22/11/2023
Me Hujja Baya Zagi:
Amsa kawai nake bukata, banason wani surutun shirme ko kafa hujja da mafarki. 👇👇
Wani dan DARIKA TIJJANIYYA yayi min DM, yace wallahi dalilin dayasa suke son IBRAHIM INYAS saboda yanason manzon Allah, masoyin annabi ne na gaskiya, saboda haka dole zasu so annabi kuma su so masoyin annabi.
A nan abunda zance shine:
Sayyidina Abubakar (R.A) masoyin annabi ne, sahabin annabi ne, abokin annabi ne, surukin annabi ne, da Abubakar annabi yayi hijira daga makka zuwa madina. Duk yakin da akayi da gwagwarmaya domin a tsayar da addinin muslunci tare da sayyidina Abubakar akayi.
Sayyidina Abubakar R.A duk dukiyarsa yayi amfani da ita wurin sayen bayi yana mayardasu addinin muslunci. Har sai da Allah ta’ala yayi yabo ga sayyidina Abubakar acikin Alqur’ani maigirma:
ٱلَّذِی یُؤۡتِی مَالَهُۥ یَتَزَكَّىٰ
وَمَا لِأَحَدٍ عِندَهُۥ مِن نِّعۡمَةࣲ تُجۡزَىٰۤ
إِلَّا ٱبۡتِغَاۤءَ وَجۡهِ رَبِّهِ ٱلۡأَعۡلَىٰ
وَلَسَوۡفَ یَرۡضَىٰ
Hadisi yazo daga Annabi SAW, annabi yace duk duniya yafi son Abubakar.
Abubakar shine mutum na farko da yafara gasgata manzon Allah saw.
SAYYIDINA UMAR R.A
SAYYIDINA USMAN R.A
SAYYIDINA ALIYU IBN ABI TALIB
Da sauran sahabbai Asharatul Mubashshirina fil JANNAH wanda tun anan duniya ALLAH ya aiko mala’ika JIBRILU yakawo ma annabi sunayensu tare da lasisi cewa ‘yan ALJANNAH ne ALLAH ya gafarta musu.
Sun zubar da dukiyarsu domin addinin Allah
An zubar da jininsu domin addinin Allah
An rabasu da gidajensu domin addinin Allah
Sun rabu da iyayensu da matansu da yayansu domin addinin Allah
Duk wadannan sahabban ba abun so bane sai INYAS dan senegal 🇸🇳 ?? 🥲🥲
KU AMSA MIN WANNAN TAMBAYOYI 👇👇
Me alakar INYAS da manzon Allah?? INYAS yazo a hadisi ko ayah??
INYAS ya rayu da annabi??
Wane yaki akayi da INYAS??
Mutum nawa INYAS ya shigo dasu a muslunci??
Da INYAS da SHEHU DAN FODIYO wane yafi yiwa addinin muslunci hidima?? Wane yafi yiwa addinin ALLAH amfani??
Shekarun INYAS nawa da mutuwa?? Kamun zuwan INYAS wadanda sukayi rayuwa acen baya akwai musluncin su ko babu?? Zasu shiga aljannah ko bazasu shiga ba??
To kai da kake an mayar dakai mahaukaci wani zaizo yace ma sai kaso INYAS sannan zaka shiga aljannah, a wane hadisi ko ayah akace haka??
Allah yayi mana sauki
Allah ya ganar damu gaskiya.
Alhassan Mai Lafia.