05/10/2025
Wani malami yana bada labari yana cewa:
Wata rana yana cikin tukin motarsa ne, sai wani jami’in kan hanya ya tsayar da shi.
Jami’in ya masto kusa da shi ya fara tambayar lasisin tuki da takardun motar, yana kallon fuskarsa ta cikin bakin tabarau dake idonsa.
Sai ya ba shi dukkan takardun da aka nema. Jami’in ya ce da shi:
Yallabai, Ba ka ɗaura seat belt ɗinka ba.
Na ce, “Eh, gaskiya haka ne.”
Ya ce, “Wannan laifi ne babba.”
Na ce, “Na yarda, na yi kuskure kuma na cancanci hukunci.”
Sai jami’in ya fara rubuta takardar tara, sannan ya tambaye ni:
“Kai malami ne ko?”
Na ce, “Eh.”
Sai ya cigaba da cewa, “Idan ɗalibi ya yi satar amsa a dakin jarabawa, kana yafe masa?”
Na ce, “A’a.”
Sai ya ce, “To me kake yi masa?”
Na ce, “Ina hukunta shi bisa doka.”
Sai jami’in ya miƙa min takardar tara yana murmushi, sannan ya ce:
“Za ka iya saukowa daga cikin mota, don Allah?”
Sai na sauko cikin mamaki, kwatsam sai ya rungume ni, ya riƙe ni sosai. Na kasa magana saboda mamaki.
Sai ya ce:
“Malam, ni ne tsohon ɗalibin nan naka, shin ka tuna lokacin da mukayi satar amsar lokacin jarabawa tare da ɗanka. Ka hukunta mu duka, ka kwace takardunmu duka, ba ka bamu maki ko daya ba, kayi mana hukunci daidai, duk da cewa akwai ɗanka a cikinmu.
Tun daga wannan rana, na fahimci cewa doka an ƙirƙire ta ne domin tayi aiki akan kowa, babu wanda yake saman doka, ba tare da nuna bambanci ba, ko da kuwa ɗanka ne.
A wancan lokacin, na yi kuka sosai saboda girmamawa gare ka, da kuma jin takaici saboda ka hukunta ɗanka don gaskiya. Tun daga nan ka zama abin kwaikwayo na.
Sai gashi yau kuma, Malam, nima ina aiwatar da irin dokar gare ka, ba tare da nuna son kai ba, ko da kuwa akan ɗana ne zan aiwatar da ita.”
Na kasa riƙe hawayena saboda farin ciki, ganin cewa daya daga cikin ɗalibaina ya fahimci ma’anar gaskiya da rikon amana.
Shi ma kuma yana ƙoƙarin danne hawayensa saboda kare mutuncin kakin da yake sanye a jikinsa.
Sai ya fito da wasu kuɗi daga cikin aljihunsa, ya ce:
“Don Allah, Malam, ka kar