Rayuwa da matar aminci dadi

Rayuwa da matar aminci dadi Wannan dandali kokarinsa yakawowa yan uwa mata da maza yadda zasu kasance cikin rayiwar aure mai am

28/06/2024

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Umar Lucio Abubakar, Aishatu Abubakar, Musa Abdu Captain, Abba S. Umar Kuki

15/02/2022

Assalamualaikum ya yan'uwa masu albarka maza da mata

05/12/2020
24/11/2020

Fa'idojin Auren Bazawara Ko Wacce Ta Girmeka A Shekaru:
ZAMANTAKEWAR AURE GA MA'AURATA:
Yana daga wasu fa'idoji da namiji zai samu in ya auri matar data girmeshi ko bazawara k**ar haka.
☛ Nafarko zai sami ladan sunna biyu wato sunnar aure da kuma ta koyi da Annabin rahama S.A.W ya auri wacce ta girmeshe, musamman ma in ya yi dan koyi da fiyayyen halitta S.A.W.
☛ Auren mace wacce tafika shekaru akwai yuyuwar samun ingantacciyar ra'yuwar aure matukar akwai soyayya, sak**akon cewa ita ta zauna dawasu mazan tasan rayuwar aure, tasan mai namiji yakeso tasan maye baya so tasami kwarancewar iya kwanciya da miji saboda haka da zarar ka auri irin wan nan kuma akwai so dakauna da tarbiyya to ba ma auren da yafi shi dadi, sak**akon tasami working expereence koda bata taba aure ba a baya shekarun data yi a rayuwarta zai sa taga abubuwa kala-kala a rayuwarta wadanda zasu zame mata darasi a zamantakewar aure nan gaba.
Haqiqa bazawara tafi budurwa sanin mak**ar aiki a zamantakewar aure musamman ma in ta sami saurayi wato wanda ta girma musamman ma ace akwai soyayya.
☛ Bazawara tana da hakurin zaman takewa fiye da budurwa dan ita tasan yau da kullum a aikace bawai abaka ba dan tagani akan wasu tagani akan kanta, sabanin budurwa ita kawai tagani akan wasune kawai.
☛ Bazawara ko wacce tafika shekaru tarigaya tasan halayen iyayan miji da yadda ake zama da su sabanin budurwa.
☛ Ayyukan gida da kula da gida gyaran daki ,iya girki da tsaftace shi, kula da yara da sauran su dukkan su zawarawa sunfi 'yan mata kwarewa a kai.
☛ Daddadan kalamai da kisisina da iya rarrashin miji, rashin katobara yayin zance, dadin shira dukka zawarawa sun kwarance fiye da 'yan mata.
☛ Rashin almabazzaranci da dukiyar maigida, k**ar bata abinci wasa da shi da sauransu.
Allah ka Azurtamu da mata na gari
Suma mata Allah ka Azurtasu da maza na gari
Albarkacin Annabi SAWW Amin.

11/11/2020

------MATA MATSALA-----
---------
Ayi maka laifi, a fika kuka.
Ka dauki jaka, a bika da bada hakuri.
Ka hakura ka dawo, a sake aikata wani laifin
da yafi na da.
Ka kalle su ace kana hararar su.
Kayi musu magana ace kana zaginsu.
Kayi fushi dasu ace baka da hakuri.
Ka kai su kara ace kayi girman banza.
Su kai ka kara, ace baka da gaskiya.
shiyasa nake tsoro akan mace anya kuwa
rayuwa ta yiwu haka??
Wai ina mazan da matan ne???
Ku sa baki inji mana!!!

