15/04/2026
Wannan haka yake malan
Shehin malami kuma jigo a jam’iyyar ADC a jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa duk lokacin da wani ɗan siyasa ya shiga uku ko ya fuskanci matsin lamba a harkar siyasa, Kwankwasiyya yake komawa domin neman mafita.
Ya ce hakan na nuna irin ƙarfin da tafiyar Kwankwasiyya ke da shi a fagen siyasar jihar da ma ƙasa baki ɗaya.