08/06/2025
Kada ka yi fushi
Fushi kalma ce da ke nufin tsananin ɓacin rai ko jin haushi saboda wata matsala ko cutarwa da mutum ya fuskanta daga wani. Wannan hali na fushi yana tasowa daga zuciya, yana bayyana ta fuska, harshe, da jiki. Sau da dama, fushi yana zama kamar gobara: yana tasowa da ƙarfi, yana kone zuciya, kuma idan ba a kashe shi da wuri ba, yana iya cinye mutunci da kwanciyar hankali gaba ɗaya.
Dalilan Fushi
Fushi ba ya zuwa haka kawai; akwai abubuwa da ke haddasa shi. Ga wasu daga cikinsu:
1. Raɗaɗin Zuciya: Lokacin da mutum ya ji an ci masa mutunci ko an yi masa abin da bai so ba, fushi na iya tashi.
2. Hassada da Kishi: Wasu suna jin fushi saboda sun ga wani yana da abin da su ba su da shi.
3. Yawan Damuwa da Rashin Natsuwa: Idan mutum yana cikin matsin rayuwa, ko yana cikin yanayi mara daɗi, sau da yawa yana jin fushi da sauƙi.
4. Rashin Haƙuri: Mutum mai rashin juriya yana saurin fusata a kowane lokaci.
5. Zargi ko Karyar Magana: Idan mutum ya ji an zarge shi da abin da bai aikata ba, fushi yana taso masa.
6. Raunin Imani: Idan imani bai yi karfi ba, zuciya ba ta da ƙarfin sarrafa fushi.
Illolin Fushi
1. Illa ga Jiki da Lafiya
Fushi yana haifar da hawan jini, bugun zuciya da sauri, gajiya, da ƙaiƙayi. A wasu lokutan yana iya haddasa bugun zuciya (heart attack) ko hawan jini (high blood pressure) wanda ke iya zama ajali.
2. Illa ga Zuciya da Hankali
Fushi yana hana mutum yin tunani cikin natsuwa. Yana gurbata tunani, yana haifar da yanke shawara marar hikima da haƙuri.
3. Illa ga Zamantakewa
Mutum mai yawan fushi ba ya jituwa da mutane. Yana ɓata alaƙa da abokai, iyali, ma’aikata, da maƙwabta.
4. Illa ga Addini
Fushi yana iya sa mutum aikata haram, kamar zagi, duka, ƙarya, laifi, ko cin zarafi. A hadisi Manzon Allah (SAW), yace :
> “Kar ka fusata, kar ka fusata, kar ka fusata.”
(Bukhari)
5. Illa ga Al’umma
Fushi yana iya jawo faɗa, yaƙi, kisan kai, da ƙiyayya tsakanin al’umma. Tarihi ya nuna cewa rikice-rikice da dama sun samo asali ne daga saurin fushi da rashin juriya.
Hanyoyin Magance Fushi
1. Yin Shiru – Kada ka yi magana a lokacin fushi, domin kalmomin da za su fito ba su da kyau.
2. Canja Matsayi – Idan kana tsaye ka zauna, idan kana zaune ka kwanta.
3. Yin Alwala ko Wanka – Ruwan sanyi yana kashe gobarar zuciya.
4. Karanta Addu’a – Kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar da cewa:
> "A’udhu billahi minash-shaytanir-rajim"
5. Tuna Sakamako – Ka tuna da illar abin da fushi zai iya jawowa. kamar kashe mutum ko lalata zumunci da abota .
6. Ka yi wa kanka horo – Koyaushe ka rika tunatar da kanka illar fushi, kuma ka sa kanka a hanya mai kyau.
7. Yawan Karanta Alkur’ani da tarihin Annabi saw, da magabata na kwarai zai Inganta imani kuma ya taimaka wajen hana zuciya tasowa da saurin fushi.
Kalmomin Hikima da Karin Magana
"Haƙuri maganin fushi."
"Mai fushi baya ganin gaskiya."
"Fushi ya fi wuta lahani."
"Wanda ya fi ƙarfin zuciyarsa, shi ne gwarzon gaske."
A ƙarshe, fushi hali ne da ke da illa da yawa a rayuwa. Idan aka bar shi ya yi yawa zai dinga tunzura zuciya, yana iya haddasa abubuwa da mutum zai yi nadama akansu. Amma idan aka sarrafa shi da hikima, fushi zai iya zama wata hanya ta samun lada da ɗaukaka a wajen Allah.
Kamar yin fushi idan an taɓa Addinin Allah.
Ya kamata mu yi ƙoƙari mu bi tafarkin Annabi Muhammad (SAW), wanda ya kasance mafi hakuri, mai kyautatawa, kuma wanda ke sarrafa fushi da warewa.
Allah ya kara mana son Annabi saw da koyi da shi.
Daga Madina- Almunawwarah