01/08/2026
Hukumar Shari'a ta jihar Kano, ta buƙaci direbobin baburan adai-daita sahu, da su daina ɗaukar mata a gefen hagu da daman su, da ake kira da "Attachment" kasancewar yin hakan haramun ne a mahanga ta addinin Musulunci, bisa cuɗanyar da ake yi da matan.
Kwamishinan na biyu a hukumar Shari'ar addinin Musulunci a Kano, Sheikh Ali Ɗanabba ne ya bayyana hakan yayin da shugabannin ƙungiyar direbobin baburan adai-daita sahu ta (VOTORA) s**a amsa gayyatar da hukumar ta yi musu, a ranar Alhamis 30 ga Yuli, 2026.
Yayin ganawar ɓangarorin biyu sun tattauna mahimman batutuwa da za su ƙara kawo tsari da tsafta a sana'ar ƴan adai-daita sahu a jihar Kano, da kuma gudunmawar da za su bayar wajen yaƙi da sha da dillancin miyagun ƙwayoyi, da sace-sacen yara, da kuma daƙile matsalolin tsaro da ke damun jama'a a jihar,
Sheikh Ali Ɗanabba ya kuma buƙaci direbobin baburan adai-daita sahu, da su daina ɗaukar mata a gefen su ɓangaren hagu da dama, da ake kira da "Attachment" kasancewar yin hakan haramun ne a mahanga ta addinin Musulunci, bisa cuɗanyar da ake yi da matan.
Ya ce duba da yadda addinin musulunci ya hana cuɗanya da matan da ba muharramai ba, bai kamata dorebobin baburan adai-daita sahun su rinƙa ɗaukar mata a gefen nasu ba domin hakan haramun ne.
Ya kuma ce za su yi zama na musamman da ƙungiyoyin baburan adai-daita sahun domin yi musu wa'azi, domin ganin masu irin wannan ɗabi'ar sun daina.