21/08/2026
Gwamna Radda Ya Ƙaddamar da Shugabannin APC Zalla na Ƙananan Hukumomi 34 da Mazabu 361 na Jihar Katsina
A ranar Juma’a, 21 ga watan Agusta, 2026, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D, CON, ya ƙaddamar da shugabannin Ƙungiyar APC Zalla na ƙananan hukumomi 34 da mazabu 361 na jihar Katsina. Ƙungiyar, wadda Sadaukin Kankia, Dakta Bala Nuhu Kankia, ya kafa kuma yake jagoranta, an ƙaddamar da ita ne a filin taro na People’s Square da ke Gidan Gwamnatin Jihar Katsina.
Gwamna Radda ya kuma yi kira ga sabbin shugabannin ƙungiyar da su yi aiki tukuru, tare da jajircewa da haɗin kai da sauran masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC a mazabunsu, wajen wayar da kan al’umma tare da yaɗa ayyukan ci gaba da wannan gwamnati ta aiwatar daga matakin mazabu zuwa tarayya.
Shi ma Tsohon Ministan, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ya yi kira ga sabbin shugabannin da su jajirce wajen ganin an samu nasarar Jam’iyyar APC daga sama har ƙasa, yana mai cewa nasarar jam’iyyar za ta taimaka wajen ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba da gwamnati ke gudanarwa domin amfanin al’umma.
A nasa jawabin, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Hon. Bishir Gambo Saulawa, ya yaba wa Dakta Bala Nuhu Kankia bisa kafa ƙungiyar, yana mai cewa za ta taimaka wajen ƙarfafa Jam’iyyar APC da kuma tabbatar da nasararta a zaɓen 2027, tare da ƙara wayar da kan al’umma kan ayyukan Gwamna Dikko Umaru Radda da na Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government
August 21, 2026.