08/11/2020

HIKAYAR SHEHU JAHA:
Agarin neman kiba an nemo Rama.
Wata rana shehujaha ya
kai saniyarsa kasuwa tunda
safe har yamma ba asamu
wanda ya taya ba,sai ga dan
anguwarsu shehu yace malam
mekake a kasuwa shehu yace na kawo saniyata ne tunda
safe ba a samu wanda ya ko
taya ba,dama mutumin dullali
ne yace kawo mugani ya fara
yawo a cukin tike ga saniya
BATALA mai cikin wata hudu nan da nan akayi cha kowa
yana so dama shehu tana so
sayarta fam goma ne sai aka
saya fam ashirin ya koma gida
yana mamaki bayan k**ar
kwana ki kadan anzo ne:an auren yar shehu sai matar sa ta
fada masa sai yace bakomai
insun zo ki fada musu akwae
maganar dani uban yarinya
zanyi matar tace toh a
zuciyarta tace allah sa shehu ba shirmensa zai yi bah masu
nema s**a zo dama mata ne
shehu ya fito yace da farko
dae yata budurwa ce mai jar
fata ka fararen hakora masu
daukar ido tana da dogon hanci har baka ga idonta farine
fat k**ar madara gashinta har
kasa yake ja,kirjin ta a cike
yake bekwanta ba,inko tana
tafiya ramkar dawisu kuma
tana dauke da ciki na WATA TARA 9 sai masu neman aure
s**ayi zuru waccar ta kalli
wan nan.
fadi magana daya 1
akan shehu jaha

