08/03/2025
ALBARKA CENTER FOR MARREAGE COUNCELLING RANO
WADDA KE BABBAR SIKANDIREN ARABIYYA TA ‘YAN MATA DAKE BAYAN TASHA, RANO
(G.G.S.I.S RANO)
Suna :………………………………………………………………… Kwanan Wata :…………………….
(Assalamu Alaikum)
Wannan cibiya mai Albarka ta shirya wannan fadakarwa ne ga dalibanta kamar yadda ta sabayi a duk karshen ko wanne wata domi inganta rayuwar su data sauran al’ummar musulmi baki daya.
TAKEN FADAKARWAR (LECTURE)
ALAMOMIN DA MACE ZATA GANE TA KAMU DA SOYYAYA TA GASKIYA
Wadannan Alamomi zasu zamarwa mace mabudi domin tantance wanda za’ayi rayuwar aure dashi da soyyaya ta gaskiya:-
Girmama namiji da ganinin Mutun cin sa.
Jin Kunyarsa.
Yawan ambaton Sunan sa.
Yin Kishi Akan sa.
Fifita Shi akan Sauran Maza.
Son Yimasa hidima da son taimakon sa.
Yawan yi Masa Murmushi da son zama dashi.
Yawan gaskata shi akan dukkanin Al’amura.
Nuna Juriyaa da Jarumta gaban sa.
Saurin zubar da Hawaye a gaban sa ko akan sa
Nuna So da Kauna a gareshi da tsoron bacin ran sa.
Yin Farin ciki Idan akaji Wani abu mai dadi akan sa da Kuma shiga damuwa Idan an samu akasin haka.
ما تحبه النساء من الرجال " خالد جاد"
Shugaban Cibiya (Center)
Mal Aliyu Usman Abdullahi
(Aliyu Tamisi Rano)
08037990078, 09046626640