30/12/2023
Ababen Da Ke Sa Cinyewar Gaban Gashi Da Yadda Za A Magance.
🥑Yin kana Nan kitso Kuma a matse Kai ko amatse gaban gashi Yana ba gashi wahala har ya Kan Kai ga cinyewar gaban gashi,wani lkcn ma Yana sa karyewar gashi,zubar gashi ba dalili.
🥑 Da wannan ne nike Baki shawara yake meson ganin gaban gashinta ya dawo da martabarshi ya bar cinyewa,gashinki ya bar zuba ba dalili.
🥑 Idan kin Tashi kitso kiyi kitsonki matsakaita Kuma Kar a matse kitson Kuma Banda daukan gaba wato all back don ya na taka muhimmiyar rawa wurin cinyewar gaban gashi ki,Kuma ya ka
sance yayi kwana goma zuwa sati biyu don yawan kwance kitso Yana sa zubewar gashi.
🥑 Barin gashinki a bushe wato da kin shafa Mai wurin kitso shike nan Sai Kuma Zaki sake wani,wannan ya bada gudumuwa wurin cinyewar gaban gashin ki da karyewar gashi, yin amfani da hair spray,hair lotion, hair butter,hair oil Yana Hana bushewar gashi, karyewar gashi ba dalili cinyewar gaban gashi don suna sa Mai ma gashi sinadaran da yake buka ta Kuma su Hana shi bushewa zai Zama Mai maiko ko da yaushe don Hana karyewar gashi da cinyewar gaban gashi.
🥑Ki Rika Yi ma gashin kan ki massaging wato matsa ko murza gashin na tsawon 5minutes akalla kullun don jini ya Rika yawo akan (scalp) din don taimaka ma kayan da ki kayi amfani dasu shiga ciki suyi aikin da ya dace.
🥑Wanke Kai, akai akai Dan rake maikon Kai da dattin Kai don gashin ya samu Daman cigaba da toho.