Home of Peace Association -HOPA

Home of Peace Association -HOPA Peace and development

06/02/2022
31/01/2022

Alhamdulillah alakullihalin

09/04/2021

ENENE AZUMI
Azumi na nufin; kamewa ga barin wani abu
Amma a shari'a (الصَّوْمُ) assaumu shi ne kamewa ga barin ci da sha da barin yin jima’i tun daga bullowar alfijir har zuwa faduwar rana da niyyar yin ibada ga Allah.
Ubangiji madaukakin Sarki yana cewa:
قَالَ تَعَالَى: "يَأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ." (سورة البقرة: 183)
Ma'ana: “Ya ku wadanda kuka yi imani, hakika, an wajabta muku yin Azumi kamar yadda aka wajabta (shi) ga wadanda s**a gabace ku domin ku ji tsoron Allah.” (Al- Bakara: 183).
Sannan Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
"بني الإسلام على خمس شهادة أن لا إلـه إلا الله وأن محمدا رسول الله وإقام الصلوة وإيتاء الزكاة وحج البيت وصوم رمضان" رواه البخاري ومسلم.
“An gina Musulunci a bisa abubuwa guda biyar; shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah ne, da tsai da Salla da ba da Zakka da ziyartar Dakin Allah (Aikin Hajji) da azumtar watan Ramadan” (Bukhari da Muslim).
Azumin watan Ramadan rukuni ne daga cikin rukunan Musulunci guda biyar. Kuma Ubangiji Madaukakin Sarki ya wajabta wa wannan al’umma azumtar watan Ramadan.
Hakika, an wajabta azumtar watan Ramadan a cikin shekara ta biyu daga hijirar Manzon Allah (S.A.W) daga Makkah zuwa Madina.

30/03/2021

Y Allah ka kara daukaka wannan kungiya mai albarka

HOME OF PEACE ASSOCIATION (HOPA)  Ya ALLAH kabada  nasara da goyan baya a wannan kungiya mai albarka ka kuma daukaka ta ...
24/03/2021

HOME OF PEACE ASSOCIATION (HOPA)

Ya ALLAH kabada nasara da goyan baya a wannan kungiya mai albarka ka kuma daukaka ta Amen

