Maeenu samaeela

Maeenu samaeela A young huzler
Love mom &dad
Proud to be Muslim
Social media influencer
Young business owner
Cute guy;;;

"It is not everything a person sets their heart on that ends up being good for them. However, Allah always acts with wis...
22/04/2026

"It is not everything a person sets their heart on that ends up being good for them. However, Allah always acts with wisdom and never makes a mistake; whether things go the way you hoped or the opposite, you should simply accept it. Nothing is certain, especially in these times where things feel blurred and confusing.
​Oh Allah, You are the Savior of my life. Make things easy for me and grant me success ameen!!!!

Listen, life is not a race where, just because a peer has succeeded, you feel you must also succeed at that exact same m...
15/04/2026

Listen, life is not a race where, just because a peer has succeeded, you feel you must also succeed at that exact same moment. If that is how you understand life, then you are ignorant of its true nature.
​Wake up and strive, be patient, and offer prayers. Remember that once you did not exist, now you do, and one day you will be gone again. Accept that everything is temporary. Allah will help you; just persevere, and one day, you will be the one telling your success,,,

13/04/2026

I accepted 2 fan badges from Zarah Aliyu and Follow for Follow Everyone.

GINA RAYUWA A CIKIN DUHU: KADA KA YARDA SURUTUNKA YA KASHE NASARARKA!Akwai abin da yake daure min kai shi ne yadda matas...
20/03/2026

GINA RAYUWA A CIKIN DUHU: KADA KA YARDA SURUTUNKA YA KASHE NASARARKA!
Akwai abin da yake daure min kai shi ne yadda matashi yake ɗokin nuna wa duniya abin da yake shirin yi, alhali bai ko fara ba. Kana da kudin jari dubu dari (100k), nan take ka ɗauka ka sa a "Status" kana cewa "New Business loading". Kana da burin gina gida, ka gayawa kowa. Kana shirin aure, kowa ya sani.
Dan uwa, bari in gaya maka gaskiya: Nasarar da ake nuna wa duniya kafin ta tabbata, ita ce nasarar da za ta lalace.

SURUTU SHI NE MAKIYIN NASARA: Duk lokacin da ka bayyana sirrinka ko burinka ga mutane, ka ba su damar su sa maƙura a ciki. Akwai mutane da yawa da ba sa son ka ga nasara, idan ka gaya musu shirin ka, za su yi amfani da munanan kalaman su ("ai ba za ta yiwu ba," "ai wane ya riga ya yi," "babu kudi") wajen kashe maka kwarin gwiwa. Gwara ka yi shiru, ka bar nasararka ta yi musu magana.

DUNIYA BA TA GIRMAMA "WANE YAKE SHIRIN YI": Mutane suna girmama mai "Ya yi." Kada ka zama mutumin da kullum yake cikin yin surutu ("Loading...", "Coming soon..."). Ka zama mutumin da yake fitowa da sakamako. Namiji mai Izza shi ne wanda yake gwagwarmaya a cikin duhu, ba wanda yake neman yabo a kafafen sada zumunta ba tare da ya kai ko’ina ba.

JIRAN SAMUWAR "ICEBERG":
Dubi yadda babban kankara (Iceberg) yake a cikin teku; babban sashi ne yake a ɓoye a ƙarƙashin ruwa, sannan ƙaramin sashi ne yake a sama. Haka nasarar namiji ya kamata ta kasance. Ka gina tushenka a ɓoye (neman ilimi, sana'a, adana kudi), idan tushenka ya yi ƙarfi, to babu wani iska da zai iya kada ka.

NASARA BA TA BUKATAR TAYA KARAWA:
Idan kana da gaskiya, kuma kana da himma, nasararka za ta bayyana kanta. Kada ka yi ƙoƙarin nuna wa duniya cewa kai "Big Boy" ne alhali a ciki babu komai. Gaskiyar rayuwa ita ce: Mutanen da kake ƙoƙarin burgewa da hotuna ko magana, su ne za su fara dariya idan ka faɗi. Ka bar su da shakkun abin da kake yi, ka maida hankali kan aiki.

SAKO NA GA MAZA MASU FAFUTUKA:
Idan kana son zama wani a nan gaba, to ka koyi yin shiru. Ka maida duk kuzarinka wajen gina "Assets" dinka (sana'a, ilimi, dukiya). Ka daina neman yabo; ka nemi sakamako. Ranar da ka cimma burinka, duniya ce za ta neme ka don ta ga yadda ka yi. Namiji mai himma, namiji mai asiri, namiji mai natsuwa—shi ne wanda yake samun nasarar da ba ta mutuwa. Tashi ka fara aikin, ka daina surutu!

