24/08/2025
A jiya, uwargidan shugaban kasa Remi Tinubu ta kaddamar da kamfanin sarrafa fatar dabbobi domin yin takalma, jaka, belt da makamantan su. Gwamnatin jihar Lagos ce ta samar da Kamfanin, kuma an kiyasta cewa za'a dau maaikata kimanin dubu goma na dindindin. Sannan kuma kimanin mutum dubu dari da hamsin (150,000) ne zasu ci moriyar wannan kamfanin. Sannan jihar Lagos zata na samun kimanin $250Million duk shekara na kudin shiga ta dalilin wannan kamfanin da ta samar.
A hannu daya, ina yabawa jihar Lagos bisa wannan hangen nesa da tai wa kanta, a dayan hannun kuma, takaici ne ya ke nema ya shake ni, duba da cewa jihohin Kano da Sokoto, kusan su suke samar da fatar da wannan kamfanin zai amfani da su wajen samar da wadannan tagomashin arzikin ga jihar Lagos, amma su jihohin namu biyu na Arewa, basu samar da irin wannan kamfanin ba.
Kai hasali ma, jihohin Kano da Sokoto, kusan su ke samarwa da kasashen turai (irin su Italy, da Spain) fatar da suke yin takalma da jakunkuna na alfarma kamar su takalmin Bertozzi, ko jakar Gucci, wanda masu kudin mu suke zuwa su siyo su da tsada. Wannan al'amari ba wai sabon abu ne ba, kusan tun kafin zuwan turawa aka san jihar Kano da samar da fata ga kasar Morocco, wadda ita ma take siyarwa da turawa.
Na san a Kano, akwai kamfanonin jima wato tannery, wanda suke gyara fatun, su shirya su, domin a fitar da su. Amma ba mu da katafaren kamfanin da zai sarrafa fatar zuwa kayan alfarma kamar yadda Lagos zata fara.
Lokacin Gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje, da ni aka je China, garin Shandong, domin tattaunawa da kamfanin fata da na tufafi wato textile, kuma bayan dawowar mu, yan china din sun turo tawaga mai karfi, inda s**a zo Kano, domin duba yiyuwar saka hannun jari, amma babbar matsalar da ta hana wannan alamari faruwa shine rashin wutar lantarki. Harkar fata da textile abu ne mai bukatar wutar lantarki kuma jihar Kano bata da shi a wadace, sannan policy din gwamnatin taraiya a lokacin bai lamunce jihohi su gina ba, idan ma sun gina t