04/07/2020
SANARWA GAME DA HANYAR DAMATURU ZUWA MAIDUGURI
Sak**akon yadda hanyar Damaturu zuwa Maiduguri ta koma tarkon mutuwa, wanda a kusan kullun sai 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP sunyi shigar sojoji sun tare hanyar sunyi garkuwa da mutane...
Rundinar sojin Nigeria ta fitar da wannan sanarwa mai matukar fa'ida, akan guraren duba ababen hawa (checkpoint) wanda rundinar sojin Nigeria ta tabbatar dasu a hukumance akan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, sune k**ar haka:
-Benisheikh
-Jakana
-Auno
-Mainok
-Njimtilo
Rundinar sojin Nigeria tace idan ba wadannan gurare ba to babu inda sojoji suke duba ababen hawa a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, don haka jama'a su kiyaye tsayawa don kar su fada tarkon 'yan Boko Haram da suke yin shigar sojoji suzo su kafa shingen duba ababen hawa suna k**a mutane.
Jama'a ku taimaka wajen yada wannan sanarwan saboda amfanar al'umma gaba daya
Yaa Allah Ka tsare bayinKa daga fadawa tarkon 'yan Boko Haram Amin