Darul salafiyyah

Darul salafiyyah Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Darul salafiyyah, Kaduna.

15/08/2022

Wani sarki yana auren mata 4.

Ya kasance yana ƙaunar ta 4 sosai, kuma yana duk abin da zai iya yi wajen faranta mata rai.

Yana son ta 3 amma yana ganin da ta samu wanda yafi shi zata rabu da shi.

Ta 2 kuwa duk lokacin d ya shiga matsala ko kuma yake cikin damuwa toh ita take taimaka masa.

Amma ta farko kuwa ba ya wani kula da ita, tare da cewa ita tafi ƙaunarsa.... ita ta ba shi gudummawa wajen gina masarautarsa.

Sarki ya kwanta ciwon ajali. Sai ya tara matansa:

Ya cewa ta 4 shin in n mutu za ki yadda a binne mu tare? Ta ce, wallahi sam ba zan yarda ba.....ta tashi ta yi tafiyarta abinta...!

Ya cewa ta 3 ke fa? Ta ce, sam! Rayuwa akwai daɗi kana mutuwa wani zan aura..! Ta yi tafiyarta..!

Ya cewa ta 2 ke fa? Ta ce, k yi haƙuri ba zan iya ba, mafi girman abin d zan maka in raka ka maƙabarta in za a binneka...!

Ya kalli ta farko cikin yanayi na jin kunya, ya ce toh Saura ke......! Ta ce, na yadda ni zan bika, duk da ka wulaƙantani, ka mayar d ni bani da amfani, ka fifita wasu a kaina....!

Sarki ya fashe da kuka ya ce, wallahi da za a dawo mini da rayuwata baya da na karramaki kuma na girmamaki, da na ƙaunace ki fiye da komai kuma d na baki lokaci na gaba ɗaya...!

Abin fahimta:

Matar farko: Ita ce gangar jikinka, duk yadda ka kai da gyara shi da ƙaunarsa tabbas da ka mutu komai ya ƙare.

Mata ta 2: Dukiyarka da Kadarorinka, kana mutuwa zasu koma hannun wasu...

Mata ta 3: Ƴan uwanka da danginka da Ƴaƴanka.

Mata ta 4: Aikinka na gari, shi kaɗai zai bika amma kuma shi ne bamu damu da shi ba, tare d cewa shi kaɗai zai bi mu Ƙabari.
*Sukairaj Hafiz Imam*

28/04/2022

G O M A N - Ƙ A R S H E.

" Hadisi ya tabbata daga Nana A'isha r.a. take cewa idan goman karshe na Ramadan s**a shigo, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam " yana raya Daransa, yana barin matansa, yana kara nau'in Ibadah da baya yi a cikin goman farko da goman tsakiya. " Dan haka mu yawaita ayyukan Ibadah a cikin wannan goman ta karshe. "

DR. JABIR SANI MAI HULA.
( Hafizahullah )

Allah yasa mu dace. Allah ya bamu ikon dagewa yasa muna cikin wanda zasu dace da albarkar wannan goman ta ƙarshe. Allah haɗa mu a aljannah baki daya. Ameen ya Allah.

28/04/2022

YIN FUSHI DA MUSULMI DAN'UWANKA.

" Idan kana jin haushin mutum musamman mutum Musulmi, Wallahi kana jawa kanka hatsari. Ba mamakin wannan Musulmin da kale jin haushinsa, saboda wani Kuskure ne da kake gani yana yi, wata kila Allah SWT ya jima da yafe masa, ya rubuta shi cikin yan aljannah. Kai baka sani ba. Yanzu da dan aljannah kake fushi. Kaki kayi masa afuwa. Saboda haka mu yafewa juna. "

DR. GARBA UMAR GOKAJI.
( Hafizahullah )

Allah ka shiryar damu baki daya. Allah ka haɗa kan musulmi baki daya. Ka yafe mana baki daya. Allah tabbatar damu akan hanya madaidaiciya baki daya.

30/03/2022

*"TUNATARWA"*

*"Ka bi a hankali wurin ƙoƙarin tozarta mutane, domin akwai wasu bayin Allah wanda duk lokacin da ka yi ƙoƙarin tozarta su, to kai ne zaka wulaƙanta"*.

30/03/2022

☘️Ya Ubangiji Ka Gafarta min Ka Kar6i Tubana, Domin Kai Mai Gafarane Mai Jin Qai.🤲

🌹🌹An Kar6o Daga Abu Hurairah Yace,Hakika Wani Mutum Yace : "Ya Manzon Allah S.A.W, Yi min Wasiyya, Domin Inaso Zanyi Tafiya,Sai Yace Masa:" *Kaji Tsoron Allah, Kuma Kayi Kabbara Akan Duk Wani Abu Mai Girma, Kuma Mai Daraja, Bayan Da Mutumin Ya Tafi, Sai Ma'aiki S.A.W Ya Yi masa Addu'a Yace : "Ya Ubangiji Ka Matso Masa Da Nesa Kusa, Ka Saukaka Masa Tafiyar."*🌹🌹

Tirmizy Ya Rawaito,Albany Ya Inganta

30/03/2022

🩸FADAKARWA GA ME DA RAMUWAR AZUMIN RAMADAN🩸

♦️Duk Wanda Ake Binsa Azumin Ramadan Wanda Ya Wuce, Dole ne Ya Rama Kafin Na Wannan Shekarar Ya Kama.♦️

🌹🌹Domin An Kar6o Daga Nana A'isha R.A Tace :*"Ya Kasance Ana Bina Azumin Ramadan, Amma Ba Na Samun Damar Ramawa Sai A Watan Sha'aban."*🌹🌹

Bukhari da Muslim

30/03/2022

🌹🌹Manzon Allah S.A.W Yace : *"Idan Dayan ku Zai Sha (ruwa), To Kada Yayi Ninfashi A Cikin kwaryar, Haka ma Idan Yaje Bandaki, Kada Ya Ta6a Tsiraicinsa Da Hannun Dama, Kuma Kada Yayi Tsarki Da Hannun Dama."*🌹🌹

Bukhari

26/03/2022

*“Wanda ya kiyaye ALLAH a kuruciyarsa da Karfinsa, ALLAH zai kiyaye shi yayin tsufarsa da raunin karfinsa, kuma zai jiyar dashi da jinsa da ganinsa da karfinsa da hankalinsa.”*

26/03/2022

TUNATARWA.

" Kayi kokari mutane suyi maka shaida, koda da Hali daya ne mai kyau. "

SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA.
( Hafizahullah )

Allah ya kara mana azama da riko da addini. Yq bamu ikon kiyaye dokokin adddinin muslunci. Ya shiryar damu baki daya akan sunnar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Ameen ya Allah.

Address

Kaduna

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Darul salafiyyah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share