04/11/2020

LABARIN WANI SARKI MAI HIKIMA.
A can wajajen kasashen gabas
anyi wani
Sarki da ya
dade akan gadon sarauta yana
mulki,da ya
fuskanci ya
tsufa sai ya yanke shawarar yin
murabus,
to amma inda Gizo ke sakar shi ne
wanda zai gaje
shi,maimakon
kawai ya zabi wani daga cikin
yayansa ko
a
mukarrabansa(yan majalisarsa)
sai ya sa aka tara
dukkan samarin garin a
fadarsa,ya ce
musu, "
shekaru
sun cin mini,lokaci ya yi a gare ni
da zan
koma gefe in nada Magaji,kuma a
cikinku na yanke
shawarar
zaba"matasan nan duk s**a rude
wannan
ya kalli
wannan,wancan ya dubi
wancan,zuciyar su cike da tunani, sarkin
ya ci gaba da
cewa"yanzu
zan
ba ku iri na shuka(seed) kowa ya
je ya
shuka shi,ya ba
shi ruwa ya kula da shi har
tsawon shekara guda,a
kawo min na ga irin abin da za ku
samu,duk wanda
na zabi tasa shi ne sabon sarki a
wannan
masarauta.
Aka raba wa matasa iri daban-
daban kowa ya tafi
gida
cike da burin zama sarki idan
shuka ta yi
kyau.
Cikin matasan nan da aka ba
akwai wani da
ake kira
Bilal,da zuwansa gida sai ya
shaida wa
Mahaifiyarsa dukkan yadda ta
wakana a
fadar Sarki,ta
yi murna
da jin wannan labari,nan take ta
taimaka masa
da
tukunya da kasa mai kyau wadda
za tai
saurin
shuka,s**a
shuka irin nan na sarki. Kowace
rana Bilal yakan ba
shuka ruwa,
sai ya yi
tsaye yana kallo ya ga yadda za ta
fito,haka ya yi
ta yi har
wajen sati uku,amma abin
mamaki ba abin da ya
fito
daga kasa,ya zuba ido har zuwa
na hudu na
biyar
kai
har na zuwa shida amma ko
tsagewa kasar ba ta yi
ba,ballatana shuka ta fito.
Zance ba haka yake ba a cikin
gari,domin
matasa
sai
murna suke shukarsu sai girma
take tana yin
kyau,hakan ba karamin tayar da
hankalinsa ya yi ba,sannan ga shi
duk inda
ya je maganar ke
nan,sai ya
yi shiru kurum,bai sanar da kowa
abin da ke faruwa
ba.
A kwana a tashi har wata shida
s**a
shude,matasa
a
gari na cike da farin ciki,shi ko
Bilal na cikin
damuwa,yana ta zuba ruwa ba
shuka,kullum
zuluminsa ya zai fuskanci sarki da
tukunya
ba komai.
Duk nisan wuri za'aje da tafiya saidai a dade ba'aje ba shekara
kwana,in ji yan magana,ranar da
Sarki ya alkawarta ta
cika,gari ya
zama tamkar ranar Sallah,ko'ina
matasa za
ka gani
dauke da tukunyar bishiya iri
daban-daban
sun yi kyau
ga tsayi,sun wa fadar Sarki
tsinke.Amma
al'amarin Bilal
kuwa a wannan rana ya tashi ne
cikin
fargaba har
sai da Mahaifiyarsa ta kwantar
masa da
hankali ta ce "ka je
da abin da ka samu ya fi kin zuwa
kana da
gaskiya,kuma kokarin ka ke nan"
Da shigarsa,sai fada ta kaure da
dariya da
sowa,ana nuna shi da tukunyarsa
ba komai,ya samu
gefe
daga
baya can kurya ya rakabe tare da
sunkuyar da kai
kasa,gabansa na dakan uku-uku.
Can jima wa sai
Sarki ya shgo fada,kowa
ya duka
ya
kai gaisuwa sannan akai shiru
ana
sauraransa,zuci
yoyi cike da fata da burin dacewa
a samu
sarauta,haka
abin
yake ga jama'ar gari wadanda
s**ai dako
ko Allah
zai sa nasu ya fito cikin nasara.
Sarki ya yi
murmushi gami da tashi yana
tafiya
cikin
kasaita da ganin shuke-shuke iri
daban-
daban,"Yau ce ranar da na
alkawarta muku cewa
daya
daga
cikinku
zai zama sabon Sarki a
masarautar nan
kuma na yaba
da abin da idanuna suke gane
min,a saboda da
haka...katsaham ! sai ya hango
tukunya ba komai a
ciki
ga mutum kuma a gefe na boye wa,nan da
nan ya yi
umarni
da a
zo da ita da mai ita,Bilal ya ji wata
rashin lafiya ta
gaba
daya ta k**a shi,cikinsa sai kululu
yake,ya
ji
kafafuwansa sun kasa daukarsa
"shi ke
nan na kashe irina za a kashe ni"
ya fada a
zuciyarsa.bai
gama
tunanin ba ya ji an yi sama da shi sai
gaban
Sarki, ai
tuni sai fada ta rude da dariya da
kyakyatawa
da sowa,wasu
har da faduwa dan mugunta,
Sarki ya daga
hannu
nan
take kowa ya yi shiru,waje ya yi
tsit, "ya
sunanka?" Sarki ya tambaya.
"Suna na Bilal" ya fada
jikisa na rawa.
Sarki ya dube shi sannan ya dubi
taron
jama'a cikin
murya mai karfin sauti da izza ya
ce
" Ku yi gaisuwa ga sabon Sarkinku
mai
suna Bilal". habawa! ai sai wuri ya
rude da gunguni na
mamaki,idanu s**a zazzago baki
a bude
cike da
tambayoyi,ya mutumin da ya kasa
shuka
iri na tsawon
shekara zai zama Sarkinsu?. Bilal
ya d**o kai a firgice,
shin abin da
kunnuwansa
s**a ji gaske ne ko Almara ko
mafarki?
Sarki ya share su ya ci gaba da
maganarsa
kawai,
"Shekarar da ta wuce na ba ku iri
daban- daban a
shuka
a kawo min yau" ya dan nisa can
ya ci
gaba. "To amma ba ku sani ba
DAFAFFEN IRI
na ba
ku (wanda
bazai shuku ba) da kuka ga ya ki
fitowa sai
kuka canza
da wani daban, Bilal ne kadai MAI
GASKIYA
da
bai canza
ba ya kawo min tukunya ba
komai, dan
haka kowa
ya yi gaisuwa ga sabon Sarki" ku
kwashe
wadannan
ciyayin ku ban wuri" Allah kasa
mucika da imani.

