23/08/2023
Quna / Quncin Zuciya💔😢
Duk Yadda Rayuwa Tai Dadi, Ba Wani Mutum (Namiji Ko Mace) Da Zuciyarsa Zata ku6uta Daga Qunci Ko Jin Quna A Wasu Lokuta, Inma wani Ya 6ata maka Rai ko Haka kawai Kaji Bakin Ciki Da Damuwa Ta Dabaibaye Ranka😢 Duniya Kenan!
Lokacin Da ALLAH Yasa Annabi Adam Da Hauwa'u A Aljanna(Suna Jin Dadi Da Shaqatawa😍) Sai Yake Gargadinsu Gameda Shedan, Yace;
فلا يخرجنكما من الجنة فتشقى
"Karku Yadda(Shed'an) ya Fitar Daku Daga Aljanna, Zakusha Wahala"
Inde Rayuwar Duniya ne Ba Makawa Daga "Qunci / Bakin Ciki ko Damuwa"
Da Yawa Ckn Mutane Kan Shiga Damuwa Har Su zubda Hawaye😭 In Zuciyarsu Tai Qunci, Wani Har Yace Maka Ya Karanta Alqur'ani Amma Bakin Cikin Dayake Ji Yaqi Gushewa (Gaba Daya)😢
Allah Sarki!
NASIHA
Ya D'an uwa! Mai Fama Da Qunci, Bakin ciki ko Damuwa sbd Wata Qaddara data Sameka ko Yaudara Da Wani Yaima, Ko Cuta, ko Zalinci ko Ha'inci Mai Ha'inci, Qetar mai Qeta Ko hassadar Mai Hassada💔😢
Hakika Ubangijinka Na Sane Da Wannan Qunci Ko Bakin cikin Da Zuciyarka Ke Ciki.
ولقد خلقنا الإنسان ونعلم ما توسوس به نفسه ونحن أقرب إليه من حبل الوريد
ALLAH Yace "Hakika Mu Muka Halicci D'an Adam, kuma Muna Sane Da Duk Maganar dake Kai Komo Ckn Ransa, kuma -Hakika- Munfi Kusanci Dashi fiyeda jijiyar Dake Wuyansa"😍😍
Allahu Akbar!
Duba Girman Sani Da Ilimin Allah😍, inda Yace;
ويعلم ما في البر والبحر، وما تسقط من ورقة إلا يعلمها، ولا جبة في ظلمات الأرض ولا رطب ولا يابس إلا في كتاب مبين
Nace: Ubangijin Da Iliminsa Yake Kewaye Da Sanin Hatta Ganye inya Tsinke Daga Bishiyarsa(yana Zuba) Hakika Lallai Yana Sane Da Hawayen Nan Naka Dake Zuba😭
Yi Koyi Da Annabin Allah Ya'aqub ckn Tawakkali, Dogaro Da mika lamarin ga Ubangiji,
إنما أشكو بثي وحزني إلى الله
Hakika Farin Ciki💖 Zaizo Daga Ubangijin Zukata(ALLAH💕)