26/07/2025
*Karka sake Maƙotanka su yi maka mummunan shaida akan waɗannan abubuwan:*
1- *Kar ka sake ayi maka shaidar rashin yin sallah ko ƙin zuwa masallaci matukar kana da lafiya*
2- *Kar ka sake ayi maka shaidar baka yiwa mutane sallama ko in sun yi maka baka amsawa*
3- *Duk rintsi duk wuya kar a sameka da laifin ƙin zuwa ta'aziyya, ko rashin duba maƙocinka yayin da bashi da lafiya*
4- *kar ka sake a kamaka da laifin zubawa maƙocinka kwata a ƙofar gidansa*
5- *Ka yi iyaka ƙoƙarinka wajan barin matarka zuwa dubiya ko barkar suna a keɓantaccan lokacin da ka zaɓa mata*
6- *karka sake ka ci kuɗin maƙocinka, ko a yi maka shaidar zalunci*
7- *kar ka sake maƙocinka ya tambayeka wani abu ka hana shi matukar kana da shi ko yaya ya ke*
8_*ka zamanto mai nuna damuwarka yayin da maƙocinka ya ke cikin wani mawuyacin hali, karka koma gefe kana tseguminsa*
9- *kar ka sake ayi maka shaidar mai nuna fariya ko nuna cewa ka fi kowa ilmi, kuɗi, matsayi, ko mukami*
10. *Kar ka sake ka kwana cikin koshi yayin da maƙocinka ke cikin yunwa*
*Ya Allah ka sanya mu cikin salihan bayinka karka sanya mu cikin gafalallu....