سعدت

قانون كورون ما أمسى له أثر
أدّوا المناسك والأطواف قد رجعت

هذا المقام وحتى الحجر يستلم
لبّيك لبّيك والأصوات قد رفعت

نكاد نقنط والإيمان يمنعنــا
والحمد للّٰه حتى الطير قد شكرت

لكلّ أجل كتاب قال خالقــنا
وللأمــور نهايـات إذا بدأت

ياربّ يُمنك نرجو أن تخلّدها
وأن تعافينا بلوى وإن نزلت

*✍️ أبو سمية*
*الشيخ بشير لول محمد زاريا*
*ليلة الاثنين*
*١٠ ربيع الأول، ١٤٤٣هــ*
*17 أكتوبر (تشرين أول) ٢٠٢١مــ*

19/10/2021

Ace Maulidi Addini,Mu Ace Ba Muyi. Yace Mu Dangale Wandomu,Mun Dangale.Wallahi Annabi S.A.W Ko Pant Yace Mu Fito Dashi,Da Pant Zamu Fito. Ace Murnar Haihuwarsa,Ya Bada Izinin Ayi Ace Ba Za Muyi Ba.To Babu Ne Kawai.Duk Littafin Daka Bude Babu.Ka Taba Ganin Wanda Yaje Ya Bude Littafi A Gaban Malami Zaiyi Karatu Akace Ga Fasalin Maulidi.

22/09/2021

WAYA.
-
"Waya ni'imah ce ga wasu mutanen, sannan taɓewa ce kuma ga wasu, yanayin aikinka da ita, shi ne zai ɗoraka a kan hanyar da zaka gane inda ta dosa dakai ko kuma inda ka dosa da ita"
-
"Ita wayarka kai ne zaka mayar da ita ta zamto ta alkhairi ko kuma akasin haka, ta hanyar aikata aiyukan alkhairi sai ta zamto wayar alkhairi mai kusanta ma'abocinta zuwa ga ɗa'ar Allah ta'ala. ta hanyar aikata sharri da ita kuma sai ta zamto wayar sharri mai kusanta ma'abocinta zuwa ga saɓon Allah ta'ala"
-
"Ka tambayi kanka, wayarka wacce hanya kake bi da ita wajen yin amfani da ita, shin hanyar da zata janyo maka yardar Allah ce, ko kuma hanyar da zata janyo maka fushin Allah ce?, kada ka manta, dukkanin wani abin da ka gudanar da ita, to tabbas abin tambaya ne gareka a ranar ƙiyamah, kuma da sannu zaka yi ma Allah bayanin yadda kayi amfani da ita"
-
Wasu babu abin da suke aikatawa da wayarsu face alkhairai, wasu kuma saidai tsabar sharri da yaɗa ɓarna a cikin jama'a, to idan ka tsaftace aikinka da ita, sai ka sami sauƙin hisabi game da ita, idan kuwa ka munana aikinka da ita, lallai hisabinka mai tsauri ne a rãnar ƙiyãmah"

Address

Kano

Telephone

+2348136404105

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bin Abdulwahab Masari posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share