Faira sitirar bayi

Faira sitirar bayi Niass sahibul sirri

Wannan Fa Duk Sun Tarune Saboda Manzon Allah (S A W)Wannan Fa Duk Basu da Wani Burinda Ya Wuce ayita Fada Musu Manzon Al...
07/09/2025

Wannan Fa Duk Sun Tarune Saboda Manzon Allah (S A W)

Wannan Fa Duk Basu da Wani Burinda Ya Wuce ayita Fada Musu Manzon Allah (S A W)

Wannan Fa Kwana akayi a Tsaye Ana Sauraron Tarihin Manzon Allah (S A W)

Ubangiji Ka Kara Mana Soyayyar SHUGABA (S A W)

MAULIDIN SHUGABA SAW Kai tsaye daga madinatu khaulak Shekh Mahi cisse yarabawa Al,ummar Annabi Shanu da Rakuma Adadi Mai...
07/09/2025

MAULIDIN SHUGABA SAW

Kai tsaye daga madinatu khaulak
Shekh Mahi cisse yarabawa Al,ummar Annabi Shanu da Rakuma Adadi Mai ya wa .

Allah Yasa Ka masa da Al khairi Al barkacin Annabi s a w 🥰

MAI INKARIN CHARBI INA HANKALINKA KE ZUWA NE.1-Ka iya hawa Jirgi kaje aikin Hajji da mota don zuwa Da'awa.2- Kake amfani...
31/08/2025

MAI INKARIN CHARBI INA HANKALINKA KE ZUWA NE.

1-Ka iya hawa Jirgi kaje aikin Hajji da mota don zuwa Da'awa.

2- Kake amfani da Sifika wajen Isar da sakonka.

3- Kake amfani da Computer wajen karatun Kur'ani.

4- Kake Amfani da Agogo domin sanin lokacin Sallah, da Kalkuleta domin hisabin Zakkah.

5- Kake aminta idan aka kalli watan Ramadana da na'urar Telescope.

6 Kake iya tsara Jadawalin Lokutan Sallah a cikin Masallacinka.

Amma rike "Charbi" wajenka Bidi'ane, koyi da Yahudawa, ko yaushe aikata wadancan kuma ya zamo koyi da Sahabbai..?

ALLAH YA GANAR.

ALHAMDULILLAH.

Tarihin duniya na nuna cewa kowace al’umma tana da fitilu da aka kunna mata na lokaci. Amma hasken da ya fi kowane haske...
30/08/2025

Tarihin duniya na nuna cewa kowace al’umma tana da fitilu da aka kunna mata na lokaci. Amma hasken da ya fi kowane haske shi ne wanda aka bayyana a cikin mutum ɗaya, wanda Allah Ya ce game da shi:

"وَمَآ أَرْسَلْنَٰكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَٰلَمِينَ"

(“Ba Mu aike ka ba, sai dai rahama ga talikai” – Al-Anbiyā’: 107).

Wannan magana ta buɗe ƙofa ga sirri mafi girma: sirrin aike.

Aike ba isar da saƙo kawai ba ne. Idan mail yana kawo wasiƙa, shi ba ya zama wasiƙar kansa. Amma Annabi ﷺ shi ne wasiƙa, shi ne saƙo, shi ne ma’anar da Allah Ya nufa. Shi yasa Qur’ani ya kira shi:

"قَدْ جَاءَكُم مِّنَ ٱللَّهِ نُورٞ وَكِتَٰبٞ مُّبِينٞ"

(“Lalle wani haske daga Allah da littafi bayyane sun zo muku” – Al-Mā’ida: 15).

Wannan yana nuna cewa aike bai tsaya ga magana ba; aike shi ne bayyana hasken Allah cikin mutum, cikin harshe, cikin hali, cikin zuciya.