28/10/2020

WATSI DA LAMARIN AURE
Duk lokacin da ya zama al'umma tayi watsi da maganar aure ba a damu dashi ba, ba a bashi muhimmanci ba toh shine tushen farko na lalacewar wannan al'umma. Domin aure shi yake samar da gida me kyau, kuma yake samar da al'umma nagari mai tarbiyyah, duk lokacin da muka yi watsi da aure to tamkar mun yi watsi da tarbiyyan wannan al'umman ne.
ILLOLIN YIN WATSI DA AURE.
Illolin rashin yin aure suna da yawa, kadan daga ciki sune:
1. Yawaitan 6arna a bayan kasa.
2. Shegu ('ya'yan zina) zasu yawaita.
3. Tausayi zaiyi karanci a cikin al'umma.
4. Koyi ne da kiristanci (Ruhbaniyanci).
5. Ragye yawan mabiyan Manzon Allah (SAW).
6. Yana raba al'umma da Manzon Allah (SAW).
Anas bn malik (RA) ya ce: Wasu samari uku cikin sahabban Manzon Allah (SAW) su ka tafi wajen matan sa suna tambayan su game da ibadan sa, bayan sun basu labari sai su ka raina na su s**a ce: "Ina mu da Annabin Allah shi da aka gafarta masa zunubin da yayi da ma wanda baiyi ba!" S**a fadi bubuwa da dama daga cikin su wani yace shi ko ba zayyi aure ba. Da Manzon Allah (SAW) yazo aka bashi labari, Sai ya hau munbari yayi huduba ya ce: "Me ya samu mutane ne wallahi nafi ku tsoron Allah da kiyaye dokokinsa, amma ina azumi kuma ina sha, Ina sallah kuma ina barci, sannan ina auren mata, duk wanda ya kyamaci sunna ta bashi tare dani". [Bukhari da Muslim].
Ashe ba taqwa bane ba, ba tsoron Allah bane, ba tsantseni bane mutum yace ba zaiyi aure ba.Tunda Manzon Allah yayi aure kuma yayi umurni akan yin aure.
Sannan aure yana kawo nutsuwa ne ga mutum, domin idan aka ga mutum yana wasu abubuwa da basu dace ba sai ace ayi masa aure zai nutsu, kuma da ikon Allah idan aka yi masa sai ka ga ya daina ya nutsu k**ar ba shi ba.
Allah Madaukakin Sarki Yace:
ﻭَﻣِﻦْ ﺁﻳَﺎﺗِﻪِ ﺃَﻥْ ﺧَﻠَﻖَ ﻟَﻜُﻢْ ﻣِﻦْ ﺃَﻧْﻔُﺴِﻜُﻢْ ﺃَﺯْﻭَﺍﺟًﺎ ﻟِﺘَﺴْﻜُﻨُﻮﺍ ﺇِﻟَﻴْﻬَﺎ ﻭَﺟَﻌَﻞَ ﺑَﻴْﻨَﻜُﻢْ ﻣَﻮَﺩَّﺓً ﻭَﺭَﺣْﻤَﺔً ۚ ﺇِﻥَّ ﻓِﻲ ﺫَٰﻟِﻚَ ﻟَﺂﻳَﺎﺕٍ ﻟِﻘَﻮْﻡٍ ﻳَﺘَﻔَﻜَّﺮُﻭﻥَ .
"Kuma akwai daga cikin ayoyinsa. Ya halitta muku matan aure daga kanku, domin ku nutsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya soyayya da rahama a tsakanin ku. Lalle a wancan akwai ayoyi ga masu yin tunani." [Surah Ar-Rum vrs 21].
Sannan ko da mutum ne aka ga ya manyanta gashi shekarun sa sun yi nisa, sai ku ji ance wannan mutumin yana da aure kuwa? Sai ace bayyi aure ba, to sai ku ga mutane sun koma suna yin masa wani irin kallo, anya kuwa baya neman mata, ko ace anya lafiyar sa kalau kuwa, sai ku ga darajarsa ya ragu a idon mutane.
Kuma yawanci arziki yana samun yawancin masu kudi ne bayan sun yi aure, samari da muke gani suna da kudi tun kafin aure basu da yawa, amma mutum na aure sai Allah ya bashi arziki kuma ya buda masa hanyar neman halalinsa. Don haka aure baya kawo talauci k**ar yanda wasu suke fadi. Cewa sai sun kai wasu shekaru masu nisa sun tara kudi sannan zasu yi aure, amma kafin nan idan dai ba mai tsoron Allah bane sai kaga ya 6ata ya'yan mutane dayawa kafin yayi aure.
Aure shine yake kawo ma mutum cikakken nutsuwa da kwanciyar hankali. Don haka aure nutsuwa yake kawowa, aure arziki yake qarowa, yana karewa mutum mutuncin sa, sannan kuma kariyane ga mutum, domin idan mutum yayi aure babu ruwan shi da neman matan banza.
Allah ya kare mu yasa mu dace. Masu son su yi aure kuma basu da halin yi ina rokon ya basu daman yi. Wainda suke dasu kuma ina rokon Allah ya zaunar dasu lafiya ya basu kuma ikon hakuri da juna.
Naku muhd Dalhat

