07/07/2025
TELA DANKALI: SHA KUSHE, ANA AMFANARKA, ANA KUSHE KA!!!
Tela, ka tsaya ka saurara ka ji inda darajarka take.
Ka taɓa ganin dankali?
Yana ginuwa a cikin ƙasa ne, a cikin laka, cikin duhu.
Amma idan lokacin amfaninsa ya zo, komai yana tsayawa ana tona ƙasa domin a samo shi. Har ana ji masa rauni, ana wanke shi da ruwa mai zafi.
Ana yanka shi ba tausayawa, ana soya shi a cikin mai mai zafi.
Ana ƙona jikinsa domin a more ɗanɗanonsa.
Amma duk da haka...
Ba a daina kushe shi duk da baƙar azabar da ake masa.
lokacin da yunwa ta cimma mutum ne kawai baya zaginsa gami da kusheshi.
Domin dankali yana da daraja, ko da kuwa ya fito daga laka ne kuma komai munin sa.
Kai ma tela, haka kake!
Ana yawan kushe ka, amma kai ne ake mafarki da kai lokacin bukata.
Ana raina sana’arka, amma kai ke ɗora ado a jikin masu raini.
Ana ce maka "ai aikin dinki ai kawai ɗinki ne", amma ba wanda zai yi alfahari a bainar jama'a sai ka yi masa ado.
Tela, ka sani:
Kai ba mai dinki bane kawai.
Kai ne injin sauya rayuwa.
Kai ne ke ɗora daraja a jikin rigar ‘yan mata.
Kai ne ke sauya tunani daga talaka zuwa mai kuɗi.
Kai ne ke sanya murmushi a fuskokin amarya da ango.
Kai ne ke kawata kasuwa da sabuwar salo da salama.
Amma duk da haka, ana maida kai tamkar ba ka da amfani.
Ana amfani da kai, amma ana ƙin yaba maka.
Ana bukatar ka, amma ana ƙin girmama ka.
To amma me ka zaɓa?
Za ka daina?
Za ka yi shiru?
Za ka bar sana’ar da kake?
Ko za ka tashi ka nuna cewa TELA BA ABIN KUSHE BANE?
Tela, ka tashi. Ka gyara dinkin ka. Ka haɗa salonka. Ka ƙarfafa kanka.
Wanda yake kushe ka, zai dawo ya neme ka.
Wanda ya raina ka, zai nemi selfie da rigar da ka ɗinka masa.
Wanda ya kira ka “maras wayo”, zai so ya koyi sana'ar ka.
Ka dage. Ka koyi kasuwanci. Ka ƙara salo. Ka cika zuciyarka da IZZAH.
Tela, kai babban mutum ne. Ka daina ƙanƙantar da kanka.
Ka na shan kushe, amma har yanzu ba ka sha kasa ba.
KA DAURE!
KA YUNKURA!!
KA MIƘE!!!
KA TSAYA!!!
Kayi tsayuwar d