“Kuma ku taimaki kanku da ɓoye sirrinku (wajen aiwatar da bukatunku), domin duk mai ni'ima, ana yi masa hassada." (Duba: Hadisi daga Tabarani, Sahihul Jami' 943).

Ya Allah Ka bamu ikon gina rayuwarmu cikin hikima da asiri, Ka kuma sanya albarka a dukkan fadi-tashin da muke yi a ɓoye da fili
Maeenu samaeela ✍️

19/03/2026

Tun kundaiji

15/03/2026

A MATSAYINKA NA NAMIJI, WAƊANNAN ABUBUWA 6 SUNE KUDIN DA ZAKA BIYA KAFIN KA SAYI NASARA.

Maganar gaskiya wacce dole ka hadiye ta: Duniya bata bayar da nasara a kyauta. Idan har kana son zama wani abu a gobe, dole ne ka ajiye kukan shagwaba ka fuskanci gaskiyar rayuwa.

A matsayinka na Namiji, wadannan abubuwa guda 6 sune Harajin da dole sai ka biya kafin ka ci riba. Babu gajeruwar hanya, zallar juriya ce kawai.

1. Kadaici:
Zaka wayi gari babu mai tambayar lafiyarka. Dole ka koyi zama kai kadai ka gina makomarka a lokacin da sa'anninka suke wajen holewa.

2. Radadi:
Zaka ji ciwo a zuciyarka da jikinka wajen fafutukar neman halas. Hawayen da kake hadiyewa a boye, sune zasu wanke maka talauci.

3. Faduwa:
Zaka tsara kasuwanci ya ruguje, Asarar da zaka yi ita zata koya maka hankalin yadda zaka kiyaye miliyoyin da zasu zo a gaba.

4. Wulakanci:
Zaka roki alfarma a rufe maka kofa a fuska. Mata zasu guje ka, abokai zasu nuna ba su san ka ba. Wannan zai koya maka dogaro da kanka.

5. Asara:
Zaka rasa kudi, zaka rasa lokaci, sannan zaka rasa mutanen da ka yarda da su. Wannan shine matakin da zai raba ka da tsoro.

6. Raini: Mutanen da baka taba zaton zasu daga muryarsu a kanka ba zasu raina ka saboda baka da kudi. Wannan rainin shine zai zama wutar da zata sa ka ninka fafutukarka.

Dan uwa, babu wani Attajiri a yau da bai tsallake wadannan matakan ba. Daure ka sha zafin yau, domin ka sayi hutun gobe.

Babu wata gajeruwar hanya zuwa ga nasara. Juriya ita ce kadai motar da zata kai ka inda kake son zuwa.

Allah yasa mudace.
UMAR ALIYU DAHIRU ✍️

15/03/2026

CUTUTTUKAN ZUCIYA 4 DA SUKE SACE MAKOMAR MATASA KAFIN SHEKARU 30.

Kwakwalwar dan adam an tsara ta ne don ta nemi jin dadi na gaggawa, amma nasarar rayuwa tana bukatar hakuri da jure wahala. Idan baka lura da wadannan cututtukan guda 4 ba a kuruciyarka, wallahi za su jefa ka a asibitin kuka idan ka tsufa:

1. Neman Yabo Ta Hanyar Bashi:
Sayen sabuwar waya ko takalma a kanti da alkawarin biya a hankali, don kawai a ce ka waye a wajen 'yan mata. Kana zaluntar kwakwalwarka da bashin da zai hana ka barcin natsuwa.

2. Tsoron Koyo Da Kaskantar Da Kai: Kwakwalwarka tana fada maka cewa kai mai Digiri ne ba zaka koyi Sana'a iri kaza ba ko sana'ar hannu ba. Wannan girman kan shine zai sa ka kare a matsayin mai jiran aiki a lokacin da masu sana'a suke gina gidaje.

3. Tarkon Nishadin Intanet:
Ka dauki lokacinka da kudin Datarka kana kallon rayuwar masu kudi a Social Media. Kwakwalwarka tana jin dadi a lokacin, amma a zahiri asarar lokacin gina taka rayuwar kake yi tunda baka sayar da komai ba.

4. Garkuwar Abokan Asara:
Zama a majalisa daga safe har dare kuna hirar kwallon kafa. Kuna bawa junanku kwarin gwiwar gurguwar rayuwa, ba tare da daya daga cikinku ya yi tunanin yadda zaku nemo N5,000 ku fara neman na kanku ba.

Tsari ne na duniya; abin da ka shuka a 20s dinka, shi zaka girba a 40s dinka. Gyara tunaninka yau.

Allah yasa mudace.
UMAR ALIYU DAHIRU ✍️

Address

Kani
Kano
STUDENT

Telephone

+18125088154

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Maeenu samaeela posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Maeenu samaeela:

Shortcuts

Share