06/10/2020

TRUE LIFE STORY...
Cikin satin nan wani babban mutum a social media yayi min magana ta inbox yana buqatar maganin ciwon sanyi, a cewarsa ya kai tsawon shekaru biyar yana bibiyar rubuce rubucena har sai da ya ji ya aminta da ni sannan ne yayi min magana...
A qa'idata idan mutum ya nemi maganin wani ciwo daga gareni to dole sai nayi masa wasu 'yan tambayoyi domin na gane irin maganin da ya dace da shi...
Shine sai ya fara bani labarin k**ar haka:-
Yace shekarunsa ashirin da wani abu da aure, amma yace bai tab'a sanin dadin aure ba kasancewar matarsa bata bashi irin kulawar da ta dace, uwa uba kuma bata da sha'awa ko kadan, idan zai shekara dubu bai kirata shimfidarsa ba, to babu abin da ya dameta, sai tayi kwanciyarta a dakinta, idan yayi ta jiranta ya gaji sai ya hakura yayi baccinsa...
Yace a haka s**a kasance tsawon wadannan shekarun sama da ashirin da s**a yi tare, yace ana cikin wannan halin ne kullum yana tunanin mafita, kwatsam sai Allah ya hadashi da wata yarinya a facebook, ta nace masa, kuma sai ta dinga damunsa da tana so su hadu dan huld'ar kasuwanci, tun yana zukewa har dai ya aminta s**a had'u....
A ranar farko da s**a had'u a ranar yarinyar nan ta yaudareshi har sai da ya kusanceta, yace kuma sai a wannan ranar ne ya san dadin jima'i tare da nuna masa sabon salo salo irin na kwanciya wanda matarsa bata tab'a yi masa irinsa ba...
Yace wallahi bai taba kusantar wata mata ba a duniya sai matarsa kawai, sai kuma yau da wannan yarinyar ta ribaceshi, yace kuma tayi nasara ne saboda a wannan lokacin yafi wata tara basu sadu da matarsa ba saboda shima ya fusata ya fita sabgarta...
Tun daga ranar nan yace shikenan sai s**a hade shi da yarinyar nan, idan yana buqatarta ko ita tana buqatarsa sai suyi waya su had'u abinsu, kuma bata buqatar ko sisin kwabonshi...
To a cewarsa a jikin yarinyar nan ya dauki wannan ciwon na sanyi, yace a halin yanzu basu tare saboda ya fahimci tana mugun bin maza, yana ta koqarin ganin ya samu damar qara aure duk da cewa bai da niyar zama da mata biyu, to amma zai qara ne domin gudun kada ya qara fadawa ga halaka irin wacce yayi a baya...
A qarshe yace in buga labarin a facebook ko zai zama izna ga matan aure masu dabi'a irin na matarsa, wadanda saboda rashin iya kula da mazajensu yake sa wasu mazan neman mata a waje ko kuma su qara aure ba dan suna so ba...
Da fatan wannan DARASI zai zama izna a garemu, Allah kuma ya karemu daga fadawa irin wannan tarkon...

Na kwafo daga dan dalin ingaranka freedom redio. mudassir shi yaturo wannan labari

Address

Kano

Telephone

+2349063708500

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Rayuwa da matar aminci dadi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share