Ustaz Vs Ustaziya Matchmaking "Halal Marriage for Ahlussunnah only"

  • Home
  • Nigeria
  • Kano
  • Ustaz Vs Ustaziya Matchmaking "Halal Marriage for Ahlussunnah only"

Ustaz Vs Ustaziya Matchmaking "Halal Marriage for Ahlussunnah only" Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ustaz Vs Ustaziya Matchmaking "Halal Marriage for Ahlussunnah only", Women's clothes shop, Kano.

Ustaz Vs Ustaziya Matchmaking (Ahlussunnah Marriage):Wannan shafi an ƙirƙire shi ne domin haɗa ma’aurata ta hanyar halal bisa ka’idojin Ahlussunnah kawai.Matsayinsa shi ne samar da wata hanya Mai sauki wajan hada Auren Ahlussunnah kadai don Gina Iyali

Shagwaɓa ustaza ta iya Sai kace ƙarama ƴar yariyaA abokina ansha da kaiIn baka da (bebe) ustaziya Daga siffofin ustaziya...
31/01/2026

Shagwaɓa ustaza ta iya
Sai kace ƙarama ƴar yariya

A abokina ansha da kai
In baka da (bebe) ustaziya

Daga siffofin ustaziya
Bata gori ba ta fariya

In kaje zance a gidansu kam
Za ta shirya abinci da jar miya

Ga ta tsaf-tsaf tamkar gimbiya
Koko na kirata sarauniya

Za ta zauna gefe kai kuma
Kai ta satar kallon soyaya

Murmushin ta kamar hasken wata
Ga biyayya gun alarammiya

In ka bata kaɗan karɓa take
Tai ta murna tai maka godiya

In ko a fagen ƙauna a nan
Ga kulawa tai ta tarairaya

Duk a zancen nata gaba ɗaya
Kalmomin so ta ka antaya

Bayan aure nan za ka san
Ka yi dace za ka yi dariya

Wata ran haka ɗai za tai fushi
Wai fa ustaz sai ka rausaya 😀

Duk cikin so ne ya malami
Tashi tattaka mata ka jiya

Ni kam ai sai ustaziya
Bani son auren ƴar duniya

Mijin Ustaziyah 💙
Mijin Mar'atusswaliha 🤍
Mijin Mai Niqab ❤️
Maison Ustaziya yayi following

Bismillahir Rahmanir Rahim🕌 Waye Ustaz na Gaskiya?Ustaz shine mabiyin tafarkin sunnaUstaz ne Ahlussunnah shi ne wanda ya...
28/08/2025

Bismillahir Rahmanir Rahim
🕌 Waye Ustaz na Gaskiya?

Ustaz shine mabiyin tafarkin sunna
Ustaz ne Ahlussunnah shi ne wanda yake:

✅ Yana bin koyarwar Al-Qur’ani da Hadith sahihai ba tare da ƙara ko ƙarewa ba.
✅ Yana koyar da mutane da hikima, tausayi, da gaskiya.
✅ Yana amfani da iliminsa wajen gyara al’umma, ba ya yaudara ko neman duniya.
✅ Yana kiyaye kansa daga bidi’a, zalunci da duk abin da ya saba wa sunnah.
✅ Yana zama abin koyi cikin aiki, magana, da halayya.

👉 Ustaz na gaskiya ba kawai malami ba ne, amma jagora mai nuna hanya zuwa alheri da tsoron Allah.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ustaz Vs Ustaziya Matchmaking "Halal Marriage for Ahlussunnah only" posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share