Wankaneh design

Wankaneh design I am professional Tailor !!! Am trying my best about disappoint my customers

07/08/2026
07/08/2026

YABON GWANI YAZAMA DOLE

A lokacin da Nasir Ahmad El-Rufai yake Gwamnan Jihar Kaduna, blogger irin Nagya a Kaduna. Kowace rana yana yana s**ar El...
26/07/2026

A lokacin da Nasir Ahmad El-Rufai yake Gwamnan Jihar Kaduna, blogger irin Nagya a Kaduna. Kowace rana yana yana s**ar El-Rufai tun daga safe har zuwa dare, har ma yana kiransa da ɓarawon kuɗin gwamnati.

Sai dai El-Rufai bai sa aka k**a shi ba. Maimakon haka, ya nemo lambar wayarsa.

Wata rana El-Rufai ya kira shi da kansa.

Wayar ta shiga...

El-Rufai: Assalamu alaikum, barka da safiya.

Blogger: Barka da safiya. Don Allah da wa nake magana?

El-Rufai: Sunana Nasir Ahmad El-Rufai.

Blogger: Oh, barka da safiya, Mai Girma.

El-Rufai: Barka da safiya, ɗan'uwa. Ina ganin rubuce-rubucenka game da gwamnatina da kuma yadda kake zargina da wawure kuɗin jiha.

Blogger: Yi haƙuri ranka ya daɗe, ba haka nake nufi ba.

El-Rufai: Ba damuwa. Hakan yana cikin shugabanci. Amma zan so ka zo Gidan Gwamnati gobe domin mu tattauna waɗannan batutuwa. Kada ka ji tsoro, babu abunda zanma.

Blogger: Ba matsala, ranka ya daɗe. Wane lokaci zan zo?

El-Rufai: Karfe 10:00 na safe.

Blogger: In shaa Allah zan zo.

El-Rufai: Zan jira ka. Amma za ka zo da mota ne ko babur? Domin na sanar da jami'an tsaro su bar ka ka wuce.

Blogger: Zan hau adaidaita sahu ne.

El-Rufai: To idan kana kan hanya ka turo min da lambar adaidaita sahun, domin in sanar da jami'an tsaro.

Blogger: To, babu matsala.

Washegari da misalin ƙarfe 9:00 na safe, blogger ɗin ya hau adaidaita sahu ya nufi Gidan Gwamnati. Da ya isa ƙofar shiga, jami'an tsaro s**a bari ya wuce, har s**a nuna masa inda zai tsaya.

Daga nan sai ADC na gwamnan ya zo ya raka shi kai tsaye zuwa ofishin gwamnan.

Da ya shiga ofishin, El-Rufai ya tambaye shi:

El-Rufai: Ka biya kuɗin adaidaita sahun?

Blogger: A'a, ranka ya daɗe.

Sai El-Rufai ya buɗe drawer shi, ya fito da wata ambulan mai ɗauke da ₦250,000, ya ba shi ya je ya biya kuɗin adaidaita sahun sannan ya dawo.

Blogger ɗin ya karɓa. A hanya sai ya buɗe ambulan, ya cire ₦5,000, ya ɓoye sauran kuɗin. Da ya isa wajen direban adaidaita sahun, sai ya ba shi ₦5,000. Direban ya yi farin ciki sosai.

Address

Mogadishu By Ahmadu Bello Way Kaduna
Kaduna

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Wankaneh design posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Wankaneh design:

Shortcuts

Share