17/01/2026
Gidauniyar Dr Abdulmumin Aminu Zaria, a yau ta gudanar da bikin yaye daliban da ta koyarwa sana'o'in hannu mutum dubu daya da dari biyu da hamsin (1250) a makarantar LEA Primary School unguwar sarki karamar hukumar Kaduna ta Arewa, karkashin jagorancin Dr. Hon. Abdulmumin Aminu Zaria.
Jigon siyasar karamar hukumar Igabi da jihar Kaduna baki daya, Rt Hon Muhammad Abubakar Mamadi, ya kasance cikin mahalarta taron inda ya ba ɗaliban da aka yaye gudummawar sa ta Naira miliyan Hudu (4,000,000).
A ƙoƙarin su na inganta rayuwar matasa ta hanyar dogaro da kai, tare da ba Mai girma Gwamnan jihar Kaduna goyon baya dan sauke nauyin al'ummar jiha.
Allah Ubangiji ya bamu nasara🙏