16/03/2021

```✔ Kasa farin ciki a zuciyar Maraya yafi ka kwana kana Sallah

✔ Kuyi gaggawar aikata alheri karkuce sai kunyi kudi mai yawa

✔A Kyautata niyya idan za'ayi aikin alheri domin asamu yardar Allah.

✔ Ayi hankali da Riya, domin tana shiga cikin aikin mutum ta barauniyar hanya.

✔ Sadaqah tana janyo maka samun nasara tare da taimakon Ubangiji acikin dukkan abinda kasa agabanka.

✔ Sadaqah tana sanyawa ka samu gagarumar nasara akan Maqiyanka da mahassadanka. Kuma kaidinsu ba zai cuceka ba.

✔ Idan wani ciwo yana damunka har ka rasa maganinsa, to yawaita sadaqah. In sha Allah ita Sadaqah magani ce, waraka ce, kuma kariya ce daga dukkan cututtuka.

✔ Sadaqah ladanta yana tabbatuwa awajen Allah. Koda dabbobi kayi wa sadaqar, ko tsuntsaye, ko Kwari.

✔ Sadaqah garkuwa ce daga sharrin 'barayi, ko gobara, kuma tana kiyaye masu yinta daga mummunar cikawa.

✔ Babbar sadaqar da zaka fara gabatarwa ayanzu, ita ce kayi "sharing" (wato ya'da) wannan rubutun daga Zauren Fiqhu ba tare da goge koda harafi guda daga ciki ba.

Idan kayi haka da niyyar sadaqah, to duk wanda ya gani ya karanta kaima kana da lada akansa.```

20/01/2021

TSOKACI GAME DA KUNGIYAR MAROWATA TA KASA.

LALLE IZGILI GA ADDINI, ANNABI KO ALLAH KANSA NA IYA KAI MAI YINSA ZUWA GA KAFIRCI.

ALLAH YAYI KARIN BAYANI GAME DA KAFIRCIN MASU IZGILI GA ADDINI INDA YACE:

(وَلَئِنْ سَأَلْتَهُمْ لَيَقُولُنَّ إِنَّمَا كُنَّا نَخُوضُ وَنَلْعَبُ ۚ قُلْ أَبِاللَّهِ وَآيَاتِهِ وَرَسُولِهِ كُنْتُمْ تَسْتَهْزِئُونَ * لَا تَعْتَذِرُوا قَدْ كَفَرْتُمْ بَعْدَ إِيمَانِكُمْ ۚ إِنْ نَعْفُ عَنْ طَائِفَةٍ مِنْكُمْ نُعَذِّبْ طَائِفَةً بِأَنَّهُمْ كَانُوا مُجْرِمِينَ)
[Surat At-Tawbah 65 - 66]

SABODA MUTUNTA IYAKOKIN ALLAH ALAMA NE TSORON ALLAH,KAMAR YADDA KETA ALFARMAR IYAKOKIN ALLAH ALAMAR TABEWA CE.

ALLAH YANA CEWA:
(ذَٰلِكَ وَمَنْ يُعَظِّمْ حُرُمَاتِ اللَّهِ فَهُوَ خَيْرٌ لَهُ عِنْدَ رَبِّهِ ۗ وَأُحِلَّتْ لَكُمُ الْأَنْعَامُ إِلَّا مَا يُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ ۖ فَاجْتَنِبُوا الرِّجْسَ مِنَ الْأَوْثَانِ وَاجْتَنِبُوا قَوْلَ الزُّورِ)
[Surat Al-Hajj 30]

YA KARA CEWA:
(ذَٰلِكَ وَمَنْ يُعَظِّمْ شَعَائِرَ اللَّهِ فَإِنَّهَا مِنْ تَقْوَى الْقُلُوبِ)
[Surat Al-Hajj 32]

MU SANI CEWA ROWA SIFFACE ABAR ZARGI TA HARAMUN WACCE BAI KAMATA MUSULMI YA SIFFANTA DA ITA BA, BALLANTANA HAR YAYI TUNKAHO KO ALFAHARI DA ITA.

ALLAH YA SHAR'ANTA MANA YAKAR ROWA NE TARE DA KYAUTATAWA BAYINSA.
ALLAH YACE:

(وَإِنِ امْرَأَةٌ خَافَتْ مِنْ بَعْلِهَا نُشُوزًا أَوْ إِعْرَاضًا فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِمَا أَنْ يُصْلِحَا بَيْنَهُمَا صُلْحًا ۚ وَالصُّلْحُ خَيْرٌ ۗ وَأُحْضِرَتِ الْأَنْفُسُ الشُّحَّ ۚ وَإِنْ تُحْسِنُوا وَتَتَّقُوا فَإِنَّ اللَّهَ كَانَ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرًا)
[Surat An-Nisa' 128]

ALLAH YA KARA CEWA DUK WANDA AKA ISAR MASA KUMA AKA BASHI KARIYA DAGA BAKAR ROWARSA TO WA'INNAN SUNE MASU SAMUN BABBAN RABO.
(وَالَّذِينَ تَبَوَّءُوا الدَّارَ وَالْإِيمَانَ مِنْ قَبْلِهِمْ يُحِبُّونَ مَنْ هَاجَرَ إِلَيْهِمْ وَلَا يَجِدُونَ فِي صُدُورِهِمْ حَاجَةً مِمَّا أُوتُوا وَيُؤْثِرُونَ عَلَىٰ أَنْفُسِهِمْ وَلَوْ كَانَ بِهِمْ خَصَاصَةٌ ۚ وَمَنْ يُوقَ شُحَّ نَفْسِهِ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ)
[Surat Al-Hashr 9]

ALLAH YA KARA CEWA ROWA TA HANYAR KIN FITAR DA HAKKIN MASU HAKKI

13/01/2021

_*🌒بسم الله الرحمن الرحيم🌒*_
_*Hadisin da ke da ala'ka da maraya 01 cikin 03.*_
°
°
_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce; {IN KANA SON ZUCIYARKA TAYI LAUSHI, SAI KA CIYAR DA TALAKA, KUMA KA SHAFA KAN MARAYA.}*_
°
°
```[Silsilatus Saheeha;854]```
=
=
_Wannan hadisin yana nuna mana cewa duk wanda yake son zuciyarsa tayi laushi to ya ciyar da talaka kuma ya kula da maraya, ya shafa kansa, ya ji tausayinsa. Allaahu a'alam._

Alhamdulillah Allah ka daukaka wannan tafiyar tamu
12/11/2020

Alhamdulillah Allah ka daukaka wannan tafiyar tamu

04/11/2020

Peace and development

Address

Kano

Telephone

+2348138015109

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Home of Peace Association -HOPA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Home of Peace Association -HOPA:

Share