02/08/2025
Assalamualaikum
Yekuwa jamaa!!!
📢 Kira Ga Dukkan zakakuran Matasan teiloli na Arewa!
Muna farin cikin sanar da ku cewa
Wasu jajirtattun Matasan teiloli sun kafa mana Kungiya Mai suna: (Northern Nigerian Association for Youth Tailors and Entrepreneurship Development – NNAFTED).
An kafa wannan kungiya ne domin:
👍 Hada kan matasa masu dinki a Arewacin Najeriya
👍 Inganta harkar dinki da kasuwancinmu
👍 Taimaka wa matasa wajen samun horo da cigaban sana’a
Idan kai tela ne matashi da ke son karfafa sanaar ka, to wannan dama ce ta musamman gare ka don haɗuwa da sauran masu sana’a.
zo mu yi karatun ta nutsu wajen gina makoma mai kyau.💪
Me za ka amfana dashi idan ka shiga NNA
FTED?
Wadannan jajirtattun shugabannin sun tanadar mana:...
✌️ Samun horo da shawarwari akan kasuwanci
✌️ Shiga baje-koli, nune-nunen kaya da don bayyana fasahar da Allah ya baka,
✌️ Koyon sabbin dabarun dinki da fasaha na zamani
✌️Samar da Muryar hadin kai don samun goyon baya da samun damar cigaban sanaarka
💪Mu hada kai,
💪mu taimaki juna,
💪mu daukaka sana’ar mu a Arewa!
👉 Shiga kungiyar yau! Ba sei gobe ba,
👉Kar ka bari a Yi ba Kai
👉Kar ka bari a baka labari
📞 Tuntubi shugabannin wannan gwagwarmaya a lambar waya....
+234 806 385 6663
+234 707 953 3239
Ku zo mu dinka cigaba mai ɗorewa tare.💪
Muna jaddada goyon baya gareku @Dan Zanko Textile
@Ibrahim M Baba Arewa Tailors Union
Da sauran abokan gwagwarmaya da duk wadanda s**a Bada gudun mawa wajen wannan yunkuri,
Allah ya Saka muku da alkhairi 🙏
Allah yayi ruko da Hannayenku.
Kun zamar mana madubin dubawa💪💪💪
RANO FASHION GALLERY