Hadejia Central Masjid

Hadejia Central Masjid Hadejia Central Worshiping and Islamic Teaching Centre
(1)

16/12/2022

LACCA! LACCA!! LACCA!!!

Kwamatin Limaman Juma'a na karamar hukumar Hadejia, karkashin jagorancin Mallam Yusuf Abdurrahman Ya'u (Babban Limamin Masarautar Hadejia)

Na Gayyatar Al'ummar Musulmi maza da mata zuwa wajan gangamin lacca wadda ya shirya
Mai Taken: *ƘALUBALEN MATASA.*

Malamai masu gabatarwa: sun hada da:
1- M. Baffa Abdurra'uf (Na'ibin Limamin Masallacin Darus Salam, Yayari)
2- M. Muhammad Mahmud Dubantu (Malami Mai Karantarwa)
3- M. Muhammad Lawan Yankoli (Na'ibin Limamin Masallacin Usman Dan Fodiyo, Fantai)
4- M. Muhammad Sani Al-Hassan (Na'ibin Ladanin Masallacin Darus Salam, Yayari)

Shugaban taro: Maigirma Shugaban Karamar hukumar Hadejia Alhaji Abdulkadir Umar Bala T.O

Uban Taro: Maimartaba Sarkin Hadejia Alhaji (Dr). Adamu Abubakar Maje con. Wadda Maigirma Galadiman Hadejia Alhaji Usman Abdul-Aziz Zai wakilta.

Ranar: Asabat da Lahadi 23rd/24th Jumadaa Al-Ulah 1444 AH. --- 17th/18th December 2022

Wuri: Babban Masallacin Juma'a na Maimartaba Sarki, cikin garin Hadejia.

Lokaci: Bayan Sallah magrib zuwa Isha

Allah ya bada ikon halarta

Sign: Mallam Yusuf Abdurrahman Ya'u Babban Limamin Masarautar Hadejia.

05/09/2022

Assalamu Alaikum!

Yanzu haka a FM Hadejia

Ana watsa shirin, ga wanda basu samu damar halartar MUHADARA da aka gabatar ba ta kwamatin Limaman Juma'a na ƙaramar Hukumar Hadejia.

02/09/2022

LACCA! LACCA!! LACCA!!!

Kwamatin Limaman Juma'a na karamar hukumar Hadejia, karkashin jagorancin Mallam Yusuf Abdurrahman Ya'u (Babban Limamin Masarautar Hadejia)

Na Gayyatar Al'ummar Musulmi zuwa wajan gangamin lacca wadda ya shirya mai Taken
ILLAR SABON ALLAH.

RANAR ASABAT DA LAHADI, 06-2-1444/ 03-9-2022

Malamai:

(ASABAT) 06 Safar 1444/ 03 September 2022

1- Budewa da addu'a Mal. Abubakar Abdullahi (Na'ibin limamin Masallacin Gidan Yogurt)

2- Makala ta (1) MA'ANAR SABON ALLAH DA RABE RABEN SA. Mal. Gazali Ibrahim (Na'ibin limamin Masallacin Matsaro). (minti 40)

3- Makala ta (2) ILLAR BOKANCI DA SIHIRI. Mal. Khalifa Suleman Abdullahi. (Minti 40)

4- Rufewa da Addu'a, Goni Abdulkadir Abdullahi.

(LAHADI) 07 Safar 1444/ 04 September 2022

ILLAR SABON ALLAH

Malamai:

1- Budewa da addu'a Mal. Umar Hamza (Na'ibi na 2 na limamin Masallacin Sarki)

2- Makala ta (1) TABARRUJIN MATA DA ILLAR SA. Mal Habibu Aminu (Na'ibin baban limamin Masarautar Hadejia). (Minti 40)

3- Makala ta (2) TASIRIN SABON ALLAH GA DAN ADAM DA AL'UMMA. Mal. Dr. Nuhu Ali. (minti 40)

4- Rufe taro da addu'a Mal. Muhammad Sani Alhasan.

Wuri: Babban Masallacin Juma'a na Maimartaba Sarki, cikin garin Hadejia.

Lokaci: Bayan Magriba zuwa Isha'i

Allah ya bada ikon halarta

Sign: Mallam Yusuf Abdurrahman Ya'u Babban Limamin Masarautar Hadejia.

