03/03/2026
MUNA NEMAN MASANA DA MASU HORASWA (CALL FOR TRAINERS)
Kungiyar Rigasa Entrepreneurs Network (REN)
tana neman kwararru masu hazaka da kishin gina al'umma wadanda s**a kware a harkar sarrafa sinadarai (Chemical Production) don kasancewa jagororin koyarwa a shirinsu na gaba.
Muna neman mutanen da s**a kware sosai wajen hada wadannan kayayyaki:
* Kula da Fata: Body Lotion da Vaseline.
* Tsaftace-tsaftace: Sabulun Guda (Bar Soap) da Sabulun Gari (Detergent).
* Kayan Ruwa: Sabulun Ruwa (Liquid Soap) da Turaren Daki (Room Freshener).
Abubuwan da ake bukata daga mai nema:
* Dole ne ya zama ya kware sosai a fannin da yake son koyarwa.
* Yana da ikon bayyana dabarun hadin cikin sauki ga dalibai.
* Yana da kishin ganin matasan Rigasa sun dogara da kansu.
* Zai iya sadaukar da lokacinsa don horas da dalibai 15 a kowane aji.
Me yasa zaka kasance tare da mu?
Wannan dama ce ta bada taka gudunmawar wajen Sake Gina Zamaninmu Ta Hanyar Kirkire-kirkire da kuma kasancewa mamba a babban rukunin kwararru na Rigasa Entrepreneurs Network.
Yadda za a nuna sha'awa:
Idan kana da wannan kwarewar kuma kana shirye ka taimaka wa al'ummarka, tuntuΙe mu ta wadannan lambobin wayar don tattaunawa:
π 07043664388 | 09076793851 | 07078369989 | 09069414144
"Zama silar nasarar wani yau. Tare za mu gina Rigasa!"