Ama Made Collections-AMC

Ama Made Collections-AMC Domin samun dinkakkun kaya da huluna na maza masu kyau a farashi mai sauki.

"..People buy what they want, not what they need" !Idan na kintata daidai, hakan na nufin mutane na sayan abinda suke so...
24/11/2023

"..People buy what they want, not what they need" !

Idan na kintata daidai, hakan na nufin mutane na sayan abinda suke so ne, ba abinda suke da buqata ba. Na naqalto hakan ne daga littafin Femi Alabi mai taken "How to sell to Nigerians". Na kara tabbatar da hakan a satin da ya gabata.

Akwae wani da yazo sayan yadi wajena, ya dirje ya zabi shadda yar meter. Kamar wasa na fada masa kudi, ko tayi bai yi ba, ya biya. Yace inda hali ayi masa su ya samu na jumuah. Duba da yanayin sa kayanshi, ba shadda yakamata ya saya ba, saboda ba wani wadataccen sutura gareshi ba. Na bashi shawari da ya dibi yadi guda biu a maimakon shadda. Ai kuwa yace a'a ! . Nai ta mamaki, na ce hakane, lallai "people buy what they want, not what they need"!

Ko ma dai yayane, ku zo mu gwangwaje ku a AMC.

19/11/2023
"SKILLS" ko "DEGREE"?   Ina iya tuna lokacin ina makarantar sakandire, sa'an nan an saka ni wajen koyon gyaran mashin. T...
21/07/2023

"SKILLS" ko "DEGREE"?

Ina iya tuna lokacin ina makarantar sakandire, sa'an nan an saka ni wajen koyon gyaran mashin. To, sai Baban mu ya lura bana mai da hankali wajen zuwa gareji, na fi kokarin zuwa makaranta. An sha duka na akan bana zuwa gareji !

Wata rana dai, Baban mu yaga abu yaki karewa, kullum duka. Sai dai watara na, ya zaunar damu ya ke fada mana cewar; "kun ga garejin nan da kuke rainawa, zai iya taimakon ku wajen karatun ku". Duk da cewar maganar ba tayi wani tasiri akai na ba, amma saboda an alaqanta ta da makaranta, na dan rage kin zuwa. Daga karshe dai dole na bar gareji, don gaskiya bani da interest akan garejin, aka maida ni wajen koyon dinki daga baya.

Duk da cewar Baba na yayi karatu, kuma yana aikin gwamnati, bai yarda mun taqaita a zalla karatu ba, ya jajirce akan mu koyi sana'a. Kuma Alhamdulillah, sana'a tai mana rana.

Ko da zuwa na jami'a, wasu lokutan in naji dugu-dugu, na kan fita cikin gari nayi dinki, in na sayar na sami na shopping, wasu lokutan kuma bani ake naje na dinko a biya ni.

Karatu don samun satifiket, yana da muhimmanci sosai, in aka hada da sana'a, sai ya kara armashi.

Allah bamu sa'a. Ameen.

Address

Rimin Zayam, Bauchi
Toro

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ama Made Collections-AMC posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share