17/09/2025
Sanarwa ta musamman !!! Ga dukkanin abokan cinkayyarmu game da rufe shagonmu.
Assalamu alaikum wa rahmatullah, ina amfani da wannan dama domin sanarwa da ɗaukacin abokan cinikayyarmu ; wanda s**a kawo mana ɗinkin kaya, da kuma wanda s**a kawo mana wankin hularsu. Zamu rufe shagonmu na tsawon wata guda sabo da wata tafiya domin cika ka'idar kammala karatunmu da mukayi.
Za mu rufe shagon ne daga ranar Talata 23rd ga watannan da muke ciki September 2025 Har zuwa karshen watan 10 na October, wannan rufe shagon zai iya tsayawa a iya wannan kwanakin mutukar yaran shagon sun dawo gari kafin lokacin ko kuma ya wuce hakan.
Da wannan nake kara kira ga duk wanda yasan da kayansa a wajenmu ; Hularsa ko kuma kayan sawarsa ko kuma siyayya to yayi kokarin zuwa ya karbi kayansa daga nan zuwa ranar talata mai zuwa kafin sallar magariba. Rashin zuwa a wannan lokacin zai sanya mutum ya tarar da shagonmu a rufe kuma bana gari.
Wanda kuma suke son kawo aikinsu zasu iya kawowa kafin ranar juma'a 19 ga September 2025 . Daga ranar juma'a bazamu sake karɓar aikin kowa ba har sai Allah ubangiji ya dawo damu lafiya.
Ina rokon wanda ya sami wannan sanarwa ya sanarwa da wanda yasan sakon bai riskeshi ba don kada sai ya tashi amfani da kayansa kuma ya rasa.
Na gode da dukkan kulawaku, da yardaku a garemu da kuke bamu ayyukanku. Ina alfahari daku da jin dadin yaddda kuke kawomana aiki ko yaushe.
Daga Naku
Sulaiman Sani Sulaiman Bazooka
CEO
SS Bazooka kupta design Chiromawa