Sirrin aike shi ne haɗuwa tsakanin abin da yake sama da abin da yake ƙasa. Sama tana da haske, ƙasa tana da jiki. Idan haske kaɗai aka sauko da shi, ido ba zai iya kallonsa ba, kamar hasken rana tsantsa. Idan jiki kaɗai aka haifa, labarin mutum zai ƙare cikin ƙabari. Amma Allah ya lulluɓe haske cikin jiki, ya sa shi tafiya a cikin kasuwanni, ya zauna da iyali, ya yi dariya da sahabbansa, amma duk wannan yana ɗauke da rahamarSa. Wannan shi ne sirrin aike: rahamar Allah cikin surar mutum.

Qur’ani ya bayyana shi da cewa:

"لَقَدْ جَآءَكُمْ رَسُولٞ مِّنْ أَنفُسِكُمْ عَزِيزٌ عَلَيْهِ مَا عَنِتُّمْ حَرِيصٌ عَلَيْكُم بِٱلْمُؤْمِنِينَ رَءُوفٞ رَّحِيمٞ"

(“Haƙiƙa ya zo muku Manzo daga cikinku, mai tsananin damuwa da abin da zai dame ku, mai tausayawa, mai jin ƙai ga muminai” – At-Tawba: 128).

A nan an bayyana sirrin aike a cikin ma’anar tausayi: shi mutum ne “min anfusikum” amma zuciyarsa ba kamar sauran mutane ba; zuciyarsa rahama ce mai cike da tausayi.

A falsafar ruhaniya, za a ce sirrin aike shi ne lokacin da Allah ya sa duniya ta ji ƙamshin sama. Aike shi ne hanyar da sirrin Ubangiji ya zama magana, ya zama misali, ya zama tafarki.

Shi yasa Annabi ﷺ ya ce: “Innama bu‘ithtu li utammima makarim al-akhlaq” – “An aiko ni ne kawai domin in cika kyawawan ɗabi’u.” Wannan ba doka kawai ba ce, sai dai fitila ce da ke nuna hanyar samun Allah.

Saboda haka, sirrin aike shi ne cewa Allah bai bar mu cikin duhu ba, Ya aiko mana da haskenSa cikin mutum domin mu iya gani da ido, mu iya bi da ƙafa, mu iya kwaikwayo da hali. Wannan shi ne ma’anar cewa Annabi ﷺ rahama ce ga talikai: rahama ce da ta sauka cikin harshen mutum, cikin dariya, cikin hawayen ibada, cikin halin juriya.

A ƙarshe, idan muke tunani a kan Rabi’ul Awwal, ba wai muna waiwayen haihuwa kawai ba ne. Muna waiwayen ranar da Allah ya bayyana sirrinSa cikin mutum, ranar da aka bayyana aike rahamar da ta haɗa sama da ƙasa, ruhu da jiki, haske da kalma. Wannan shi ne ainihin sirrin aike: cewa Annabi ﷺ ba kawai wakili ba ne, sai dai shi ne rahamar Ubangiji da kanta da aka aiko cikin halitta.

TARBIYAR SUFAYE A tsarin tarbiyya da jagorancin sufaye, akwai matakai daban-daban da Shehunai s**a shimfiɗa domin gyaran...
29/08/2025

TARBIYAR SUFAYE

A tsarin tarbiyya da jagorancin sufaye, akwai matakai daban-daban da Shehunai s**a shimfiɗa domin gyaran muridai. Wannan tsari ya samo asali daga koyarwar manyan Shehunanmu, na ga wani tsari na Maulanmu Al-Allama Sidi Muhammad al-Mashri da ya kawo shi a cikin littafinsa mai suna Rawḍ al-Muḥibb al-Fānī, inda ya bayyana yadda Shehi yake karɓar muridi da yadda yake tafiyar da shi a bisa matakai har zuwa ga karshen kusanci.

