Likitan Yadi

Likitan Yadi Perfect at men clothing designs 👖👚

04/11/2025
04/11/2025
04/11/2025
22/04/2025
21/04/2025

Watch, follow, and discover more trending content.

17/04/2025

'YAR SA TA FARKO AKA KAWO LEFE AKWATI (12), BAYAN YA GAMA DUBAWA, YAYI RANTSUWA DA ALLAH BAZAI KARBA BA, SAI AN MAYAR DA SU!!!

GA DALILAN DA YA BAYAR:

1) 'Yata ba sayarda ita Zan yi ba. So nake tayi aure a matsayin ibada ba holewa ba.

2) Kuma 'yata tana da qanne 'yammata, shike nan sauran qannenta sai su sa rai suma sai an kawo musu akwati goma sha biyu ko sama da haka, kuma idan Allah bai horewa mijin ba, su raina shi. Suga ya gaza.

3) Suturar da ya zuba acikin lefen masu tsadar gaske, duk iyayensa da s**a kawo lefen babu wacce tasa mai tsadar su, me yasa ya kasa siyawa iyayensa su sa kafin ya siyawa 'yata, idan mai arziki ne shi ba makaryaci ba.

4) Da ace rabin kudin kayan lefen, abinci ya siya, Shekara nawa zasu yi suna cin abincin shi da Matarsa kafin ya kare.

5) Yanzu da yayyi wannan lefen ya nunawa 'yata shi mai arziki ne, idan zama yayi zama tsakaninsu har ta gane abinda take zato ba haka bane, yana ganin zai yi mutunci a idonta.

6) Shike nan yana so 'yata ta ringa alfahari acikin qawaye cewa babu wacce aka yiwa lefe kamar nata, wanda hakan zai jawo mata kiyayya da hassada a tsakanin qawayenta, kuma shi kansa alfaharin haramun ne.

7) Yana daga cikin al'adar da ta haddasa zinace zinace a kasar Hausa, domin samari basu da wadatar hada kayan lefe. Gara su kebe da 'yan matan nasu yafi sauki.

Na fada kuma babu canji ko dai a rage lefe ko kuma a dakatar da maganar aure har sai lokacin da shi da iyayensa s**a fahimci abinda nake nufi.

Idan an rage lefen anyi biki har ta tare, idan yana so ya siya mata kantin kwari ta ajiye a dakinta babu ruwa na, matarsa ce.

Me zaku ce gameda wannan Uban?

Address

Yandoma Bakin Dandali
Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Likitan Yadi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share