03/09/2024
MINTI 2 YA ISHEKA KA KARANTA...
Idan ka cire wani Abu daga cikin dukiyarka ka badashi sadaka , wannan sadakar zai maka Magana uku 3
1. zai ce maka fa ni'ima madalla da wannan Aiki da kayi, Dama Ni dukiya kararriya ce Amma yanzu ka dawwamar dani.
A cikin Al'kur'ani Allah yana cewa :
MAA'INDA K*M YAN FADU WA MAA INDALLAHI BAAQIY
Duk Abinda kuka mallaka zai kare Amma duk Abinda yake A gurin Allah mai wanzuwa ne
(SURAH- NAHLI Ayah 96)
Idan kayi kyauta ko sadaka tamkar kayi Ajiyane A wajen Allah, zata wanzu har kaci moriyarta A lahira
2. Dukiyarda ka bayar sadaka zata gayamaka cewa Ni kayan wasune Amma yanzu kamayarda ni naka
Dukiya kayan Magadaa ne, ba naka ba, da'ace zaka mutu yau duk sun zama gaado , daga ciki waɗanda s**a kasance Naka sune waɗanda ka kashesu A hanyar Allah da waɗanda kayi kyauta dasu ko ka bayar sadaka
3. Dukiyarda ka bayar sadaka zata faɗa maka cewa Kai ne kake gadina Amma daga yanzu ni zan zama mai gadinka
Kaine kake tsare dukiyarka wani zubin ka kaisu banki ka ɓoye, duk wani dukiyarda ka bayar sadaka zai zama mai baka kariya Ranar Alkiyama
Da'ace Allah zai bawa mamacci damar komowa duniya zai zaɓi yayi sadaka, Allah yana faɗin Ayayinda bawa yazo Mutuwa yakan faɗi cewa Ya ubangijina da za'a jinkirta min izuwa wani lokaci da nayi Sadaka, baice da zeyi Hajji ba ko umara ko sallah ko Azumi, Malamai s**ace mamacci bai Ambaci yayi sadaka ba sai dan ganin girman ladan sadaka da yagani Ayayinda ya mutu
Dan haka ku yawaita sadaka kusani mumini yana cikin inuwar Sadakarsa A Ranar Alkiyama
Duniya da Lahira Allah ta'ala yasa mu dace... Ameen