Da’irar Shehi

Shehi yana da wasu da’irori guda uku na tarbiyyartar da muridi:

1. Da’irar Nesa (الدايرة البعيدة)

2. Da’irar Tsaka-tsaki (الدايرة المتوسطة)

3. Da’irar Kusa (الدايرة القريبة)

1. Da’irar Nesa

Idan murid ya fara zuwa wajen Shehi, zai karɓe shi da abin da ya dace da halinsa – ya ba shi wuridi (azkar) tare da wasu addu’o’i da s**a dace. Sai ya sanya shi a da'ira nesa, ya bar shi tare da sauran jama’a, ba tare da ɗora masa wasu sharadi ba har ma ya bar shi da wasu halayensa babu batun tilasta masa wani abu, sai dai kawai wuridi. A wannan lokaci Shehi yana lura da shi daga nesa, yana kallo ko zai samu cigaba.

2. Da’irar Tsaka-tsaki

Idan Shehi ya lura murid ya fara nuna ƙwazo, sha’awa da niyyar bin hanyar sufanci, sai ya shigar da shi cikin da'irar tsaka-tsaki. A nan Shehi zai fara ba shi wasu umarni, ya hana shi wasu abubuwa, amma ba tare da tsanantawa ba. Wannan mataki ne na horo amma cikin sauƙi da sassauci.

3. Da’irar Kusa

Idan Allah Ya so murid ɗin ya shiga halartar sirri (ḥaḍra), Ya shirya shi da soyayyar Allah, soyayyar Manzon Allah (Sallalahu alaihi wa salam), da soyayyar Shehinsa, sannan ya yi niyya ta gaskiya wajen hidima da ɗaure zuciya cikin tsarkakewa – Shehi zai tabbatar cewa muridi ba shi da wata manufa wajen bin Shehi sai tsira daga halaka ta lahira.
A wannan lokacin sai Shehi ya shigar da shi cikin da'irar kusa, inda yake ɗora masa sharudda bisa ga halinsa da matsayin tarbiyyarsa. Wannan shi ne cikakken kusanci da Shehi.

Wannan tsari na matakai uku yana nuni da hikima da tausasawar Shehunanmu wajen tarbiyyar muridai. Ba sa tilasta murid a matakin farko, sai sun ga ya nuna ƙwazo da ƙaunar tafiyar. Har sai zuciyarsa ta cika da soyayyar Allah da Manzo da Shehi, sannan a dauke shi zuwa ga matakin kusanci. Wannan tsari yana tabbatar da cewa tarbiyyar sufaye tana tafiya ne bisa hikima, hankali da tausayi, domin a karshe murid ya zama bawan Allah na gaskiya,.

Rashin bin wannan tsari na mataki mataki ne ya haifar mana da gurbattatun muridi yanzu lamarin ya koma kamar gasa, da mutum ya zo babu jarabawa mataki mataki sai kawai a ce ya kamata ka yi wusuli.

Kafin wannan lokacin idan kaje a baka wazifa ba dukka za a ce an baka ba wani Shehi cewa zai yi kaje ka dinga yin iya lazimun safe da idan ka kwana biyu kana yi sai a ce to ga lazimun yamma idan ka tabbata kana yi sai a baka wazifa kuma a ce ka dinga zuwa zikirin Juma'a

Dan Allah sabbabin Shehunanmu a dinga kula da irin wannan.

 ❣️KUƘARA MANA HAUKA ACIKINKU BIJAHI SAYYADA HAFSATU
28/08/2025

❣️
KUƘARA MANA HAUKA ACIKINKU BIJAHI SAYYADA HAFSATU

Sheikh Ahmad Aliyu  Abulfathi RTA akoda yaushe yakan kusanto da Almajiranshi kusa dashi yana somusu  dukkan Alkhairi a r...
28/08/2025

Sheikh Ahmad Aliyu Abulfathi RTA akoda yaushe yakan kusanto da Almajiranshi kusa dashi yana somusu dukkan Alkhairi a rayuwansu baya fifita kanshi akansu.Tare suke sallah tare suke wazifa tare suke tafiya tare suke cin abinci.
Ya na girmamasu, suna girmama shi. Yana musu kallon 'ya'ya suna masa kallon uba.Haka s**a rayu cikin aminci da kwanciyar hankali hars**a koma ga Allah. Allah ka sakawa sheikh Ahmad Abulfathi da Alkhairi.

