21/09/2025
YADDA AKEYIN SALLAH DARE
Dole ne mutum ya tsarkake niyyan sa, sannan sallah dare anfi so ayishi ne a farkon dare, ko ƙarshen dare, ba tsakiyan dare ba, kokuma mutum ya cinye daren gaba ɗaya, ma'ana daga ɗayan dare har 4:30am na dare, shine ka cinye daren gaba ɗaya!
1) Akwai buƙatan ka tsarkake zuciyarka da kuma kaya na musamman domin wannan sallah daren, idan kuma baka da kayan sallah dare, to kayan da zaka yi sallah dare dashi ka wanke shi idan da hali har turare kayi masa kafin lokacin sallah yayi.
2) Akwai buƙatan ka watsa ruwa (wanka). Kayi wanka a bisa sunnah, ma'ana babu samulu ko soso, sannan kuma lokacin da kake wankan kayita tuna kanayin wannan wankanne saboda kusantar ubangijinka mai tsarki da son tsabta!
3) Akwai buƙatan Alwala da nitsuwa da maida hankali yadda yadace, saboda Manzon Allah (SAW) yace duk wanda yakeson nitsuwa cikin sallar sa to yayi Alwala da nitsuwa da maida hankali, tabbas sallah zata samu nitsuwa da maida hankali. Ma'ana idan kana farillah ka gane farillah kakeyi, idan kana sunnah ma kagane sunnah kakeyi, haka mustahabbi.
4) Kada ka takura kanka da tsawaita Karatun surah bayan Suratul fatiha, hakan zaisa shedan yayita wasa da Kwakwalwar ka yayita tunama Abinda bashi ne ba, Amma surorin kasa-kasa ma ya wadatar, hakanne zaisa kayita samu kushu'i cikin Sallah ka, Kuma kada kayita ta tuna komai sai Lahira da sallah da kakeyi, Kuma kayita karatu a nitse Aya bayan Aya gently, In shaa Allah Kai kanka zakaji kamar Allah ya karba Anyi Maka register a Aljannah kokuma bukatar ka ya biya.
5)Akwai buƙatan idan kazo ka ƙabbarta ka fara tuna sheɗan zaizo ya ɓata maka sallah, saboda babu inda sheɗan yafi ziyarar zukatan bayan Allah kamar lokacin da yaga zasuyi sallah kokuma suna sallah, saboda yasan sallah itace babban ibada kuma mafi Alkhairi ga rayuwar ɗan Adam. Kaikuma kayi sallar ka cikin tuna Allah da lahira (Ƙiyama).
6) Zaka iya Addu'a cikin sujudan ka, kuma kada ka takura kanka da raka'oi masu yawa, kayi abinda zaka iya, idan kuma zaka ɗa