31/05/2026
SHIN KUNSAN MEYESA THUMBPRINT ƊIN KOWANE YATSA YA BAMBANTA......✍️✍️
Fiye da shekaru 1400 da s**a gabata, Alƙur’ani ya ambaci wani sirri game da yatsun ɗan Adam wanda yake da matuƙar daidaito, wanda kimiyyar zamani ta fahimci muhimmancinsa ne bayan ƙarnika masu yawa.
أَيَحْسَبُ الْإِنسَانُ أَلَّن نَّجْمَعَ عِظَامَهُ بَلَىٰ قَادِرِينَ عَلَىٰ أَن نُّسَوِّيَ بَنَانَهُ
Allah Yace a cikin Alƙur’ani... “Shin mutum yana zaton ba za Mu tattara ƙasusuwansa ba?
Eh mana! Muna da ikon daidaita har ma da yatsunsa.”
(Al-Qiyamah 75:3–4)
A yau, kimiyyar binciken laifuka ta tabbatar da cewa zanen yatsan kowane mutum na musamman ne, hatta tsakanin tagwaye iri masu k**a ɗaya. Wannan ne yasa zanen yatsa ya zama ɗaya daga cikin hanyoyi mafi inganci wajen gane mutum.
(Forensic Science Handbook, FBI Scientific American: “No Two Fingerprints Are Alike”) Wato babu wasu yatsu guda biyu da s**a kasance iri ɗaya....
Alƙur’ani bai tsaya kawai ga ambaton ƙasusuwa ba, sai ya keɓance yatsu, yana nuna wani matakin daidaito wanda ɗan Adam bai sani ba a wancan lokacin.
Wannan aya tana daga cikin manyan ayoyin da suke nuna cikakken ilimin Allah da k**alar halittarsa. Zaka iya duba Tafsir Ibn Kathir akan Suratul Qiyamah aya ta 3–4.
Alƙur’ani ba littafin kimiyya bane, amma duk lokacin da aka gano wata gaskiyar kimiyya, za’a ci karo da abubuwa masu nuna hikima da daidaito a cikin Alƙur’ani.
وَمَنْ أَصْدَقُ مِنَ اللَّهِ حَدِيثًا
“Kuma waye yafi Allah gaskiya a magana?”
(An-Nisa’i 4:87)
Usman Abdurrazaq Gumel