08/09/2026
*INA ADALCI?*
An k**a *Sheikh Khalifa Sani Zaria*, an daure shi, an tozarta shi da suna "zargin juyin mulki"...
Amma tambaya a nan ita ce: *INA HUJJA?*
Babu makami da aka k**a a hannunsa.
Babu murya ko saƙo da ya nuna ya shirya juyin mulki.
Babu shaida ko ɗaya da kotu ta tabbatar.
Abin da kawai yake da shi ne harshensa - yana fadin gaskiya.
Shin yanzu fadin gaskiya ya zama laifin juyin mulki a Najeriya?
Rashin adalci da aka yiwa Sheikh Khalifa ba laifinsa ne kadai ba, cin mutunci ne ga duk wani Malami mai cewa gaskiya. Idan za a iya daukar Malami mai mutunci a tozarta shi ba tare da hujja ba, to gobe waye?
Muna kira ga hukumomi, muna kira ga al'ummar musulmi: Ku saki Sheikh Khalifa Sani Zaria. Adalci ya tabbata. Ba za a gina kasa da zalunci ba.
* *