Sheikh Imam Hassan Cisse Allah Ya Jikansa Ya Gafarta Masa.Wannan hoton lokacin da Imam yake Kasar Denmark Cikin Aikin Ya...
28/08/2025

Sheikh Imam Hassan Cisse Allah Ya Jikansa Ya Gafarta Masa.

Wannan hoton lokacin da Imam yake Kasar Denmark Cikin Aikin Yada Addinin Allah A Lokacin Rayuwansa. Allah Ya Saka Masa Da Alhairi Amin.

SHEHUNKU SHINE JIRGIN KU A hakikanin tafarkin tasawwuf, malamai sun yi bayanin cewa Shehi (Shaykh al-Tarbiyya) shi ne ja...
28/08/2025

SHEHUNKU SHINE JIRGIN KU

A hakikanin tafarkin tasawwuf, malamai sun yi bayanin cewa Shehi (Shaykh al-Tarbiyya) shi ne jagora da kuma madogara ga mai neman Allah. Ba tare da jagora ba, mutum yana shiga cikin hadarin tafiya cikin "teku" na zuciya da shakku tafiyar ba tare da kwararre ba ba ta taɓa yiwuwa.

An ce:

مَنْ لا شَيْخَ لَهُ، فَشَيْخُهُ الشَّيْطَانُ

Wato: Wanda ba shi da Shehi, shaidan shi ne jagoransa.

Saboda haka, an ɗora wa muridi nauyin ya bin Shehinsa wanda domin shi ne zai gyara zuciya (al-bāṭin), domin aikin Shehi shi ne ya tsarkake zuciya daga tarkacen duniya da son zuciya, sannan ya raya ta da zikiri da soyayyar Allah da ManzonSa Sallalahu alaihi wa salam.

Shehinka shi ne a matsayin jirgi

Shehi shi ne jirgin da ke tsallaka tekunan soyayya zuwa ga Manzon Allah Sallalahu alaihi wa salam shi ne yake keta hijabai masu katange zuciya. Wannan ma’anar tana cikin kalaman daga manyan malamai na tasawwuf.

Maulanmu Shehu Tijjani (Allah ya kara masa yarda) ya na faɗar cewa: "Shehi shi ne gadar da muridi zai bi don isa ga Madinatul Ma’rifa."

Imam al-Qushayri a cikin Risālatul-Qushayriyyah ya bayyana cewa, muridi ba zai iya isa ga matsayi na ƙwarai ba sai da shugabanci da jagoranci na Shehi, saboda shi ne mai ba shi usulun tazkiya da sirrul ma’rifa.

Shehin ku shine hanyar da kuke isa ga Manzon Allah Sallalahu alaihi wa salam, wanda kuma zai kai ku ga Allah Madaukakin Sarki. Wannan ba wai a matsayin wasiyya bane, a’a, a matsayin hanya ta ruhaniya da aka tabbatar da ita daga ayyukan manyan malamai.

Daidaito (al-istiqāma) shi ne iska da ke tura jirgin ku. Idan aka rasa wannan iska, jirgi ba zai motsa ba. Idan aka yi kuskure wa Shehi ko aka yi ganganci, yi masa rashin biyayya iskar nan zata tsinke, ka daga jirgin tafiya ta tsaya. Amma matuƙar muridi ya kasance da gaskiya, ikilasi , da haƙuri, ba zai nutse ba, kuma ba zai rasa tafarkin ba.

Imam Junayd (Allah ya kara masa yarda) ya ce:

"Hanya ce da ta ginu da gaskiya; wanda ya yi gaskiya ya tsira, wanda ya

YA AHMADU ABILFUTUHATINI KAI NAKE GANI MAI DUBAN SHINE YACE NA DUBO KA👌❤️
28/08/2025

YA AHMADU ABILFUTUHATI
NI KAI NAKE GANI MAI DUBAN SHINE YACE NA DUBO KA👌❤️

Bijayi baba jami'u bulala
28/08/2025

Bijayi baba jami'u bulala

28/08/2025

Address

Naija State
Minna

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Faira sitirar bayi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share