29/06/2022

Ayyukan da s**a fi falala A kwanaki goma na farkon Watan Hajji

1. Sallar Nafila Ta Dare.

Allah Subhanahu wa taala Yayi rantsuwa da wasu lokutta domin nuna mahimmancinsu. Allah Yace: {وَالْفَجْرِ (1) وَلَيَالٍ عَشْرٍ} [الفجر: 1، 2] Maana: (1. Inã rantsuwa da alfijiri. 2. Da darũruwa gõma.) Saboda haka Sallar nafilar dare musamman a lokacin sulusin dare na karshe tana da falala sosai.

2. Aikin Hajji da Umra.

3. Layya ranar Goma ga watan.

An ruwaito hadisi daga Aisha – radiyallahu ‘anha tana cewa:

(عن عائشة : أن رسول الله صلى الله عليه و سلم قال ما عمل آدمي من عمل يوم النحر أحب إلى الله من إهراق الدم إنها لتأتي يوم القيامة بقرونها وأشعارها وأظلافها وأن الدم ليقع من الله بمكان قبل أن يقع من الأرض فيطيبوا بها نفسا). رواه الترمذي والحاكم.

(Manzon Allah – Tsira da amincin Allah su tabbata agareshi – yace: Dan Adam bai aikata wani aiki ba ranar layya wanda yafi soyuwa zuwa ga Allah kamar zubar da jinin layya domin ko lalle zata zo ranar tashin kiyama da kohoninta da gashinta da kofatunta, kuma jininta yakan fada a wurin Allah ga wani wuri kafin ya zuba a kan kasa, saboda haka ku farantar da ita layyar wani rai.)

4. Azumin ranar Arafat ga mauzana gida.
Muslim ya ruwaito hadisi cewa an tambayi Manzon Allah – Tsira da amincin Allah su tabbata agareshi –:
(Game da azumi ranar Arafat sai yace: yana kankare zunuban shekarar baya da wanda ta rage)

قَالَ وَسُئِلَ عَنْ صَوْمِ يَوْمِ عَرَفَةَ فَقَالَ « يُكَفِّرُ السَّنَةَ الْمَاضِيَةَ وَالْبَاقِيَةَ » مسلم

5. Sauran ayyukun alheri na kamar karanta alqurani, tasbihi, takbiri, azumin nafila, sadaqa, da sauransu.

An ruwaito hadisi daga Aisha – radiyallahu ‘anha tana cewa:

عنْ عَائِشَةَ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قَالَ : سَدِّدُوا وَقَارِبُوا وَاعْلَمُوا أَنْ لَنْ يُدْخِلَ أَحَدَكُمْ عَمَلُهُ الْجَنَّةَ ، وَأَنَّ أَحَبَّ الأَعْمَالِ أَدْوَمُهَا إِلَى اللهِ وَإِنْ قَلّ. رواه البخاري

Kuyi saiti (wurin dacewa da ayyuka) ku yi kusanci (wurin samun daidai a ayyukka) kuma ku sani cewa ba wanda aikinsa zai shigar dashi aljannah, kuma mafi soyayyen ayyuka a wurin Allah sune wadanda aka dawwama akansu ko da kadan ne basu da yawa.

Allah Ya bamu dacewa kuma Ya karbi Ayyukan mu na ajizai masu gazawa. Amin

26/05/2022

Assalamu Alaykum,

Bayan hutu da akayi na watan ramadan in Sha Allah gobe Juma'a 25- Shauwal - 1443/ 27- May - 2022 za a cigaba da karatukan da da aka saba yi na ranakun Juma'a Asabat da Lahdi bayan sallar magrib.

Juma'a da Asabat: Babban Limamin Masarautar Hadejia M. Yusuf Abdurrahman Ya'u.

Lahadi: Na'ibin babban Limamin Masarautar Hadejia, M. Habibu Aminu.

JUMA'A: Al'wajiz fi fikisus sunnah wal kitabil Aziz.
ASABAT: Al'adabul Mufrad
LAHADI: Riyadussalihin

Wuri: Babban Masallacin Juma'a na cikin garin Hadejia

Allah ubangiji ya bamu ikon halarta, Allah ya bamu ikon aiki da abinda za'a karantar.

Sign: Chief Imam Hadejia Emirate.

PUBLIC ANNOUNCEMENT ⚠️His Royal Highness the Emir of Hadejia Alhaji (Dr) Adamu Abubakar Maje (CON) will tomorrow Saturda...
29/04/2022

PUBLIC ANNOUNCEMENT ⚠️

His Royal Highness the Emir of Hadejia Alhaji (Dr) Adamu Abubakar Maje (CON) will tomorrow Saturday 29th Ramadan 1443 lead the closing of this year Ramadan Tafsir.

At Hadejia Central Masjid

25/04/2022

Address

Emir Palace Road
Hadejia

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hadejia Central Masjid posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category